Blogging How to find Key Word in Hausa

[Blogging] Yadda zaka binciko Keyword domin SEO dinka

[Blogging] Yadda zaka binciko Keyword domin SEO dinka

 

Kamar yadda nasha fada a baya cewa babbar matsalar Bloggers din Arewa itace SEO to a yau zanyi bayanin yadda zaka binciki KeyWord domin sanyawa a shafinka.

YANA DA KYAU KA KARANTA WANNAN: [Blogging] Hanyoyi 6 da zaka sanya mutane su dinga shiga Blog dinka

Menene Key Word?

Sune kalmomin da jama’a ke yawan bincika a internet, misali “Yadda ake yin kaza ko yaya ake yin kaza” to kowane post zakayi akwai irin Keyword din da yake bukata dai-dai da abinda post din ya kunsa.

 

Menene Amfanin Saka Key Word a Blog?

Amfani da Key Word a Blog zai baiwa mutane damar samun shafinka cikin sauki, sannan shafinka zai kara gudu a google ta hanyar masu bincike, domin kuwa zai saukakawa google sauki wajen da anyi bincike ya dinga bada shafinka a sama.

 

Yadda Zaka Nemo Key Word na Posting Dinka:

Misali yanzu nayi rubutu akan kaza to sai ka duba google kayi searching makamancin wannan abin da ka rubuta zai baka wasu tambayoyi makamantansa a kasa, kamar yadda kuke gani a kasa.

Blogging How to find Key Word in Hausa

To duka wadannan nau’ika ne, na Key Word da zaka iya dauka ka sanya su a post dinka, wato wuraren da ake sanya tag, kamar yadda nayi bayaninsu a post din da ya gabata.

 

Sannan kai da kanka zaka iya tsara tambayoyi akan post dinka ka saka wanda kake ganin mutane zasu iya bincikarsu ta internet.

RUBUTUKA MASU ALAKA:

[Blogging] Hanyoyi 6 da zaka sanya mutane su dinga shiga Blog dinka

[Yau da kullum] Hanyoyi 8 da dalibi zai iya neman kudi daga makaranta

[Blogging] Hanyoyi Hudu (4) da Zaka Samu Traffic a Shafinka ta Social Media a 2019

[Blogging] Yadda Ake Saka Link A Post

Basheer Sharfadi

Social Media Strategsits.

10-06-2019.

Facebook Comments
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *