Da farko ya zama wajibi na bayyana cewa, kada a yi tsammanin mutum kurum zai yi zama irin na randa a daki yana jiran zubar ruwan kudi daga Facebook. Tilas sai an yi aiki da gaske kuma an bata lokaci mai yawa kafin haka ya cimma ruwa.
Don haka idan ka san nufin ka zaman jiran gawon shanu ne, to nan ba muhallinka ba ne.
Idan tsammanin ka zauna ka bararraje kana sakace kudi na zubo maka kamar ruwan sama daga Facebook, to lallai an ci dununka.
Wannan tunani daidai yake da na mai neman ƙahon kare.
Na biyu, wajibi ne ka guji halin dantsako, samu ka guji dangi.
Saboda ɗawainiyar ta fi karfin aikin mutum daya.
Idan ka ce komai za ka yi da kanka, a karshe za a yi nama ya dahu romo danye.
Don haka aiki tare da sauran al’umma kuna karfafa junanku da shawarwari.
Na uku kuma matakan samun kudi a Facebook da ma intanet kamar shiga kogi ne, gwargwado zurfin wajen gwargwadon inda zai kawo maka.
Idan kana bukatar kudancewa a dare daya, wajibi ne ka zuba hannun jarin daloli a inda ya dace.
Samun kudi a facebook ya danganta da irin kokarin mutum da himmarsa wajen samar da rubutu ko bidiyo original ba na kwaikwayo ba, Ya kuma danganta da irin hanyoyin da aka bi.
Rashin dacewa ne ke saka wasu na zuba kudinsu a wuraren bogi, inda ake musu romon baka, a karshe a bar su da kuturun bawa.
Sha’anin kudi a intanet yana bidar takatsantsan da dogon bincike kafin ka shiga.
Idan ba ka san kan abin ba, yana da kyau ka tambayi wadanda suka sani.
Wasu manazarta sun bayyana cewar, a cikin hanyoyin samun kudi goma na intanet, tara duk karairayi ne da damfara.
Don haka, wajibi ne mu yi aiki wurjanjan domin sanin dabaru na hakika ba na hakilon neman kudi a intanet ba.
Facebook Comments