Connect with us

News

[Fake News] Fitattun labaran karya 10 kan Coronavirus

Published

on

Labaran Karya Kan Corona Virus, Fake News on Coronavirus in Hausa

1. Shin Saddam Husseini yayi magana kan Coronavirus?

An ta yada wannan bidiyon tare da cewa a shekarar 1990 cewa tsohon shugaban kasar Iraq, Saddam Hussein ya bada labarin annobar Coronavirus.

Bincike: a binciken da cibiyar Sharfadi Technology ta gudanar kan wannan bidiyo ya gano cewa bidiyo ne da aka jirkita shi, ta yadda aka samo bidiyon marigayin sannan aka cire asalin muryarsa dake kan bidiyon aka maye gurbinta da wata murya daban.

Madogara: ‘Yar gidan marigayi Saddam Hussein, Raghad Saddam Hussein ta wallafa wannan bidiyo a shafinta na Twitter kamar yadda kuke gani a kasa, sannan ta karyata shi tare da cewa wannan ba bidiyo ba muryar mahaifinta ba ce.

2. Shin Donal Trump ya ga bidiyon masu dawafi a Ka’aba yayi alkawarin shafe dakin ka’aba?

Anyi ta yada wannan bidiyon cewa an nunawa shugaban kasar Amurka, Donal Trump dakin Ka’aba yayin da ake gabatar da bautar Allah, a don haka yayi alkawarin shafeta, shi ne har ta kai an rufe Ka’aba saboda Coronavirus.

Bincike: Zahiri abinda yake cikin bidiyon ana nunawa Trump sassan kasar sa ne, amma sai aka cire wurin aka dasa hoton dakin ka’aba sannan aka cire sautin aka saka na wani daban.

Ku kalli sahihin bidiyon daga shafin Daily Motion.

3. Shin babban limamin kasar Ghana ya ce za a iya shan giya don kariya ga Coronavirus?

An ta yada wannan labarin a kafafan sada zumunta kamar yadda kuke gani a kasa:

 

Bincike: Sai dai wannan labari ba haka yake ba, domin kuwa tuni babban limamin ya fito ya karyata wannan maganar a kafafan yada labaran kasar, sannan ya ce yayi magana da manema labarai ne kan matsayar su dangane da annobar Coronavirus kamar yadda kuke gani a takardar dake kasa:-

4. Shin daliban FCE Gombe sun kamu da Coronavirus?

An ta yada labarin cewa daliban kwalejin tarayya dake Gombe sun kamu da annobar Coronavirus kamar yadda kuke gani a kasa.

Sai dai har izuwa yau 29-03-2020 hukumomi basu bayyana cewa an samu koda bullar cutar a jihar Gombe ba.

Sannan na ci karo da posting din wani matashi da ya karyata labarin kamar yadda kuke gani a kasa.

5. Shin an yi mafarki da Annabi (s.a.w) ya ce a jika gashi a sha saboda Coronavirus?

Sai dai tuni malaman addini irin su Sheikh Muhammad Harun Ibn Sina da kuma Malam Aminu Daurawa suka karyata wannan labarin, ga jawabin Malam Daurawa daga shafin Freedom Radio.

Karin labarai:

[Fake News] Gwamnan Oyo ya tsige mai taimaka masa saboda yada labaran karya kan Coronavirus

[WhatsApp] Hanyoyi Bakwai (7) Da Zaka Tantance Ingancin Sako a WhatsApp

[Facebook] Hanyoyi (11) da Zaka Tsayar da Samun Labaran Karya a Facebook

6. Shin an aiko da kayan sawar masu cutar Coronavirus zuwa Najeriya?

Kamar yadda ku ka gani a sauti da hoton dake sama, an ta yada su cewa wai kayan masu cutar Coronavirus ne ake tattarawa zuwa Najeriya.

Bincike: wannan hoto dai ya jima a internet tun kafin zuwan Coronavirus, hasalima tun shekarar 2016 akwai shafukan da suka taba sanya shi a internet, kamar yadda kuke gani a hoton dake kasa.

7. Shin shugaban kasar Russia ya sako Zakuna akan titi domin hana mutane fitowa saboda Coronavirus?

An ta yada wannan labari kamar yadda kuke gani a hoton dake kasa.

Bincike: Wannan labari ba haka yake ba, babu wannan zancen ko kadan a kasar Russia, domin kuwa hoton Zakin da ake yadawa an dauke shi ne a birnin Johannesburg na kasar Africa ta Kudu a shekarar 2016 yayin daukar wani Film.

Ku kalli hoton Zakin da wurin a kasa:-

8. Shin Shugaban kasa Buhari ya kamu da Coronavirus?

An ta yada wannan hoto mai tambarin CNN dake kasa, mai dauke da bayanin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kamu da cutar Coronavirus sai dai kawai an boye labarin ne ga al’umma.

Bincike: Binciken mu ya tabbatar cewa kafar yada labarai ta CNN ba tayi wannan labarin ba, sai dai kawai wasu sun dauki wani hoton labarin CNN ne sai suka gurbata shi, ku kalli asalin hoton a kasa.

9. Shin Coronavirus ta kama ‘yan majalisa 10 da Sanatoci 15?

An ta yada wannan hoton dake kasa.

Bincike: Sai dai kamar yadda kuke gani na haka hoton yake ba a TVC wuraren da aka kewaye zaka ga alamar anyi editing din hoton ne, wato an cire asalin labarin dake jiki an maye gurbinsa da wannan.

10. Shin Jariri ya yi magana kan Coronavirus?

An ta yada wannan audio da hoton dake kasa da cewa a kasar Mali ne wani jariri ya yi bayanin kan cutututtuka da ake ta fama da su.

Bincike: Wannan hoto ya jima Internet kamar yadda kuke gani tun 2017, kuma ko a shekarar 2019 ma an yada labarin karya akansa lamarin da har BBC Hausa tayi labari mai taken “Shin da gaske an haifi jariri da rubutun dawowar Annabi Isa a hannunsa?”

Wata ce kawai ta yi Voice note na murya ta hada da hoton tana yadawa ba tare da wani tushe ba.

Note: Za mu cigaba da sabinta wannan shafin da sabbin labaran da muka samu na karya kan Coronavirus.

Zaku iya aiko mana da labarin da kuka ci karo dashi domin mu bincika ta WhatsApp a lambar waya 09035830253.

Zaku iya samun bayanan da muke wallafawa kan labaran karya da mu ke cin karo da su ta shafin mu na Facebook Sharfadi.Com

Karin Bayani: Zaku iya samun sahihan bayanai kan Coronavirus ta shafuna hukumar lura da cutuka masu yaduwa ta kasa NCDC na Twitter.

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Saurari Shirin Daga Shafukan Sadarwa

Shirin dake tattauna batutuwan da suka shafi shafukan internet da kuma rahotonni daga makarantunmu.

31-10-2019

14-09-2019

07-09-2019

31-08-2019

24-08-2019

10-08-2019

03-08-2019

26-07-2019

For Registering Domain Names, I trust DomainKing.NG

Subscribe To Our Youtube Channel

Subscribe To Khalyperh The Voice Channel

Subscribe To AU Studio On Youtube

Litattafai Cikin PDF

  1. Takardar Sanin Makama Ga Daliban Da Zasu Zana Jamb 2018 Download Now
  2. Mu Koyi Computer A Saukake Download Now
  3. Duniyar Facebook A Yau Download Now
  4. Yadda zaka fara neman kudi Online ta NNU Download Now
March 2020
M T W T F S S
 1
2345678
9101112131415
16171819202122
23242526272829
3031  

ADS

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG
error: Content is protected !!