[Social Media] Masu yawan amfani da social media na cikin hadarin kamuwa da ciwon hauka -Binciken Masana

Mania Kanwar Hauka Na Saurin Kama Mutane Masu Saurin Bude Shafukan Sada Zumunta ~ Likita Ajiboye.

Kwararren Likita Daga Asibitin Koyarwa Na AdoEkiti Mai Suna Ajiboye Yace Wannan Cuta Tana Kama Masu Nacin Bude Shafukan Sada Zumunta Wadanda Ana Idar Da Sallah Ko Kwanciyar Bacci Ko Duk Inda Suke Babu Abinda Suke Budewa Sai Facebook, WhatsApp Da Sauransu. Wannan Cuta Kama Sassan Kwakwalwar Dan Adam Kuma Ita Kwakwalwa Ba Kowanne Sako Take Karba Ba.

Kwararre Akan Fannin Social Media Basheer Sharfadi Yace “Baya Iya Awa Guda Ba Tare Da Ya Bude Wadannan Zaurukan Sada Zumunta Ba, Amma Wannan Cuta Za’a Iya Samunta Domin Akwai Hotunan Da Wasu Ke Dorawa Kaga An Fasa Kwakwalwar Mutum, Ko Hoto Mai Jini Dole Hankali Ya Tashi Wani Zai Iya Samun Tabin Hankali.

Ya Kara Da Cewa “Ni Yanzu In Naga Wannan To Na Sallami Shafin Bazan Kara Shiga In Kalli Wannan Abin Na Tada Hankali Ba, Idan Naga Kana Dora Abubuwan Da Basu Dace Ba Wanda Zai Daga Min Hankali Ko Hatsari Wanda Zai Tunzura Kwakwalwata Zan Guje Masa Babu Yadda Za’ai Naga Abin Domin Kare Kaina Daga Samun Matsala.”

To Allah Ya Kiyaye Ya Kara Mana Lafiya Da Ingantaccen Hankali.

Saurari Rahoton Freedom Radio Kano Akan Wannan Batu:

Download Now

Ayi sauraro lafiya.

RUBUTUKA MASU ALAKA:

[Social Media] Abubuwan dake Jawo Yin Batanci a Social Media –Guarantee Radio Kano

[Social Media] Yada Labaran Karya -Arewa Radio 93.1 FM Kano

[Blogging] Hanyoyi Hudu (4) da Zaka Samu Traffic a Shafinka ta Social Media a 2019

[Radio Program] Social Media da Kasuwancin Internet -Arewa Radio 93.1 Kano -Sharfadi

[Shiga Ka Karanta] Yadda ‘Yan Social Media Zasu Aikawa da Hukumar INEC Sakon Halin da ake ciki a yankunansu kai tsaye ta wayarsu.

Facebook Comments
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *