Connect with us

WhatsApp

Shin ana iya hacking din WhatsApp?

Published

on

Menene WhatsApp?

WhatsApp daya ne daga cikin dandalin sada zumunta wanda yake baiwa mutum damar aikawa da sakon sauti ko video, hoto da kuma rubutu, kai har ma da kira kai tsaye cikin video da audio.

Zuwa Yanzu WhatsApp yana da mutane masu amfani dashi kimanin Biliyan Biyu da Miliyan Dari Biyu a fadin duniya.

WhatsApp mallakar kamfanin facebook ne.

KARANTA:

[WhatsApp] Ma’anar WhatsApp Business da Abubuwan da ya kunsa

[WhatsApp] Abubuwa (16) da GB WhatsApp ya tsere asalin WhatsApp dasu

Yadda Ake Bude WhatsApp

Yadda ake bude WhatsApp shine za kaje Play Store din wayarka, ko kuma a turo maka whatsApp din sai ka bude zai baka dama kamar yadda kake gani a kasa, sai ka zabi code din lambar waya na kasar ka, misali a Nigeria +234 daga nan sai ka sanya lambarka amman banda zero (0) na farko sai ka dannan continue/next.

WhatsApp zaiyi loading sannan zasu aika maka da sakon code zuwa ga layin naka sai ka dauko ka saka, sannan kayi gaba, idan kuma layin ma yana kan waya to zai iya wucewa ba tare da ka sanya code din ba, wanda ake kira “automatic detected”

Daga nan zai budo maka ka saka sunan da kuma Profile Picture shikenan WhatsApp dinka ya budu.

Shin ana iya hacking din WhatsApp?

Eh ana yin hacking din WhatsApp sai dai a baya yana da kamar wuya, amma a yanzu abin ya sauya, domin kuwa ana iya yin hacking din WhatsApp ta hanyar amfani da whatsapp dinka ayi scanning (wato a haska camera a dauki hoton code na WhatsApp din ka) ko kuma ta hanyar a kira ka a waya ayi maka dabara a aiko maka da code (wasu lambobi) kai kuma ka tura daga nan  shikenan an sheke maka account dinka.

Hanyoyin da zaka bi domin kare Account dinka na WhatsApp sune:

 1. Ka lura da kyau da duk wanda zaka baiwa wayar ka.
 2. Kada ka yarda wani ya kiraka a waya ko yayi maka dabara ya tura wasu code ta wayarka ya karba.
 3. Ka shiga “Settings”
  1. Ka shiga “Account”
  2. Sai ka shiga “Two step verification”
  3. Sai ka sanya lambobi guda 6 wadannan ba zaka iya mantawa ba.
  4. Zaka sake sanya lambobin sannan kayi “Enabled”

Karanta wadannan rubutukan:

[WhatsApp] Yadda Zaka Dawo da Lambar da Aka Dakatar Daga Yin WhatsApp

[WhatsApp] Dalilan da Yasa WhatsApp Ke Dakatar da Mutum daga WhatsApp

Facebook Comments
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ku Saurari Fasaha Radio Kai Tsaye

Note: Fasaha Radio tana aiki tsawon awanni 24 domin wayar da kan al'umma akan yadda ake amfani da fasahar zamani.

Saurari Shirin Daga Shafukan Sadarwa

Shirin dake tattauna batutuwan da suka shafi shafukan internet da kuma rahotonni daga makarantunmu.

31-10-2019

14-09-2019

07-09-2019

31-08-2019

24-08-2019

10-08-2019

03-08-2019

26-07-2019

For Registering Domain Names, I trust DomainKing.NG

Subscribe To Our Youtube Channel

Subscribe To Khalyperh The Voice Channel

Subscribe To AU Studio On Youtube

Litattafai Cikin PDF

 1. Takardar Sanin Makama Ga Daliban Da Zasu Zana Jamb 2018 Download Now
 2. Mu Koyi Computer A Saukake Download Now
 3. Duniyar Facebook A Yau Download Now
 4. Yadda zaka fara neman kudi Online ta NNU Download Now
October 2019
M T W T F S S
« Sep   Nov »
 123456
78910111213
14151617181920
21222324252627
28293031  

ADS

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG
error: Content is protected !!