How Detect fake images on internet in Hausa

[Fasaha] Yadda ake gane screenshot na karya

[Fasaha] Yadda ake gane screenshot na karya

 

MUNA FASA KWAI

YADDA AKE GANE SCREENSHOT NA KARYA

Hanyoyi da dama ake amfani da su domin haka, saboda ba abu ne mai sauki wajen gano ainihin hoto a intanet ba. Shi ya sa ma dai yanzu hotuna sun zama tamkar ababen nune ba na hujja ba.

 

Duk lokacin da aka saka hoto a intanet musamman facebook, yana daukar kwafi ne ya ajiye a matsayin na al’umma gwargwadon tsarin da mai posting ya yi. Watau kamar dai ka je neman aiki ka bayar da kwafin takardunka na ainihin kuma suna hannunka. Don haka nan yake da wuya a gane salsalar hoto daga facebook kadai.

Amfanin wannan shi ne, zai yi wuya a san asalin hoton ko screenshot din sai dai a dogara ga abin da mai hoton ya fada. Illarsa kuma, hoton ya zama na al’umma hatta mai hoton ma ba zai iya da’awar nasa ba ne. Kenan za a iya murguda shi yadda aka ga dama.

 

To amma hoton da aka sa a sauran kafafen intanet mafi yawa ana samu google na alkinta bayanan hotuna daga ranar da aka sanya shi a intanet din. Irin wadannan hotunan ne ake gano asalinsu da lokacin da suka hau intanet. Masu irin wadannan hotunan na rike hakkin mallakar su ko da za a kwafa ba tare da izninsu ba. Gidan Wikipedia ba sa karbar hotunan masu hakkin mallaka musamman wadanda suka samo asali daga facebook. Wannan kenan.

 

Yadda ake gano asalin hotuna kuwa, ‘yan dabaru ne da suka hada da:

 1. Amfani da kaifin hankali da tunani: Wasu hotunan kana gani za ka iya fahimtar hadafinsu da inda suka karkata. Akwai bukatar nazari kan wanda yake yada hoton da irin bayanan da hoton ke dauke da shi. Idan screenshot ne misali, ana duba irin lafuzan da ke makale a rubutun da sauransu.

 

 1. Ana duba hoto ta fuskar da ake kira ‘reverse Image search’. Kamfanin google da Bing da Yandex suna bayar da damar bincikar asalin hoto a manhajojinsu.

 

 1. Amfani da fasahar ‘exif’; Exif na nufin ‘Exchangeable image file’. Wasu dunkulallun bayanai ne dangane da hoto wanda ke nuna ranar da aka dauke shi da irin kyamarar da aka yi amfani da ita da karfinta. Da waje da kuma irin tsaiwar ko saitin kyamarar. Kwararru a wannan fannin suna duba bayanan domin fito da wasu abubuwa.

 

Ana iya amfani da exif ta intanet ko ta wasu manhajoji a android da apple da kuma kwamfuta. Sai dai sau tari bayanan da ake samu a hotunan facebook ba a iya samun cikakken bayanansu a exif, kasancewar suna jirkita su domin ya dace da manufarsu ta adana bayanai.

 

 1. Tuntubar wanda ya yada hoton ya aiko da shi ta email: Ana iya samun bayanai daga hoton asali kasancewar kamanninsa ba su jirkita ba. Ta nan za a gane yadda aka hada shi idan an duba exif dinsa.

 

 1. Duba rariyar likau ko turakar rubutun da aka ce an dauko hoton. Ana iya ziyarar gidan wanda aka ce ya yi rubutun da aka dauko hotonsa domin a tantance. Idan ya kasance misali ana tantamar ko ya goge rubutun ne, akwai kafafen intanet da suke kwafar rubuce-rubuce suna adanawa koda kuwa an goge su ana iya samun burbushin su. Watau abin da ake kira ‘meta data’.

 

Akwai gidaje kamar ‘Facebook Trend’ da ‘Way Back Machine’ da Social Archive’ da sauransu. Abu mafi sauki sai kurum a kwafi wasu kalmomi na rubutun a rubuta a google bayan an sa su cikin alamun baka watau ” “. Za a iya gano burbushin rubutun. Wasu kamfanonin ma, suna iya karbar kwangilar bincike idan an biya su.

 

 1. Akwai wasu gidajen website da ke iya bincika hoto tare da exif dinsa. Gidajen sun hada da:
  1. https://www.tineye.com/search
  2. https://exif-viewer.com
  3. http://exif.regex.info/exif.cgi
  4. https://www.prepostseo.com/reverse-image-search
  5. http://imageedited.com/
  6. https://www.imageforensic.org/

 

 1. Adobe Photoshop da Corel Draw da sauransu. Wasu manhajoji ne na kwamfuta da ake gina hoto ko wargaje shi a sake masa fasali da kuma duba inda asalin hoton yake. Aiki da su na bukatar nutsuwa da daukar lokaci ana nazari. Ana dudduba wasu tubalan ginin hoton ne da ake kira pixel.

Nan gaba za mu da yadda ake hada murya ta karya

RUBUTUKA MASU ALAKA:

[Fasaha] Yadda ake hada Screenshot na karya

[Facebook] Yadda zaka saka alamar “Follow” a Facebook dinka maimakon “Add Friend”

[WhatsApp] Hanyoyi Bakwai (7) Da Zaka Tantance Ingancin Sako a WhatsApp

[WhatsApp] Abubuwa (16) da GB WhatsApp ya tsere asalin WhatsApp dasu

Danladi Haruna
18 Ramadan 1440
23 ga Mayu 2019

Facebook Comments
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *