[Computer] Abubuwan da zaka lura dasu a lokacin siyan Computer
Jama’a Assalamu Alaikum a yau zanyi magana akan abubuwan da yakamata mutum ya lura dasu a yayin da ya tashi siyan Computer.
Akwai abubuwa da dama da yakamata wanda ke shirin siyan Computer ya lura dasu, amma ga wasu daga cikinsu.
Saboda me kake son siyan Computer?
Akwai bukatar mutum yayi nazari sosai shin akanme yake son siyan computer? Mai zaiyi da ita? Wannan zasu taimaka masa wajen sanin wacce tafi can-canta dashi.
Desktop/Laptop: Akwai bukatar ka fara yin nazari shin Desktop kake bukata ko Laptop, ina bukatar computer domin yin rubutukana da adanawa ko don yaran gida su dinga koya, to ina bukatar Desktop idan bamu da matsalar wuta, a’a ina son wadda zan dinga ayyukana sannan in tafi da ita duk inda nake so sai na nemi Laptop.
Battery: akwai bukatar ka tabbatar da ingancin batir din Computer musamman ma Laptop domin gudun kada ka samu computer din da bata rike batir, kunsan batir yana da matukar mahimmanci a computer sosai da sosai.
Processor, akwai akwai bukatar ka tabbatar da wane irin Arctecture Processor ne da computer din Intel ko Nvidia, a nan dai Intel, yafi gudu da kuma saukin amfani domin mafi yawan computer dake da Nvidia kan fuskanci matsalolin daukar zafi da makamantansu.
Yadda zaka duba bayanan Computer dinka shine:
Ka danna “Windows + E”, ko ka shiga “My Computer” sai kaje kan “This PC” ko “My Computer” a wani Windows din, sai kayi “Right Click” zai baka zabi da dama sai ka shiga “Properties” zai budo maka bayanan.
Sannan zaka iya danna “Windows” + R” zai budo maka wajen rubutu sai ka rubuta “msInfo32” sai ka danna “Enter”shikenan zai budo maka wuraren bayanan computer dinka da dama sai ka duba.
Storage/Harddisck/Rom: akwai bukatar duba girman Memory din, misali idan ina son computer domin nayi gyaran bidiyo ko harkar downloading to kana bukatar samun mai space da yawa domin aikin da zakayi.
RAM: shima akwai bukatar tabbatar da RAM nawa computer din take dashi, yawan Ram zai taimaka mata wajen yin gudu sosai fiye da wadda bata dashi da yawa.
32,86 da 64 Bit: misali idan kana son computer domin yin amfani da word, excel, ko su Adobe Audition duka mai 32 bit zata iya yi, amman idan kana bukatar kowace soft ware ta dinga bude maka akwai bukatar ka samu 64 bit, Computer mai 32 bit tana iya daukar Ram 4Gb ne kadai, yayin da 64 bit zai iya daukar har sama da 196GB.
Cables: akwai bukatar ka tabbatar da wayoyin Cables da suka zo dashi shin suna da kyau, chager da sauransu idan Desktop ce, in Laptop ce ka tabbatar da ingancin chager din.
Connectivity: akwai bukatar ka lura ingancin ramukan dake sadar da computer da na’urori wadanda suka hada da.
USB Port: wuraren da ake sanya USB dukkansu suna aiki?
VGA/HDMI Port: akwai bukatar suma ka gwada ka tabbatar da ingancinsu, domin idan ka tashi yin amfani da Projector.
Charge Port: ka tabbatar da ingancin wuri caji shin idan an jona caja yana hawa?
Sound Port: ka tabbatar da wurin da ake sanya Headphobe yana aiki, yadda zaka iya hada computer dinka da External Speaker Kenan.
Microphone: ka tabbatar wurin da ake saka Microphone yana aiki, misali ga dan jarida zai bukaci daukar sauti da computer dinsa, don haka wannan bangaren yana da muhimmanci a wurinsa don ya samu damar amfani da ayyukansa.
CD ROM: Akwai bukatar ku tabbatar da wurin saka plate din CD yana aiki.
Speaker: akwai bukatar ka tabbatar kayi Playing wani file don ka tabbatar da sautin computer dinka cewa yanayi ko bayayi, misali na sayi computer domin na dinga yin kallo, to kunga speaker tana da matukar muhimmanci a gurinsa.
Camera: Akwai bukatar duba ingancin Camera din wayarka musamman idan kana bukatar ka dinga daukar hoto, ko recording da ita.
Screen Size: akwai bukatar duba girman Screen din, misali idan ina son Computer domin yin Video Editing to ina bukatar mai girman screen domin mai karamin screen ba kowacce software ta Video editing zata dauka ba.
Softwares: wannan musamman ga masu siyan computer da ba sabuwa ba, akwai bukatar su tabbatar akwai manhajojin da suke bukata aciki, maimakon sai sun siya kuma suzo suna yawon neman softwares, ana kara wankar kudinsu, musamman nasu Anti Virus da sauransu.
Facebook Comments