How to increase your blog traffic in Hausa

[Blogging] Hanyoyi 6 da zaka sanya mutane su dinga shiga Blog dinka

[Blogging] Hanyoyi 6 da zaka sanya mutane su dinga shiga Blog dinka

A yau zanyi magana akan wasu hanyoyi guda 6 da zaka sanya mutane su dinga shiga blog dinka a koda yaushe.

  1. Ka dinga wallafa bayanan masu amfani da shafinka, idan akayi maka comment na yabawa to kayi kokarin wallafashi domin wanda yayi zaiji dadi, sannan suma masu bibiyarka zasu kara samun gamsuwa da kai, sannan ka basu damar bayyana ra’ayoyinsu a comment.
  2. Ka dinga yin reply ga masu aikowa da shafinka sakonni ta comment ko inbox.
  3. Ka dinga yin sharing tsoffin postin misali yau nayi magana akan Yadda ake satar account din facebook to akwai bukatar lokaci zuwa lokaci ka kara dawo dashi domin ka samu sabbin abokai an samu karin wanda basu karantashi ba a baya, wannan ga irin namu Bloggers din kenan ba masu Blog din Labarai ba.
  4. Ka dinga shirya zabe ko kacici-kacici/tambaya idan anci kayi yabo ko ka saka kyauta, wannan zai kara jawo maka hadin kan jama’a sosai, misali kwanaki shafinmu na Jaridar Tsanya ya sanya gasar cewa duk wanda ya fadi inda aka dauki wasu hotuna da ya wallafa za’a bashi 1,500 haka aka samu wata daliba ta amsa kuma aka bata kyautar, hakan ya janyowa shafin tarin jama’a sosai.
  5. Kada ka dinga wallafa rigingimu a shafunka, musamman rigingimun addini ko na kabilanci da makamantansu ka maida hankali kan iya abinda shafinka ya sanya gabam ka guji wallafa koda ra’ayinka na siyasa, misali a shafin com na internet da su Facebook bamu taba wallafa wani ra’ayinmu akai ba idan zamuyi wannan sai muyi amfani da personal account dinmu, haka akeso.
  6. Ka baiwa masu ziyarar shafinka damar suyi subscribing ta email ta yadda kana wallafa abu zasu gani a email dinsu, sannan ka gayyacesu zuwa sauran shafukanka na social media.

Allah ya taimaka.

 RUBUTUKA MASU ALAKA:

[Blogging] Abubuwa 10 da zaka bunkasa SEO a Blog dinka

[Blogging] Manyan Hanyoyi Uku (3) da Zaka Samu Kudi da Blog Dinka

[Blogging] Hanyoyi Hudu (4) da Zaka Samu Traffic a Shafinka ta Social Media a 2019

[Blogging] Yadda Ake Saka Link A Post

Basheer Sharfadi

Social Media Strategists.

01-06-2019.

Facebook Comments
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *