Connect with us

Facebook

Yadda ake samun kudi ta Facebook (Rubutu na 3)

Published

on

Karanta rubutukan da suka gabata:

Yadda ake samun kudi ta Facebook (Rubutu na 1)

Yadda ake samun kudi ta Facebook (Rubutu na 2)

A gabatarwa, na bayyana cewa Facebook na biyan jama’a cikin tsarin da suke kira ‘Ad Break’.

MENE NE AD BREAK?

Ad break tsari ne daga Facebook wanda suke bayar da dama ga masu dora bidiyo su saka talla a farko ko tsakiya ko karshen bidiyon.

Kowanne talla akwai abin da suke biya gwargwadon tsawonsa.

Mutum na iya samun kimanin dala 150 duk wata a kowanne bidiyon da yake cikin tsarin ad break.

Ka ga idan kana saka bidiyo daya kullum kana iya samun kimanin dala 4500 duk wata.

Ana tsara yadda ake son tallan ya fito a wata manhaja mai suna ‘Creator Studio’ wadda facebook din ya tanada ga masu shafuka.

Rubutu masu alaka:

[Kasuwanci] Yadda Zaka Siyar da Kayanka Cikin Gaggawa ba Tare da ka Biya Wani Kudi Ba

[Facebook] Yadda Za’a Dinga Biyan Masu Dora Video A Facebook Kudi

CANCANTAR SHIGA TSARIN AD BREAK

Akwai matakai da sharadai da sai shafi ya cika su kafin ya shiga tsarin Ad-break. Bari mu bi su daki – daki.

 • Dole sai wanda ya kai shekara 18 da haihuwa zuwa sama.

*Wajibi ne ka kiyaye dokoki da sharudan Facebook, Kada sunanka yayi kaurin suna a fagen taratsi irin na intanet.

 • Wajibi ne mutum ya zamana yana da asusun banki mai karbar daloli (Dom Account) a ƙasashen da tsarin ke aiki in ban da Seremiya da Iraki da Sudan da Cuba da kuma Syria.

 • Dole ne shafin da za ka saka bidiyon ya zama yana da mabiya a kalla dubu goma.

 • Dole bidiyon ya an samu kallon bidiyo sau dubu 30 a shafinka. Kuma masu kallon sun iya jure kallon akalla na minti daya.

Duk wadannan a cikin kwanaki sittin da suka gabata.

 • Dole kuma bidiyon ya zama original na ainihi da ka kirkira ba satar fasaha ba ne kuma ana magana da yaren da facebook ta aminta da shi.

In kuma ba da amintaccen yare ake magana bidiyon ba, to sai a saka fassara da yaren da aka amince da shi.

 • Kuma ana so ka kalli wani bidiyo na minti biyu da ke koyar da yadda ake shiga tsarin.

 • A karshe akwai makarantar Facebook Business da suke bayar da horo na musamman akan yadda ake kwarewa har akai ga samun kudi sosai.

Mai bukata sai ya yi magana na ba shi adireshin makarantar.

MAFI KARANCIN KUDIN FACEBOOK KE BIYA
Facebook na biyan mutane duk wata idan kudin sun kai akalla dala 100. Idan misali a watan Janairu ka samu kudin tallanka sun kai dala 100, to a sati na uku na Fabrairu za su aiko maka da su.

Idan kuwa ba su kai ba, sai ka jira na uku na watan Maris su aiko maka da abin da ka samu a watan Janairu da Fabrairu.

Za mu kwana nan kafin mu kawo yadda ake saka talla a bidiyo daga Creator Studio.

Rubutu masu alaka:

[[Express Radio]] Kasuwanci da Neman Kudi ta Yanar Gizo -Basheer Sharfadi

[YouTube] Yadda Ake Samun Kudi Ta YouTube

Facebook Comments
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ku Saurari Fasaha Radio Kai Tsaye

Note: Fasaha Radio tana aiki tsawon awanni 24 domin wayar da kan al'umma akan yadda ake amfani da fasahar zamani.

Saurari Shirin Daga Shafukan Sadarwa

Shirin dake tattauna batutuwan da suka shafi shafukan internet da kuma rahotonni daga makarantunmu.

31-10-2019

14-09-2019

07-09-2019

31-08-2019

24-08-2019

10-08-2019

03-08-2019

26-07-2019

For Registering Domain Names, I trust DomainKing.NG

Subscribe To Our Youtube Channel

Subscribe To Khalyperh The Voice Channel

Subscribe To AU Studio On Youtube

Litattafai Cikin PDF

 1. Takardar Sanin Makama Ga Daliban Da Zasu Zana Jamb 2018 Download Now
 2. Mu Koyi Computer A Saukake Download Now
 3. Duniyar Facebook A Yau Download Now
 4. Yadda zaka fara neman kudi Online ta NNU Download Now
November 2019
M T W T F S S
« Oct    
 123
45678910
11121314151617
18192021222324
252627282930  

ADS

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG
error: Content is protected !!