Connect with us

Instagram

[Instagram] Abubuwan da Facebook F8 yazo dasu a Instagram

Published

on

Facebook F8 Tools for Instagram

[Instagram] Abubuwan da Facebook F8 yazo dasu a Instagram

A farkon watan mayun da muke cikine kamfanin Facebook ya gabatar da taron shekara-shekara na bana wanda aka yiwa lakabi da Facebook F8 a yayin taron dai an kaddamar da sabbin sauye-sauye a manhajojinsa, a yau zanyi magana akan wasu daga sauye-sauyen da kamfanin yazo dasu manhajar Instagram.

  1. Shop from Creators:

Sabon tsarine da zai baka damar siyan kayayyaki cikin sauki.

Duba hoton dake kasa:

A sabon tsarin kamar yadda kuke gani a hoton dake sama, maimakon kayi screenshot na wani kaya da ka gani, ko ka tambayi bayani akansa ta comment ko kayi DM kawai zaka danna ne ka samu cikakken bayani sannan ka siya nan take, ba tare da ka bar Instagram dinba.

  1. Damar neman taimako, ko kirkirar wayar da kai:

A wannan sabon tsarin zaka iya kirkirar story da mutum zaibi ta ciki yayi donating, kamar don kungiyoyi kenan dake neman tallafi ko kuma wani batu da kakeson wayar da kan al’umma.

Duba hoton dake kasa:

  1. Personal Connection:

Dai-dai yake da Close connections a facebook da nayi bayanin a posting din da yagabata, zai baka dama ka kayyade iya wadanda kakeso suga abinda ka wallafa, koda kuwa mutum yana cikin followers dinka, ba zai gani ba sai iya wanda ka amince dashi.

Kalli hoton dake kasa:

  1. Damar ganin wadanda sukayi liking din abu:

A yanzu ba iya adadin wadanda sukayi liking zaka dinga gani kawai ba, a’a zaka iya ganin shin su waye ma sukayi like din, kamar yadda ake iya ganin na Comment.

  1. Sabinta Camera:

Yanzu zaka iya yin Story ba tare da ka saka hoto ba kamar yadda kuke gani a hoton dake kasa.

Zan dakata anan sai a rubutu na gaba.

 RUBUTUKA MASU ALAKA:

[Facebook] Abubuwan da Facebook F8 yazo dasu a Messenger da WhatsApp

[Facebook] Anyi taron shekara-shekara kan Facebook F8 a Kano

[Internet] Wikipedia da Yadda ake Amfani Dashi?

 [Instagram] Zamu kwace followers din duk wanda yayi cheat –Instagram

Basheer Sharfadi

Social Media Strategists.

15-05-2019.

Facebook Comments
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ku Saurari Fasaha Radio Kai Tsaye

Note: Fasaha Radio tana aiki tsawon awanni 24 domin wayar da kan al'umma akan yadda ake amfani da fasahar zamani.

Saurari Shirin Daga Shafukan Sadarwa

Shirin dake tattauna batutuwan da suka shafi shafukan internet da kuma rahotonni daga makarantunmu.

31-10-2019

14-09-2019

07-09-2019

31-08-2019

24-08-2019

10-08-2019

03-08-2019

26-07-2019

For Registering Domain Names, I trust DomainKing.NG

Subscribe To Our Youtube Channel

Subscribe To Khalyperh The Voice Channel

Subscribe To AU Studio On Youtube

Litattafai Cikin PDF

  1. Takardar Sanin Makama Ga Daliban Da Zasu Zana Jamb 2018 Download Now
  2. Mu Koyi Computer A Saukake Download Now
  3. Duniyar Facebook A Yau Download Now
  4. Yadda zaka fara neman kudi Online ta NNU Download Now
May 2019
M T W T F S S
« Apr   Jun »
 12345
6789101112
13141516171819
20212223242526
2728293031  

ADS

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG
error: Content is protected !!