Connect with us

Facebook

Yadda ake samun kudi ta Facebook (Rubutu na 5)

Published

on

How-to-Make-Money-Online-with-Facebook-2

Karanta rubutukan da suka gabata:

Yadda ake samun kudi ta Facebook (Rubutu na 1)

Yadda ake samun kudi ta Facebook (Rubutu na 2)

Yadda ake samun kudi ta Facebook (Rubutu na 3)

Yadda ake samun kudi ta Facebook (Rubutu na 4)

Bayanin da ya gabata na fadi cewa dole sai shafi ya samu mabiya dubu 10 kafin a amince masa ya soma samun kudi.

Wasu na ganin irin hakilon da za a sha kafin a samu wadannan mutane. Hakika tara mabiya a shafi na da amfani sosai, don haka ma facebook suka fito da wasu tsarurruka na samarwa masu shafi wasu kudaden. Tsarin da zan yi magana a yau shi suke kira da ‘Fan Subscription’

MENE NE FAN SUBSCRIPTION

Tsari ne mai shafi watau page admin yake iya saka wa mabiya shafinsa ‘yan kudaden da za su rika biya duk wata.

Wannan tsarin ba haraji ba ne, amma gudunmawa ce daga mabiya domin nuna kaunarsu ga shafin da suke so kuma a tallafawa masu shafin.

Ta wannnan tsarin duk wanda ya amince zai rika bada gudunmawa yana biyan wasu ‘yan kudade duk wata.

Akwai wani shafi na magoya bayan Michael Jackson wanda ke da mabiya miliyan 22, yana samun kimanin dala miliyan 29 da doriya duk wata.

Mafi karancin abin da mutum zai iya bayarwa gudunmawa duk wata shi ne $4.99 kimanin naira 1800. A cikin abin da shafi ya tara, zai kwashi 30% ya turawa masu shafin abin da ya rage na 70%.

Ribar mai bayar da gudunmawar kudin ga shafin kuwa, ya hada da lambobin yabo da kuma za a iya kebe shi wasu abubuwan da ba kowa ke iya gani ba.

Kamar dai yadda ake yi a wasu jaridun. Kuma ana iya ba shi ragi kan wasu abubuwan da shafin ke sayarwa da sauransu.

Shi wannan tsarin dai ana ganin Facebook ya kwaikwaya ne daga Patreon inda suke cire 8% zuwa 12% na abinda mutum ya tara ta karkashin su. Don haka ne ma masu kwakkwafi ke ganin Facebook sun tsananta kwarai. Amma dai an fi samu sosai a facebook din.

Rubutu masu alaka:

Menene gaskiyar hanyoyin samun kudi da ake tallatawa ta WhatsApp?

[Online Business] Yadda zaka tsara karbar kudi ta internet

YADDA AKE SHIGA TSARIN FAN SUBSCRIPTION

Ya zuwa yanzu dai ba kowa ne shafi ne yake shiga kai tsaye ba, Facebook ne ke aikawa admin katin gayyatar shiga wannan tsari.

Su kuwa suna duba cancanta da kasa da kuma abubuwan da shafin yake gudanarwa.

Lokacin da suka fara tsarin cikin watan Fabrairu da ya gabata, shafuka goma kadai suka gayyata daga kasar Amerika da Ingila.

A yanzu suna gayyatar shafuka dubunnai a kowacce rana daga ko ina a fadin duniya.

Akwai yiwuwar nan gaba su rage kudin kamashon da suke zaftarewa.

Rubutu masu alaka:

[[Express Radio]] Kasuwanci da Neman Kudi ta Yanar Gizo -Basheer Sharfadi

Hanyoyi Goma Sha Takwas [18] da Zaka Iya Samun Kudi ta Internet

Mu kwana nan

Danladi Haruna

Facebook Comments
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ku Saurari Fasaha Radio Kai Tsaye

Note: Fasaha Radio tana aiki tsawon awanni 24 domin wayar da kan al'umma akan yadda ake amfani da fasahar zamani.

Saurari Shirin Daga Shafukan Sadarwa

Shirin dake tattauna batutuwan da suka shafi shafukan internet da kuma rahotonni daga makarantunmu.

31-10-2019

14-09-2019

07-09-2019

31-08-2019

24-08-2019

10-08-2019

03-08-2019

26-07-2019

For Registering Domain Names, I trust DomainKing.NG

Subscribe To Our Youtube Channel

Subscribe To Khalyperh The Voice Channel

Subscribe To AU Studio On Youtube

Litattafai Cikin PDF

  1. Takardar Sanin Makama Ga Daliban Da Zasu Zana Jamb 2018 Download Now
  2. Mu Koyi Computer A Saukake Download Now
  3. Duniyar Facebook A Yau Download Now
  4. Yadda zaka fara neman kudi Online ta NNU Download Now
November 2019
M T W T F S S
« Oct    
 123
45678910
11121314151617
18192021222324
252627282930  

ADS

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG
error: Content is protected !!