Connect with us

WhatsApp

Menene gaskiyar hanyoyin samun kudi da ake tallatawa ta WhatsApp?

Published

on

Assalamu Alaikum, akwai wani abun dake yawo a kafafen sada zumunta musamman a manhajar WhatsApp batun Bitcon Investment, sun shirya tsaf mutanen kuma suna da tsari wanda ke kama da gaske.

Akwai bukatar fadakarwa kawarai da gaske.

Suna aiki ne da sunan nan da na aika maka, da zaran mutum yayi rijista da su zasu zuba mar kudin sannan duk wanda ya shigo daga baya ko ba kai ne ka kawo shi ba indai ka riga shi shiga to zaka ke samun qarin coins (kudi) sannan ni sun kirani sun tambayeni shin ta banki nake bukatar a bani kudin sai nace musu eh, shi kenan sai suka turo min code na wasu lambobi sai dai sender information din ba lamba ba ne sunan da ya bayyana shi ne WhatsApp wanda ya yi kama da saqon Kamfanin WhatsApp.

Wannan tambaya ce da daya daga cikin mabiya shafin Sharfadi.com ya aiko mana, kuma mun mika ta ga wani kwararre a bangaren kimiyya da fasahar sadarwa Mallam Danladi Haruna, ga kuma amsar da ya bamu.

 

A dan binciken da na yi a takaice babu wani investment da kamfanin WhatsApp ke yi domin biyan mutum a wasu lokuta.

Shi kansa kamfanin subsidiary ne don haka ba shi da ikon shiga kasuwar hannun jari sai da iznin iyayensa watau Facebook, wanda su ne masu mallakin dandalin WhatsApp.

To amma a gefe daya kuma, akwai mutane da dama da suke amfani da Whatsapp domin cinikin hannun jari, su wadannan mutane sun rabu gida biyu, kaso na farko sun kirkiri wani bot (script) da yake taimaka musu wajen hada-hada.

Wato maimakon yadda aka saba ka aika sako (text) zuwa wata lamba sai a baka option, sai suke amfani da whatsapp, Idan kana da account da su za su ba ka software ka saka a wayarka, sai su baka wata lamba da za ka rika aikawa sako ta whatsapp kana sarrafa account dinka ta nan.

Babba daga masu irin wannan shi ne, lite.im. Suna da lambar bot, +1 786-916-7825 wadda ake aikawa sako ana sarrafa account din Bitcoin ko Litecoin.

Kaso na biyu kuma shi ne wadanda ke bude groups a whatsapp domin cinikin Bitcoin da sauransu.

Mafi yawan wadannan duk na gaibu ne babu komai ciki sai damfara.

Sun karkasu da dama kamar hyip, mlm, cryptosearch da sauransu.

Da dama suna da dabarun da suke jan hankalin mutane domin su yarda da su.

Suna iya kirkirar sako (message) daga kwamfiyuta su saka username zuwa WhatsApp ko wani abu da zai ja hankali da sauransu.

Ban yi sa’ar gamuwa da ko mutum daya da ya samu riba da su ba, amma na samu wadanda suka afka tarkonsu da dama.

Yadda zaka gane ingancin su ko akasin haka.

  • Tabbatar da cikakken adireshinsu.

  • Tabbatar da rijsita da hukumar CAC

  • Tabbatar da rijista da hukumar NSE

  • Tabbatar da rijista da hukumar SEC

Sauran rijista kuma da yansanda, efcc, icpc da sauransu.

Sai dai fa har yanzu shugabannin kasashe ba su yarda da cryptocurrency ba, duk da yadda yake bunkasa a duniya.

Rubutu masu alaka:

[Yau da kullum] Hanyoyi 8 da dalibi zai iya neman kudi daga makaranta

[Blogging] Manyan Hanyoyi Uku (3) da Zaka Samu Kudi da Blog Dinka

[Tattali] Wurare Biyar (5) da Muke Yin Asarar Kudi ba Tare da Mun Sani Ba

Facebook Comments
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ku Saurari Fasaha Radio Kai Tsaye

Note: Fasaha Radio tana aiki tsawon awanni 24 domin wayar da kan al'umma akan yadda ake amfani da fasahar zamani.

Saurari Shirin Daga Shafukan Sadarwa

Shirin dake tattauna batutuwan da suka shafi shafukan internet da kuma rahotonni daga makarantunmu.

31-10-2019

14-09-2019

07-09-2019

31-08-2019

24-08-2019

10-08-2019

03-08-2019

26-07-2019

For Registering Domain Names, I trust DomainKing.NG

Subscribe To Our Youtube Channel

Subscribe To Khalyperh The Voice Channel

Subscribe To AU Studio On Youtube

Litattafai Cikin PDF

  1. Takardar Sanin Makama Ga Daliban Da Zasu Zana Jamb 2018 Download Now
  2. Mu Koyi Computer A Saukake Download Now
  3. Duniyar Facebook A Yau Download Now
  4. Yadda zaka fara neman kudi Online ta NNU Download Now
November 2019
M T W T F S S
« Oct    
 123
45678910
11121314151617
18192021222324
252627282930  

ADS

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG
error: Content is protected !!