Connect with us

Blogging

[Blogging] Ma’anar Google AdSense da abubuwan da yakamata ka sani Kafin ka nema

Published

on

Google Ad sense and how to apply for google adsense in hausa language

Menene Google AdSense?

Google AdSense sashi ne da kamfanin google keda shi wanda yake karbar tallukan mutane, shi kuma ya tallatawa al’umma, cikin hanyoyin da yake amfani dasu wajen tallatawa al’umma akwai amfani da shafukan abokanan talla, misali kamfanin kwalliyar mata na Samira Zakirai Beauty Secret ya baiwa kamfanin Google talla cewa ya tallata masa abubuwan da yake, ga mutane kaza ‘yan yanki kaza to google zai duba cikin abokanan tallansa misali Sharfadi.com tana cikin abokanan google to suna iya sanya tallan da aka basu a shafinmu kamar yadda kuna iya ganin tallansu a wannan post din, mu kuma sai su dinga biyan mu, idan mutane sunbi tallan ta shafinmu.

RUBUTUKA MASU ALAKA:

[Blogging] Ma’anar Blogging da Abubuwan da Ya Kunsa

[Blogging] Abubuwa Bakwai (7) Da Yakamata Ka Sani Kafin Fara Blogging

Abubuwan da Yakamata ka Sani Kafin Ka Nemi Google Ads:

A baya kafin na nemi Ads abinda nake ji akansa shine baya yi, gan-gance duk shirmene, an saremin gwiwa sosai, amma a zahirin gaskiya ba haka yake ba, babban abinda ke baiwa jama’armu matsala shine rashin cika dukkan doka da ka’idar da google din keda shi, akwai abubuwa da dama da yakamata ka lura dasu kafin ka nemi google ads.

 1. Ya zama shafinka yana samun maziyarta (masu shiga) na yau da kullum.
 2. Ya zama rubutun (content) din naka ne bana wani ba, kada ka dauki rubutun wani ka saka, musamman wanda ya riga ya saka a shafinsa.
 3. Rubutunka ya zama bai saba da doka da ka’idar google ba, Misali basa karbar shafin da yake magana kan kiwon lafiya ko na batsa.
 4. Ya zama shekarunka sun kai 18 zuwa sama, idan shekarunka basu kai ba akwai bukatar iyaye ko mahukuntanka su shiga ciki.

SHIGA NAN DOMIN DUBA DOKA DA KA’IDOJIN DA GOOGLE ADSENSE KE DASHI

 1. Kafin ka nema ka tabbatar kana da kwararan rubutu akalla guda 20, kuma son samu kowanne ka hada mai kalmomi akalla dubu guda (1000).
 2. Ka tabbatar shafinka yana da bangaren “About Page” “Contact Us, da Privacy Policy” (game da shafin, hanyoyin tuntubarmu da kuma doka da sharudan amfani da shafin).
 3. Kuma Privacy Policy din ya zama ya dave da Privacy Policy na Google.

SHIGA NAN DOMIN DUBA DOKAR DA GOOGLE ADSENSE KE DASHI KAN CONTENT

SHIGA NAN DOMIN KA KIRKIR PRIVACY POLICY DINKA

Zamu dakata a nan sai a rubutu na gaba mai taken “Yadda Zaka Nemi Google AdSense”.

Basheer Sharfadi

Social Media Strategists.

26-08-2019.

RUBUTUKA MASU ALAKA:

[Blogging] Yadda zaka binciko Keyword domin SEO dinka

Saurari Shirin Daga Shafukan Sadarwa 27-07-2019

[Blogging] Hanyoyi 6 da zaka sanya mutane su dinga shiga Blog dinka

[Blogging] Hanyoyi Hudu (4) da Zaka Samu Traffic a Shafinka ta Social Media a 2019

Facebook Comments
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Continue Reading
1 Comment

1 Comment

 1. Abdoul madjidou

  August 27, 2019 at 11:47 pm

  Allah ya taimaka akan wannan wayar da kan alumma da kake musamman hausa Allah ya saka da alkhairi a gaskiya alumma na bukatar irinku

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ku Saurari Fasaha Radio Kai Tsaye

Note: Fasaha Radio tana aiki tsawon awanni 24 domin wayar da kan al'umma akan yadda ake amfani da fasahar zamani.

Saurari Shirin Daga Shafukan Sadarwa

Shirin dake tattauna batutuwan da suka shafi shafukan internet da kuma rahotonni daga makarantunmu.

31-10-2019

14-09-2019

07-09-2019

31-08-2019

24-08-2019

10-08-2019

03-08-2019

26-07-2019

For Registering Domain Names, I trust DomainKing.NG

Subscribe To Our Youtube Channel

Subscribe To Khalyperh The Voice Channel

Subscribe To AU Studio On Youtube

Litattafai Cikin PDF

 1. Takardar Sanin Makama Ga Daliban Da Zasu Zana Jamb 2018 Download Now
 2. Mu Koyi Computer A Saukake Download Now
 3. Duniyar Facebook A Yau Download Now
 4. Yadda zaka fara neman kudi Online ta NNU Download Now
August 2019
M T W T F S S
« Jul   Sep »
 1234
567891011
12131415161718
19202122232425
262728293031  

ADS

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG
error: Content is protected !!