how to create online payment link in Hausa

[Online Business] Yadda zaka tsara karbar kudi ta internet

[Online Business] Yadda zaka tsara karbar kudi ta internet

Da yawan masu talla ko sayar da kayayyaki ta internet musamman masu tasowa kan gaza wajen samar da kyakykyawan tsarin karbar kudi ta internet, misali idan ka tashi karbar kudi maimakon ka bayar da account number dinka ayi maka transfer, sai ka bada link wanda mutum zai shiga yayi amfani da katin ATM dinsa ya biyaka kudinka.

 

Yin hakan shine kyaky-kyawar hanya mai inganci da ake bi, to akwai hanyoyi da dama da ake irin wannan tsarin daga ciki akwai:

  1. PayStack: ana amfani dashi wajen tsare karbar kudi, zakayi register dasu, zasu baka damar kirkirar karbar kudi kala-kala misali ina sayar da jaka zan iya fitar da link dinta mutum zai ga hotonta da farashinta kuma idan ya shiga zai biyani kudina, sannan ya shigarmin da bayanansa, wato zaka iya neman bayanan mutane kamar lambar waya, adireshi da sauran duk bayanan da kakeso.
  2. Remita SME: kamar yadda na san REMITA ba boyayye bane a wurinku, to ba don iya biyan kudi ga gwamnati ki makarantu aka yishi ba, suma suna da sashen dake irin wannan tsarin da zaka nemi a biyaka kudi.

Akwai wadansu shafukan da dama da suke irin wannan aikin zan kawo karin wasu kadan daga ciki a kasa

  1. VOGUE PAY
  2. LANDEDU
  3. TRUE BILL
  4. LYNKS
  5. METER FEEDER
  6. LANDED
  7. MY PAGA

Note: Dukkan kamfanunuwan dake wannan tsari akwai abinda suke cirar matsayin ladan aikinsu.

RUBUTUKA MASU ALAKA:

[Online Business] Ma’anar Kasuwancin Yanar Gizo –Arewa Radio 93.1 FM

[Online Business] Menene Kasuwancin eBook Marketing?

[Online Business] Abubuwa 6 Ga Wanda Zai Fara Kasuwanci Ta Social Media A 2019

[Online Business] Hanyoyi Ashirin (20) Da Zaka Bunkasa Kasuwancinka Ta Instagram

Basheer Sharfadi

Social Media Strategists.

10-06-2019.

Facebook Comments
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *