Connect with us

Facebook

Yadda ake samun kudi ta Facebook (Rubutu na 6)

Published

on

How-to-Make-Money-Online-with-Facebook-6

Karanta rubutukan da suka gabata:

Yadda ake samun kudi ta Facebook (Rubutu na 1)

Yadda ake samun kudi ta Facebook (Rubutu na 2)

Yadda ake samun kudi ta Facebook (Rubutu na 3)

Yadda ake samun kudi ta Facebook (Rubutu na 4)

Yadda ake samun kudi ta Facebook (Rubutu na 5)

Yau kuma za mu yi magana akan wata hanya mai sauki ta samun kudi daga facebook.

Wannan hanya ita ce BRANDED CONTENT

Shahararrun masu fada aji a soshiyal midiya kamar selibiritis da ‘yan siyasa da kuma kamfanonin jarida da sauransu suna iya karbar talla su saka a shafukansu bayan sun caji kudi masu kauri.

Bari mu dauki misali da shafin Rariya, sau da dama suna saka tallan wani abu a shafin su domin yayata shi.

Ta yiwu suna yin haka a cikin tsarin bayan gida.

Duk da haka dai suna da yancin aiwatar da haka gwargwadon cajin da suke ganin ya dace da su.

Sai dai facebook ba zai taimaka musu wajen karba da alkinta musu dukiya ba.

Tsarin Branded Content na matukar taka rawa wajen tallata haja kuma yana samarwa masu shafuka makudan kudade.

Ana yinsa kuma har a instagram. Anan ne ma ya fi shahara kuma ake samun tagomashi sosai. An ce a shekarar 2014 ana cajin abin da bai wuce $50 ba, amma yanzu farashin na kai wa har $1700.

A fitattun mutanen da suke da tagomashi a wannan tsarin akwai wata da ake kira Zoe Sugg ana mata lakabi da Zeolla. Mujallar Heat da ke Ingila ta bayyana cewar duk hoton talla daya da Zeolla ta saka a instagram da Facebook tana samun kimanin £12,000 daidai da $15,700.

Rubutu masu alaka:

Menene gaskiyar hanyoyin samun kudi da ake tallatawa ta WhatsApp?

[Yau da kullum] Hanyoyi 8 da dalibi zai iya neman kudi daga makaranta

YADDA AKE SHIGA TSARIN BRANDED CONTENT

Kowanne shafi mai mabiya dubu goma zuwa sama na iya shiga wannan tsarin, sai dai Facebook suna gudanar da bincike kan abubuwa da dama kafin su bari shafinka ya soma samun kudi ta tsarin Branded Content.

Suna duba idan shafinka ya samu mabiya da yawa, kuma kana yi musu biyayya daidai gwargwado.

Idan sun ga shafinka yana bunkasa, to za su iya aiko maka wata lamba ka makala a shafinka.

Wannan lambar suna kiranta ‘Business Value’. Alamar tana daukar kamar haka:

$, $$, $$$, da kuma $$$$.

Yawan adadin alamun dala na nuna irin kima da darajar farashin shafin a wajen talla. Misali shafi mai alamar $$$$ shi ne mafi kololuwar tsada, shi kuma mai alamar $ shi ne mafi araha.

Idan mutum ya zabi makimancin farashin shafinsa, to ya bude kofa ta farko ta samun kudi daga shafin.

Daga nan sai kurum ka aikawa facebook bukatar kana so su duba shafinka a sa shi a tsarin Branded Content. Ga likau din.

https://facebook.com/help/contact/1865970047013799

Ana iya aika bukata ma ta wancan likau din tun kafin ma su ba ka lambar nan ta farashi ba, amma idan sun ba ka alamar, za ka fi saurin samun yardar su.

Idan sun duba sun ga shafin ya cancanci saka masa talla suna biyanka, to za su yi maka sako ta email.

Da zarar sun amince da shafinka, za su rika baka talla kai tsaye ta farfajiyar Content Creator tare da bayanin yadda za ka yi da shi.

Duk tallan da ka saka a shafinka ta wannan tsari za mabiyanka za su ga an rubuta ‘paid partnership’ kamar yadda aka nuna a hoton nan.

Mun kammala bayani akan Facebook Internal Ads.

Rubutuka masu alaka:

[[Express Radio]] Kasuwanci da Neman Kudi ta Yanar Gizo -Basheer Sharfadi

[Kasuwanci] Yadda Zaka Siyar da Kayanka Cikin Gaggawa ba Tare da ka Biya Wani Kudi Ba

Idan na samu lokaci zan dora akan bayanin samun kudi ta Facebook daga wajen Facebook.

Wassalam
Danladi Haruna

Facebook Comments
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ku Saurari Fasaha Radio Kai Tsaye

Note: Fasaha Radio tana aiki tsawon awanni 24 domin wayar da kan al'umma akan yadda ake amfani da fasahar zamani.

Saurari Shirin Daga Shafukan Sadarwa

Shirin dake tattauna batutuwan da suka shafi shafukan internet da kuma rahotonni daga makarantunmu.

31-10-2019

14-09-2019

07-09-2019

31-08-2019

24-08-2019

10-08-2019

03-08-2019

26-07-2019

For Registering Domain Names, I trust DomainKing.NG

Subscribe To Our Youtube Channel

Subscribe To Khalyperh The Voice Channel

Subscribe To AU Studio On Youtube

Litattafai Cikin PDF

  1. Takardar Sanin Makama Ga Daliban Da Zasu Zana Jamb 2018 Download Now
  2. Mu Koyi Computer A Saukake Download Now
  3. Duniyar Facebook A Yau Download Now
  4. Yadda zaka fara neman kudi Online ta NNU Download Now
November 2019
M T W T F S S
« Oct    
 123
45678910
11121314151617
18192021222324
252627282930  

ADS

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG
error: Content is protected !!