Connect with us

WhatsApp

[WhatsApp] Shin ko GB WhatsApp yana da kariya? Me yasa ba’a samunsa a Play Store?

Published

on

its gb whatsapp safe or not in Hausa

[WhatsApp] Shin ko GB WhatsApp yana da kariya? Me yasa ba’a samunsa a Play Store?

 

GB WhatsApp ko WhatsApp GB manhajar WhatsApp ce ta asali da wasu (ba kamfanin WhatsApp dinba) suka sabinta ta, tare da yi mata sabbin kare-kare ta hanyar kara baiwa masu amfani da manhajar karin damarmaki.

 

WhatsApp na asali da kuma GB WhatsApp duka suna aiki da server guda tamkar Facebook ne ka shiga ta asalin application dinsu ko kuma ta facebook lite, sai dai shi Gb ba mallakar masu asalin WhatsApp din bane wato kamfanin Facebook.

 

A karon farko GB WhatsApp bai saba da doka da kuma ka’idar kamfanin WhatsApp ba, amma daga baya ya yiwa kamfanin karantsaye saboda damar da ya baiwa masu amfani dashi tayi yawa sannan bayanan masu amfani dashi bashi da tsaro.

 

Babu tsaro a GB WhatsApp!

Maganar gaskiya babu kariya a Gb WhatsApp su kansu kamfanin facebook dake mallakar asalin WhatsApp din har yanzu da akwai kasha a gindinsu na sun gaza tsare bayanan masu amfani dashi balantana kuma wanda wasu suka kwafi nasu.

 

Masu amfani dashi na cikin hatsarin a satar musu bayanai, shine mutum zai dinga samun sakonni da kiran waya na babu gaira babu dalili.

 

Me yasa babu GB WhatsApp a Play Store?

 

Play Store sunki karbar manhajar GB WhatsApp saboda suna ganin anyi satar fasahar wasu ne, don yayi kama sosai da asalin WhatsApp wannan dalilin yasa ba zaka iya samunsa a Play Store dinba.

A dokar Google dai baya saka duk wata manhaja mai irin wannan matsalar ko kuma wanda zata iya kawo rigima ko me yada karerayi da sauran laifuka.

 

Ire-iren GB WhatsApp

GB WhatsApp yana nan iri-iri daban-daban sama da guda daya, kowa yana kokarin shima yayi nasa, don haka ba kala daya bane.

 

Shawarata gama da GB WhatsApp

Idan kana amfani da WhatsApp ne don gaisawa dan sada zumunci kadai to babu laifi zaka iya amfani dashi.

 

Idan kuma kana da sabgogi kamar kana kasuwanci kana karbar bayanai masu muhimmanci, ko kai dan jarida ne kana karbar rahotonni ta hanyarsa to kada kayi amfani da GB WhatsApp.

 

Wane mataki kamfanin suka dauka kan GB WhatsApp?

A yanzu haka masu amfani da GB WhatsApp na cikin hatsarin rasa account dinsu, domin kuwa WhatsApp suna bi suna rufe layukan dake amfani da GB din.

 

Karanta cikakken bayani anan:

RUBUTUKA MASU ALAKA:

[WhatsApp] Dalilan da Yasa WhatsApp Ke Dakatar da Mutum daga WhatsApp

[WhatsApp] Yadda Zaka Dawo da Lambar da Aka Dakatar Daga Yin WhatsApp

[WhatsApp] Hanyoyi Bakwai (7) Da Zaka Tantance Ingancin Sako a WhatsApp

[Facebook] Abubuwan da Facebook F8 yazo dasu a Messenger da WhatsApp

Basheer Sharfadi

Social Media Strategists.

21-05-2019.

Facebook Comments
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ku Saurari Fasaha Radio Kai Tsaye

Saurari Shirin Daga Shafukan Sadarwa

Shirin dake tattauna batutuwan da suka shafi shafukan internet da kuma rahotonni daga makarantunmu.

14-09-2019

07-09-2019

31-08-2019

24-08-2019

10-08-2019

03-08-2019

26-07-2019

For Registering Domain Names, I trust DomainKing.NG

Subscribe To Our Youtube Channel

Subscribe To Khalyperh The Voice Channel

Subscribe To AU Studio On Youtube

Litattafai Cikin PDF

  1. Takardar Sanin Makama Ga Daliban Da Zasu Zana Jamb 2018 Download Now
  2. Mu Koyi Computer A Saukake Download Now
  3. Duniyar Facebook A Yau Download Now
  4. Yadda zaka fara neman kudi Online ta NNU Download Now
May 2019
M T W T F S S
« Apr   Jun »
 12345
6789101112
13141516171819
20212223242526
2728293031  

ADS

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG
error: Content is protected !!