Connect with us

Online Business

[WhatsApp] Ma’anar WhatsApp Business da Abubuwan da ya kunsa

Get Started with WhatsApp Business in Hausa

[WhatsApp] Ma’anar WhatsApp Business da Abubuwan da ya kunsa

Menene WhatsApp Business?

WhatsApp Business manhajar WhatsApp ce da akayi ta domin masu sana’o’I yadda za suyi amfani da ita, wajen tallatar hajarsu, WhatsApp business zai baka damar alaka da tattaunawa da abokanan kasuwancinka wato Costomers cikin sauki.

Zaka iya amfani da asalin WhatsApp a matsayin Personal WhatsApp dinka, sannan ka bude WhatsApp Business domin sana’arka.

Abubuwan da Zaka Iya Yi da WhatsApp Business:

Business Profile: Zaka bude Profile din kasuwancinka ta WhatsApp yadda mutum yana dubawa zai ga bayanan sunan kamfaninka/sana’arka, Adireshinka, da kuma contact din da za’a iya tuntubarka, kai harma da link na website dinka in kana dashi, ko kuma na facebook page dinka, wato dai duka wannan bayanan maimakon sai mutum ya tuntubeka sannan kayi masa, kawai yana dubawa lambarka ta WhatsApp Business zai gansu.

Business Messaging Tools: Zai baka karin kayan kawata sako, kamar Auto Responder da zata dinga amsawa mutum sako nan take, da zarar ya aiko maka da sako koda kuwa baka online, shine zaka ga idan ka yiwa mutum magana a WhatsApp sai kaga anyo maka reply da cewa baya kusa amma in yazo zai duba sakonka.

WhatsApp Web: Zai baka dama ka amsa sakonnin costumers dinka ta hanyar amfani da Computer, tamkar dai WhatsApp din da ake yi ta Computer.

Shin zaka iya hada WhatsApp da WhatsApp Business a Waya Daya?

Eh, zaka iya hada su amman kowanne da lambarsa daban, ba zai yiwu ka budeso da lamba da yaba.

Note: a WhatsApp Messenger zaka iya yin backup na sakonninka amma a WhatsApp Business ba’a yin restoring a dawo da sakonni sai dai in kayi saving dinsu a wayarka.

Yadda ake bude WhatsApp Business:

Ka shiga rumbin manhajoji na PlayStore ko App Store na wayarka sai ka nemo WhatsApp Business idan ka sauke, sai ka shiga kayi register, zaka shigar da lambar wayarka tamkar dai yadda ake register da WhatsApp Messenger, banbancin kawai shine shi zaka zabi Category wato bangare ko nau’in kasuwancinka, daga nan zai bude zaka fara amfani dashi.

Zan dakata a nan sai a rubutu na gaba.

RUBUTUKA MASU ALAKA:

[WhatsApp] WhatsApp da Abubuwan da ya kunsa, da dalilan dake jawo banning –Arewa Radio 93.1 Kano

[WhatsApp] Yadda Zaka Dawo da Lambar da Aka Dakatar Daga Yin WhatsApp

[WhatsApp] Yadda Zaka Magance Matsalar Shan Data Da Cinye Storage Daga WhatsApp Group

[WhatsApp] Yadda Zaka Dakatar da Posting Sai Iya Admin Kadai a Group Din WhatsApp

Basheer Sharfadi

Social Media Strategists.

09-07-2019.

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Saurari Shirin Daga Shafukan Sadarwa

Shirin dake tattauna batutuwan da suka shafi shafukan internet da kuma rahotonni daga makarantunmu.

31-10-2019

14-09-2019

07-09-2019

31-08-2019

24-08-2019

10-08-2019

03-08-2019

26-07-2019

For Registering Domain Names, I trust DomainKing.NG

Subscribe To Our Youtube Channel

Subscribe To Khalyperh The Voice Channel

Subscribe To AU Studio On Youtube

Litattafai Cikin PDF

  1. Takardar Sanin Makama Ga Daliban Da Zasu Zana Jamb 2018 Download Now
  2. Mu Koyi Computer A Saukake Download Now
  3. Duniyar Facebook A Yau Download Now
  4. Yadda zaka fara neman kudi Online ta NNU Download Now
July 2019
M T W T F S S
1234567
891011121314
15161718192021
22232425262728
293031  

ADS

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG
error: Content is protected !!