Connect with us

Blogging

[Blogging] Abubuwa 10 da zaka bunkasa SEO a Blog dinka

Published

on

how to boost your seo ranking in hausa

[Blogging] Abubuwa 10 da zaka bunkasa SEO a Blog dinka

 

Da yawan Bloggers dinmu na AREWA suna jin jiki saboda matsalar SEO wasu saboda rashin sani, wasu kuma saboda rashin bin doka da ka’ida, tabbas SEO yana daga cikin manyan matsalolin da AREWA Bloggers ke fuskanta, domin duk site din da SEO dinsa baya motsawa to tabbas sunansa gawa, domin samun Traffic ta Google shine mafi albarka da alkhairi fiye da samu ta Facebook dasu WhatsApp.

 

A yau nayi nazari kan wasu hanyoyi guda goma (10) Blogger zaibi domin bunkasa SEO a Blog dinsa.

 

 1. Kayi amfani da kalmomin da mutane ke bincika (keyword search) misali mutane suna yawan shiga internet su rubuta yadda ake abu kaza, to idan kazo yin post sai kayi amfani da yadda ake abu kaza, to da zarar mutane sun binciki wannan abun zai hanzarta kawo musu site dinka.
 2. Ka saka keyword sama da guda daya a wurin tagging, misali nayi rubutu akan Yadda ake bude email to a wurin tag zan iya saka Yadda zaka bude email, Yaya zan bude email, ina son bude email, yadda duk wanda akayi searching zai wurga masa amsarka, a kowane post akwai wurin taggin.
 3. Ka saka take rubutu mai jan hankali, yana da kyau ka kula da kyau wajen saka taken da zai ja hankali misali zanyi rubutu akan blogging sai na saka Ma’anar Blogging da Abinda ya kunsa ko kuma Yaya ake yin abu kaza da sauran Title wanda kana ganin mutum zai iya bincikar wannan taken.
 4. Ka dinga saka BackLink a duk sanda kayi magana akan wani abu to kayi mention dinsa, kamar yadda kuke gani a wannan shafin duk sanda wani bayani ya biyo ta kan wani ko wata gaba da mun riga munyi bayani akanta to mukan yi mentioned dinta ta yadda zaku ga gun yayi highlighting kawai dannawa zakuyi, hakan yana taimakawa SEO sosai da sosai.

Karanta wannan: [Blogging] Yadda Ake Saka Link A Post

 1. Sanya hoto a posting yana da kyau idan zakayi posting kayi amfani da hoto kuma ka sanyawa hoton sunan post din da kayi misali nayi posting akan yadda ake samun kudi da facebook to sai na sakawa hoton suna how to make money with facebook.
 2. Ka sanya ALT Text a hoton da ka saka, idan kazo dauko hoto akwai wurin Alt Text ana bukatar nan ma ka saka bayanin abinda hoton ya kunsa sau tari shima muna saka abinda mukasa a tag a wajen hakan zai sanya da anyi searching a internet ya bayar da hoton.
 3. Ka sanya Image Description idan kazo dauko hoto akwai wurin Description da zaka rubuta takaitaccen bayani akan abinda hoton ya kunsa, shima wannan yana matukar taimakawa SEO dinka.
 4. Ka saukaka bayaninka, kada kazo kayi bayani mai tsauri ko wanda ba zai gamsar da al’umma ba domin hakan ka iya hana al’umma shiga shafinka, kaga kai kuma ba haka kakeso ba.
 5. Ka tabbatar ka zabi Category a posting dinka misali kayi posting akan Facebook ko labarai to ya zama kana da folder ta facebook ko labarai da zaka sanya wannan post din.
 6. Ka dinga saka Related Post kada ka damu da wanda site dinka ke sakawa Automatically a’a ka sanyashi da kanka wani a tsakiya wani a kasa kamar misali a wannan post din kunga a sama mun baku wani link related da mukace Karanta wannan sannan a kasa zamu kara baku Rubutuka Masu Alaka: ku dinga yin wannan domin site zai iya kawo post din da basu sukafi can-canta suzo a related ba.

 RUBUTUKA MASU ALAKA:

[Blogging] Ma’anar Blogging da Abubuwan da Ya Kunsa

[Blogging] Abubuwa Bakwai (7) Da Yakamata Ka Sani Kafin Fara Blogging

[Blogging] Abubuwa 6 da Blogger zai kiyaye a yayin rubutunsa

[Blogging] Hanyoyi Hudu (4) da Zaka Samu Traffic a Shafinka ta Social Media a 2019

[Blogging] Manyan Hanyoyi Uku (3) da Zaka Samu Kudi da Blog Dinka

Allah ya taimaka amin.

Basheer Sharfadi

Social Media Strategists.

31-05-2019.

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Saurari Shirin Daga Shafukan Sadarwa

Shirin dake tattauna batutuwan da suka shafi shafukan internet da kuma rahotonni daga makarantunmu.

31-10-2019

14-09-2019

07-09-2019

31-08-2019

24-08-2019

10-08-2019

03-08-2019

26-07-2019

For Registering Domain Names, I trust DomainKing.NG

Subscribe To Our Youtube Channel

Subscribe To Khalyperh The Voice Channel

Subscribe To AU Studio On Youtube

Litattafai Cikin PDF

 1. Takardar Sanin Makama Ga Daliban Da Zasu Zana Jamb 2018 Download Now
 2. Mu Koyi Computer A Saukake Download Now
 3. Duniyar Facebook A Yau Download Now
 4. Yadda zaka fara neman kudi Online ta NNU Download Now
May 2019
M T W T F S S
 12345
6789101112
13141516171819
20212223242526
2728293031  

ADS

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG
error: Content is protected !!