Connect with us

Facebook

[Facebook] Ba Hackers ne ke turawa mutane sakon bidiyo ta inbox ba

Published

on

facebook message that says video and your name

DALILI DA TUSHEN HOTUNAN LIKAU A JAKAR SAKONNI

ABUBUWAN LURA
✓ Gidan gwallet.com ke yada likau din amma ba hackers ba ne.
✓ Wanda ke tura wa bai ma san yana aikawar ba.
✓ Ana amfani da tsarin Google wajen tsinto wanda zai aika da sakon da wanda za a aikawa.
✓ Facebook na iya toshe asusun mutum saboda gudun kishiya.
✓ Da zarar ka ga sakon ya diro maka, kurum ka goge shi baki alaikum.

MU YI WAIWAYE
Farfajiyar duniyar Intanet sarari ne da kowa wanda ya san abin da yake yi zai tara makudan kudade ta hanyoyi da dama. Masanan kimiyyar intanet suna kiran ta da suna ‘Online Real Asset’. Kowa yana iya shiga ya ci arziki kuma ya bar arziki inda yake.

Babbar hanyar da ake bi a samu arziki a intanet ita ce dabarar samun maziyarta masu yawa a farfajiyar gidanka. Wannan ana kiransa ‘traffic’. Duk gidan da ba shi da traffic a intanet, kana iya daukarsa tamkar kangon gidan da ake zuba juji a ciki.

Saboda rububin neman traffic aka samu wasu manyan kanfanoni da ke kawo dabarun haka cikin sauki. Kamfanin Google da yake lambawan a gidajen intanet baki daya, ya samar da wata manhaja ko masarrafi da ake kira Google Analytics ko GA a takaice. Amfanin GA na da yawa kwarai, daya daga ciki shi ne nakaltar dabi’un mutum a intanet da abubuwan da ya fi son gani da gidajen da ya fi ziyarta da irin rubutun da yake yi da sauran abubuwa da yawa. Ta amfani da GA ana iya gane dabi’un mutanen gari guda sukutum a intanet.

Rubutuka masu alaka:

[Facebook] Yadda Zaka Kare Facebook Dinka daga Blocking ko Hacking

[Facebook] Hacking da Disable da Abubuwan Dake Jawosu a Facebook

[Hacking] Hanya ta Farko da Akebi Wajen Satar Account din Facebook

Ku duba irin sakonnin da ake aikawa mutane a kasa:

GAME DA GWALLET.COM
Wannan gida ne da aka bude shi a shekarar 2008 kuma zai tsaya a shekarar 2021. Yana tallata hajar intanet a duniya ta hanyoyi da dama wadanda suke na zahiri da badini. Kamfanin Radiumone da ke jihar Kalifoniya ta Amrika ne ya samar da shi. Kuma babban gidan GoDaddy ne yake kula da shi. Kuma shi ne gida na 26,719, a ma’aunin alexa. Wanda yana nufin gidan na ci duniyarsa da tsinke.

A kiddigar da gidan rankchart ya yi, gwallet.com na jawowa kamfaninsa traffic kimanin dubu 10 a kullum. Lissafa duk traffic daya a matsayin dala daya, nawa kenan a duk wata?

Ta hanyar amfani da GA gwallet ke tsinto wanda zai ba wa sallahu ya aikawa wani a matsayin likau kamar na bidiyo. Duk wanda ya latsa likau din maimakon ya ga bidiyonsa na motsawa, sai ya ga wani gidan ya bude. Su kuma gwallet su samu kudi ta haka. Wanda ya ga an aika masa sakon, ya yi karatun ta nutsu, ta yiwu a kasa da mako guda ya bude wani bidiyo ta hanyar likau ko kuma yana shiga irin wasan nan da ake yi a facebook wanda ake kira Nametest da sauransu.

Shi kuma wanda yake aikawa duk da bai san yana aikawa din ba, ta yiwu a kasa da mako guda ya latsa wani likau din ko ya raba wani likau ta hanyar ‘sharing’.

Ko ma dai menene ba hackers ba ne kamar yadda wasu ke zargi, sai dai facebook na iya toshe mutum bisa horo. Domin kuwa dabara ce ta sa gwallet ya ki biyan facebook su yi musu talla sai yake bin mutane ta bayan fage. Haka kuma likau din na iya kunsar wani abu da ake kira ‘malicious code’ wanda shi kuma ana iya dabar da shi wajen satar bayanan mutum amma fa idan ya bada username da password dinsa. Wannan ake kira ‘phishing’. Maganin abin kurum ka goge sakon da zarar ya shigo jakarka. Fakat.

BANBANCIN GWALLET DA HACKERS
Abin da ya sa na ce ba gwallet da ke aika bidiyon likau ta jakar sakonni ba hackers ba ne shi ne:

• Hackers na amfani da wata dabara da ake kira ‘spoofing’ duk kwakwar mutum ba zai iya gane wani abu game da su ba.

• Masu rangwamen matsayi a hackers din ne ke amfani da ‘domain mask’ ko ‘identity protect’ don kada a gane daga inda suke da wanda yake mallakinsu. Shi kuwa gwallet.com komai nasa a bude yake.

• Hackers na gasken tuni sun daina aiki da dabarar ‘social engineering’ suna iya yanka duk asusun da suka ga dama matukar sun iya aika masa sako walau ya bude ko bai bude ba. Na tabbata da hackers ne ba wanda zai samu damar zuwa neman bahasi. Da tuni sun sheke mutum!

• Facebook basu dauki lamarin hacking din asusu da sauki ba. Da tuni an shiga kwarototo kan wannan lamari kamar dai yadda aka yi a lokacin bayyanar virus mai suna ‘Reila Odinga’ da irin su ‘Heart Bleeding’ da kuma Facebook Virus da ake kira ‘Is that your videos?’

SHAWARA
Lokaci ya yi da Hausawa za mu fi maida hankali wajen samun ‘yan daloli a intanet maimakon bari wasu suna ci da gumin datar da kullum muke hadiya fiye da tuwo ko magani.

Rubutu: Mallam Danladi Haruna.

Rubutuka masu alaka:

[Facebook] Kutse a Facebook, rigakafi da yadda ake dawo da account din da aka sace

[Facebook] Yadda Ake Dawo Da Facebook Din da Akayi Disable

[Facebook] Yadda Ake Dawo Da Facebook Din Da Aka Sace

[Hacking] Hanya ta Biyar da Akebi Wajen Satar Account din Facebook

Facebook Comments
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ku Saurari Fasaha Radio Kai Tsaye

Note: Fasaha Radio tana aiki tsawon awanni 24 domin wayar da kan al'umma akan yadda ake amfani da fasahar zamani.

Saurari Shirin Daga Shafukan Sadarwa

Shirin dake tattauna batutuwan da suka shafi shafukan internet da kuma rahotonni daga makarantunmu.

31-10-2019

14-09-2019

07-09-2019

31-08-2019

24-08-2019

10-08-2019

03-08-2019

26-07-2019

For Registering Domain Names, I trust DomainKing.NG

Subscribe To Our Youtube Channel

Subscribe To Khalyperh The Voice Channel

Subscribe To AU Studio On Youtube

Litattafai Cikin PDF

  1. Takardar Sanin Makama Ga Daliban Da Zasu Zana Jamb 2018 Download Now
  2. Mu Koyi Computer A Saukake Download Now
  3. Duniyar Facebook A Yau Download Now
  4. Yadda zaka fara neman kudi Online ta NNU Download Now
November 2019
M T W T F S S
« Oct    
 123
45678910
11121314151617
18192021222324
252627282930  

ADS

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG
error: Content is protected !!