How to detect fake screenshot in Hausa

[Fasaha] Yadda ake hada Screenshot na karya

[Fasaha] Yadda ake hada Screenshot na karya

FASA KWAI – 1

YADDA AKE ƘIRƘIRAR SCREENSHOT NA JABU

Na san wannan fasahar tun a 2014, amma ban taɓa amfani da ita ba don na san hadafin masu shirya abin da suke kira ‘frank’. Ana iya tsara duk wani post ko comment ko like ko reply gwargwadon yadda ake bukata.

How to detect fake screenshot in Hausa How to detect fake screenshot in Hausa

How to detect fake screenshot in Hausa

Idan kuka duba wadancan screenshots din gaba daya na jabu ne da na hada. Daga ido babu ta yadda za a bambance shi da na gasken. Anan gaba sannu a hankali zan kawo yadda ake bambace aya da tsakuwa.
Kafin mu je ga sirrin yadda ake gano hotunan jabu, bari na fadi yadda ake kirkirar su.
Hanyoyin iri biyu ne; akwai na website akwai na application. Dukkansu manufarsu kurum samun ‘traffic’ su rika jefa maka talla suna samun kudi da kai. Mu kuwa muna yi domin kagantawa abokan huldar mu.

Wasu daga website din da ake kera jabun screenshot sun hada da:

 1. tweetgen.com
 2. prankmenot.com
 3. zeobb.com
 4. generatestatus.com
 5. simitator.com
 6. smore.com
 7. https://igenerator.eu
 8. https://galau.me
 9. https://postcreator.com
 10. sharelinkgenerator.com

WADANDA KE CIKIN APPLICATION KUMA

 1. Fake Tweets
 2. Status Maker
 3. Whataspp Prank
 4. Facebook Imitator
 5. Yazzy
 6. Fake Chat
 7. Prank chat da sauransu

Zan so ‘yan sabuwar kungiyar mu ta yaki da jabun labarai su shiga akalla biyu daga wadannan kafafe da manhajoji su jarraba kirkirar screenshot na jabu.

A rubutu na gaba za mu zo da yadda ake gane jabun.

RUBUTUKA MASU ALAKA:

[Facebook] Hanyoyi (11) da Zaka Tsayar da Samun Labaran Karya a Facebook

[WhatsApp] Hanyoyi Bakwai (7) Da Zaka Tantance Ingancin Sako a WhatsApp

Yadda Zaka Tantance Sannan Ka Karbi Katin Zabenka (Kowa Da Kowa)

[Social Media] Yada Labaran Karya -Arewa Radio 93.1 FM Kano

Danladi Haruna
17 ga Ramadan 1440
22 ga Mayu 2019

Facebook Comments
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *