Connect with us

Google

[Google] Abinda yasa Google ya yanke hurda da kamfanin Huawei

Published

on

Goog;e and Huawei 2019 Crisis in Hausa

[Dambarwa] Abinda ya faru tsakanin kamfanin Google da Huawei

 

Munnir Abdulhamid
(Fasaha/Waya).

Amakon nan labaru sun mamaye kafafen sada zumunta na cewa kamfanin google ta dakatar da alakar kasuwan ci dake tsakanin ta da Huawei,mun bi diddiga labarin domin kawo muku hakikanin abubda ke faruwa.

Google kamfani ne dake kasar Amurka, suke da mallakin manhajar nan ta Android kuma suke da Application irin su Gmail, Youtube, Google Map, da kuma rumbun nan Na Play Store inda anan ne ake dauko halastattun Android Application.

Huawei Kamfani ne dake kasar China Suna kera naura masu tarin yawa manya daga ciki akwai Wayoyi (Mobile Phone), Computer,da Kuma Abubuwan da suka shafi Networking. Mafi yawancin Wifi Routers da ake aiki dasu da kuma Moderm na kamfanin ne.

15 ga watan nan (May) Gomnatin Amurka ta fidda dokan haramta kasuwan ci tsakanin kasar na Amurka da kuma kamfanin Huawei bisa zargin akwai wasu na’urar da kamfanin ke aiki dasu domin tattara bayanan sirri a cikin na’urar da suke sayar wa, hakan yasa kasar Amurka tayi dokar tsaida dukkan wani alakar kasuwan ci tsakanin kasar da kuma kamfanin na Huawei.

Kaman yanda mukayi bayani a baya cewa kamfanin Google na kasar Amurka ne, hakan yasa suka fito suma a ranar 19 ga watan na May suka sanar da tsaida alakar kasuwan cin da ke tsakanin su da kamfanin na Huawei.

Tirkashi wannan Sanar wa yana nuna cewa wayoyin Android na kamfanin Huawei ba zasu sake samun dukkan wani sabon Update ba daga kamfanin na Google kuma dukkan Wani sabon waya da Huawei zasu kera toh fa badai a saka mata Android ba sai dai wani manhajar kuma ta daban. sai dai kuma kamfanin na Google sun dagawa Huawei kafa na kwana chasa’in ma’ana zasu cigaba da samun Update daga nan har Zuwa kwana chasa’in (wata uku daga yanzu).

Masu fashin bakin akan abubuwan da suka shafi kimiyya da fasaha sun yita korafi inda suka nuna wannan mataki da Amurka ta dauka a matsayin abunda bai kamata ba wanda zai iya haddasa Asara sosai da kuma ci baya a kasuwar waya a duniya baki daya har ma da kasuwan Computer kasantuwar bayan Google akwai kamfani irin su Microsoft da kuma Intel invidea wanda dukkan su suna kasar na Amurka.

Ta bangaren kamfanin Huawei basu nuna damuwar su ba a Sanarwa ta farko da suka fitar sun nuna cewa suna daya daga cikin manyan abokan kasuwancin google kuma zasu cigaba da kasancewa a hakan, matakin kuma da google ya dauka a kansu sunce zasu cigaba da zura ido suga mai zai biyo baya, Sun kuma sanar da masu aiki da wayoyin su cewa suna da shiri na musamman da zasu gabatar da manhajar su ta musamman wanda zasu maye gurbin Google Play Store dashi.

#TechHausa #Hausa #Tech #Google #Android#Huawei

RUBUTUKA MASU ALAKA:

[Google] Zamu fara sanya talla a babban shafinmu –Google

[Google] Google, Facebook da Tarihin Sharfadi.com -Arewa Radio Kano 93.1

[Google] Ma’anar Google da Abubuwan da Ya Kunsa -Express Radio Kano

[Google] Yadda Google Ke Samun Kudin Shiga

Facebook Comments
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ku Saurari Fasaha Radio Kai Tsaye

Note: Fasaha Radio tana aiki tsawon awanni 24 domin wayar da kan al'umma akan yadda ake amfani da fasahar zamani.

Saurari Shirin Daga Shafukan Sadarwa

Shirin dake tattauna batutuwan da suka shafi shafukan internet da kuma rahotonni daga makarantunmu.

31-10-2019

14-09-2019

07-09-2019

31-08-2019

24-08-2019

10-08-2019

03-08-2019

26-07-2019

For Registering Domain Names, I trust DomainKing.NG

Subscribe To Our Youtube Channel

Subscribe To Khalyperh The Voice Channel

Subscribe To AU Studio On Youtube

Litattafai Cikin PDF

  1. Takardar Sanin Makama Ga Daliban Da Zasu Zana Jamb 2018 Download Now
  2. Mu Koyi Computer A Saukake Download Now
  3. Duniyar Facebook A Yau Download Now
  4. Yadda zaka fara neman kudi Online ta NNU Download Now
May 2019
M T W T F S S
« Apr   Jun »
 12345
6789101112
13141516171819
20212223242526
2728293031  

ADS

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG
error: Content is protected !!