Connect with us

Fact Check Hausa

Fact Check: Ko Aisha Buhari ta bada umarnin kone ofishin Abba Kyari?

Published

on

Sponsor:

Gaskiyar Magana: Labari Ne Na Bogi!

Wani bidiyo mai tsawon minti hudu da dakika goma sha bakwai (4:17) da wata kafa mai suna Gido24TV dake dandalin YouTube  wanda yanzu haka ake yaduwa a WhatsApp ta wallafa ya bayyana cewa Uwargidan Shugaba Buhari, wato Aisha Buhari ta bada umarnin nan take cewa a kona ofishin shugaban ma’aikatan dake aiki a karkashin Shugaba Buhari wato Abba Kyari.

Kamar yadda wannan bidiyo da aka wallafa ranar 26 ga Maris, 2020 ya fada, umarnin ya biyo bayan gane cewa Abba Kyarin yana dauke da Cutar COVID-19 bayan da akayi masa gwaji. Bidiyon ya kara da cewa Aisha Buhari tace Abba Kyari yaje ofishin sa bayan dawowarsa daga kasar waje kuma duk abubuwan da ya bata sun harbu da Cutar COVID-19 dan haka dole a kona komai dake cikin ofis din dan akare mutane daga kamuwa da wannan cutar.

Wannan zance marar tushe har wayau kara da cewa Uwargida Aisha tace tunda kasashen duk suna ta kokarin kawar cutar kuma kawo yanzu babu maganin ta, dole ne a kona ofishin Abba Kyarin.

Binciken CCD

Masu tantance gaskiya ko rashin gaskiyar labari na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya Da Cigaba wato CDD sun gudanar da bincike mai zurfi kuma sun gano cewa wannan kageggen labara ne. Masu binciken sun gano cewa acikin wannan bidiyo mai tsawon minti  hudu (4) da dakika goma sha bakwai (17) babu inda aka zayyana cewa Aisha Buharin ta bada wannan umarnin ballantana rana ko lokacin da ta tayi wannan bayani.

Har wayau binciken ya gano cewa anyita anfani da hotunan Aisha Buhari da Zahra Buhari da Abba Kyari da tsohuwar ministan kudi Kemi Adeosun da hoton wuta yayin ake gabatar rahotan da ba’a ganin wanda yake gabatar dashi. Acikin wannan kageggen labari, mai gabatarwa tun da farko yayi alkawarin nunawa mai kallo yadda kona ofishin Abba Kyarin ya kasance amma har inda bidiyon ya kare ba’aga hakan ba. Kawo yanzu ankalli wannan bidiyo sau dubu shida da dari biyar kawo ranar 30th ga watan Maris, 2020 da misalin karfe 11:15 na dare, wannan yana nufin yawan masu kallon wannan labari na karya zai cigaba da karuwa.

Afili yake cewa wanda suka gina wannan labari na karya suna da aniyar samun riba ta hanyar karfafawa mutane gwiwa su cigaba da kallon wannan dandali nasu dan kuwa manhajar YouTube tana biyan kudi gare su a duk lokacin da aka kalli bidiyon, saboda haka masu kallo suna karuwa su kuma masu wannan labari na karya suna kara samun kudi.

Karin rahotonni:

Fact Check: Da gaske an karantawa Trump Qur’ani saboda Coronavirus?

[Fake News] Fitattun labaran karya 10 kan Coronavirus

[Fake News] Gwamnan Oyo ya tsige mai taimaka masa saboda yada labaran karya kan Coronavirus

Kammalawa:

Wannan labari, labari ne na bogi saboda haka CDD tana jan hankalin yan Najeriya da suyi watsi dashi tare da dena kallon sa dama kara yadashi a sauran kafafan sada zumunta zamani. Har wayau CDD tana kara jan hankali cewa a dena kirkira dama yada labaran karya.

Tantancewar Mu: Labari Ne Maras Tushe

Summary:

Tantancewar Da CDD Ta Aiwatar

Shin Aisha Buhari Ta Bada Umarnin Kona Ofishin Abba Kyari?

Gaskiyar Magana: Labari Ne Na Bogi!

Wannan labari, labari ne na karya saboda haka CDD tana jan hankalin yan Najeriya da suyi watsi dashi tare da dena kallon sa dama kara yadashi a sauran kafafan sada zumunta zamani. Har wayau CDD tana kara jan hankali cewa a dena kirkira dama yada labaran karya saboda illar da yake dashi.

Tantancewar Mu: Labari Ne Maras Tushe

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Saurari Shirin Daga Shafukan Sadarwa

Shirin dake tattauna batutuwan da suka shafi shafukan internet da kuma rahotonni daga makarantunmu.

31-10-2019

14-09-2019

07-09-2019

31-08-2019

24-08-2019

10-08-2019

03-08-2019

26-07-2019

For Registering Domain Names, I trust DomainKing.NG

Subscribe To Our Youtube Channel

Subscribe To Khalyperh The Voice Channel

Subscribe To AU Studio On Youtube

Litattafai Cikin PDF

  1. Takardar Sanin Makama Ga Daliban Da Zasu Zana Jamb 2018 Download Now
  2. Mu Koyi Computer A Saukake Download Now
  3. Duniyar Facebook A Yau Download Now
  4. Yadda zaka fara neman kudi Online ta NNU Download Now
April 2020
M T W T F S S
 12345
6789101112
13141516171819
20212223242526
27282930  

ADS

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG
error: Content is protected !!