How to make fake audio in Hausa

[Fasaha] Yadda ake hada murya (audio) na karya

[Fasaha] Yadda ake hada murya (audio) na karya

 

MUN FASA ƘWAI

Tambihi
A shekarar 2015, wani hamshakin dan siyasa a jihar Katsina ya bayar da sanarwar cewar ya saka kyautar naira miliyan 5 ga duk wanda ya kawo masa shaidar cewar ya yi sanarwa a kafafen yada labarai cewar yana goyon bayan wani dan takara a jihar.

An samu cewa ana ta saka muryarsa a gidajen rediyo yana fadin ya bar jam’iyyar sa kuma yana kiran magoya bayansa su fito su zabi abokin hamayyar sa.

Daga bisani, bayan an zurfafa bincike, aka gano cewar hadin gambizar muryarsa aka yi domin cimma manufa.

 

Yadda Ake hada Sauti Iri Daban-daban

Ana iya haɗa sautin murya ba tare da wahala ba matukar akwai kayan aikin. Dabarar da aka sani tun tuni ana kiran ta ‘voice synthesizer’. Abubuwa biyu ake yi a wannan tsarin da ake kira ‘Pitching’ da ‘Morphing’.

Pitching shi ne duba yanayin hawa da saukar murya da yadda mutum ke furta wasu haruffa ko kalmomi. Da amfani da pitching ne kayayyakin sauti kamar fiyano ko kalangu ake iya kaɗa su a ji kamar suna faɗin wasu kalmomi.

Morphing ya danganci dabarar da ake yi wajen canja kalmomin zuwa irin yadda ake so. Ta haka ne ake fitar da murya daga ta tsoho zuwa ta yaro, ko ta mace ko ta aljani da sauransu.

Irin wadannan dabaru da su ake amfani wajen saka kwamfuta ko waya suna furta kalaman rubutu watau ‘Text to Speech’.

Da aka zurfafa sai kuma aka zo da wata dabara wajen kwaikwayon muryar mutum har a ji yana ambata wasu kalamai da ba shi ya yi su ba.

Wadannan sautukan na kasa duk mutum daya ne ya furta su, watau ni, amma sun fitar da muryoyin mutane daban-daban har da na mata.

Ana amfani da manhajoji da dama. Daga cikinsu akwai:
1. Adobe Voco
2. Wavenet
3. Morphovx
4. Lyrebird
5. Voice Clone
6. VoiceMod
7. Celeb Voice Cloner

Na kawo su ne ba tare da bayani ba, gudun canja manufa.

Don haka. Da zarar ka ji muryar wani ko wata an nado, matukar ba daga ingantacciyar madogara ba ce. Kar ka yi saurin yanke hukunci har sai ka tabbatar da cewa ba harhadawa aka yi ba.

Yadda ake gano Muryar Hadi…. Shi ne rubutu na gaba.

RUBUTUKA MASU ALAKA:

[Fasaha] Yadda ake gane screenshot na karya

[Fasaha] Yadda ake hada Screenshot na karya

[Facebook] Yadda zaka saka alamar “Follow” a Facebook dinka maimakon “Add Friend”

[WhatsApp] Hanyoyi Bakwai (7) Da Zaka Tantance Ingancin Sako a WhatsApp

Danladi Haruna
20 ga Ramadan 1440
25 ga Mayu, 2019

Facebook Comments
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *