Connect with us

Facebook

Yadda ake samun kudi ta Facebook (Rubutu na 4)

Published

on

How-to-Make-Money-Online-with-Facebook-3

Karanta rubutukan da suka gabata:

Yadda ake samun kudi ta Facebook (Rubutu na 1)

Yadda ake samun kudi ta Facebook (Rubutu na 2)

Yadda ake samun kudi ta Facebook (Rubutu na 3)

Kafin mu yi nisa cikin bayanin Creator Studio bari mu yi gayauna mu kara fadada bayani akan rubutun jiya.

Da yawa suna ganin akwai wahala kwarai kafin a cike kaidojin nan da aka gindaya. Sai dai fa duba zunzurutun kudin da za a iya samu.

Facebook suna nuna cewar zomo baya kamuwa daga zaune ne. Duk da haka ga wasu hanyoyi da ake iya samu cika sharuddan cikin sauki.

  1. Samun mabiya dubu 10 ba shi da wahala matukar mutum na da abin fadawa jama’a su yaba ko ma su yi tir da shi.

Kowa na da irin dabarar da yake yi wajen jan hankalin mutane zuwa shafinsa.

Wasu na dagewa kan abin da ya shafi addini ko siyasa har ma da masu batsa da sauransu. Duk manufar itace su samu followers da likes.

Bari kuma mu yi misali da wani shafi. Kwanakin baya wasu kangararrun ‘yan dandantsa suka kutsa shafin Bulama’s Cartoon suka kwace wa mai shi ta karfi da yaji.

A lokacin kuwa ya samu mabiya sama da dubu 100. Bulama sai ya hakura ya bude wani sabon shafi mai suna New Bulama’s Cartoon ya bar musu tsohon suna saka bidiyo suna samun kudi.

Yanzu haka cikin kasa da wata biyu wannan sabon shafi ya samu mabiya kusan dubu 24. Kun ga ya samu haka ne albarkacin abubuwa masu kayatarwa da yake sakawa masu jan hankalin mutane.

Rubutu masu alaka:

[Facebook] Za’a Fara Biyan Kudi Domin Saka Story A Facebook Da Messenger

[Fasaha] Wayar Android Akan Kudi N500 Ta Farko A Africa

Bayan haka kuma ana iya ba wa facebook talla su yayata shafin ya samu mabiya da yawa ta hanyar da suke kira Boosting.

  1. Ba lallai sai kana da Dom Account kafin ka soma samun kudi daga facebook ba. Kana iya farawa kudin na taruwa har ka mallaki account din. Idan ma baka iya samu ba, alwai wadanda suke iya shige maka gaba su karbo maka sai ka basu awalaja. Shi ya sa nace aiki tare cikin kungiya na da amfani sosai anan.
  2. Ana iya zabar daga yarukan da facebook din suka amince a matsayin shi ne babban yaren da ke Bidiyon. Misali, bidiyon da aka yi da Hausa sai a zabi English a matsayin yaren da ke ciki ko kuwa a makala Subtitle.
  3. Mintuna dubu 30 da aka ambata ana nufin lokaci irin na intanet wanda ake lissafa shi adadin masu kallo a lokaci guda da kuma tsawon lokacin da aka kalla. Misali, idan aka kalli bidiyo mai tsawon minti 3 sau dubu, to ana da mintuna dubu 3 kenan a lokaci guda. Cikin kwana goma ana iya hada minti dubu 30.
  4. Bai zama lallai sai ka shiga makarantar nan ta horaswa daga Facebook ba. Sai dai tana amfani sosai, domin har satifiket ake ba wa zaratan dalibai. Hakan na sa wa mutum ya zama na daban daga sauran Ayyuhan nasun Facebook.

Ga shafin makarantar
https://facebook.com/business/learn/

Rubutu masu alaka:

[Facebook] Yadda Za’a Dinga Biyan Masu Dora Video A Facebook Kudi

[Instagram] Yadda Instagram Ke Samun Kudin Shiga

Za mu kwana anan

Danladi Haruna

Facebook Comments
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ku Saurari Fasaha Radio Kai Tsaye

Note: Fasaha Radio tana aiki tsawon awanni 24 domin wayar da kan al'umma akan yadda ake amfani da fasahar zamani.

Saurari Shirin Daga Shafukan Sadarwa

Shirin dake tattauna batutuwan da suka shafi shafukan internet da kuma rahotonni daga makarantunmu.

31-10-2019

14-09-2019

07-09-2019

31-08-2019

24-08-2019

10-08-2019

03-08-2019

26-07-2019

For Registering Domain Names, I trust DomainKing.NG

Subscribe To Our Youtube Channel

Subscribe To Khalyperh The Voice Channel

Subscribe To AU Studio On Youtube

Litattafai Cikin PDF

  1. Takardar Sanin Makama Ga Daliban Da Zasu Zana Jamb 2018 Download Now
  2. Mu Koyi Computer A Saukake Download Now
  3. Duniyar Facebook A Yau Download Now
  4. Yadda zaka fara neman kudi Online ta NNU Download Now
November 2019
M T W T F S S
« Oct    
 123
45678910
11121314151617
18192021222324
252627282930  

ADS

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG
error: Content is protected !!