Connect with us

YouTube

[YouTube] Yadda Ake Dora Video a YouTube

Published

on

how to upload video on youtube

[YouTube] Yadda Ake Dora Video a YouTube

Menene Social Media?

 • Social Media Shafukane ko Manhajoji da zasu baiwa mutum damar tattaunawa da wani ta hanyar rubutaccen sako, hoto, hoto mai motsi (video) da kuma cikin sauti.

Mutane da dama kan tattauna batutuwa tare da musayar ra’ayi a wadannan shafuka.

Menene YouTube:

YouTube daya ne daga cikin shafukan sadarwa na yanar gizo mallakar kamfanin Google wanda ke baiwa mutum damar kallar video da kuma dora video a kai, ta yadda zai samu damar aikawa da mutane sakon video, YouTube shine shafi na biyu a duniya da al’umma suka fi ziyarta. adireshin YouTube shine www.youtube.com.

Yadda ake dora Video a YouTube:

Yadda ake dora video a YouTube shine a computer zaka ga alamar “Upload” da zarar ka shiga YouTube ko kuma kai tsaye kaje www.youtube.com/uplaod

A waya kuma akwai shima ta sa alamar ta uploading kamar yadda kuke gani a kasa

Kana shiga zai budo maka dukkan videos din dake kan wayarka sai ka zabi wanda kake son uploading, idan kuma live zakayi akwai alamar “Go” a wajen.

 

Abubuwan da Zaka Kula Dasu Wajen Yin Uploading

 1. Title
 2. Description
 3. Tag
 4. Featured Image
 5. Privacy
 • Title: a nan zaka saka taken (sunan) Videonka ana buka

Tar ka sanya take mai jan hankali sosai.

 • Description: a nan zaka tsara takaitaccen bayani akan abinda videonka ya kunsa. (amman a waya a nan ake saka tag).
 • Tag: shine ka sanya kalmomin da kake ganin za’a iya yin searching ko kake son suga videonka, akwai cikakken bayani ka nemi darasinmu na HashTag.
 • Featured Image: Shine hoton da kake so ka gani akan videon, misali zaka ga a YouTube ance “Ka San Abin Kunyar Da Maryam Yahaya Tayi? Ga hotonta kuma akai, amman kana shiga sai ka ga ba Maryam Yahaya bace. To a nan ne ake saka irin wannan hoton. (amman yin wancan salon kuma yaudara ce ya sabawa addininmu).
 • Privacy: shine yadda zaka zabi suwa kake so su kalli videon ka.

 

YouTube Privacy:

YouTube Privacy shine a wajen dora videonka zaka zabi suwa kake so su ga videon ka? Privacy a YouTube ya rabu gida uku (3) kamar haka:

 1. Private
 2. Unlisted
 3. Published
 • Private: shine babu wanda zai ga videon sai kai kadai.
 • Unlisted: shine baka son kowa ya ga videon sai wanda ka turawa link dinsa. (shine ga masu sayar da video a YouTube).
 • Published: shine ka sanya videonka yadda kowa da kowa zai iya gani.

Zan dakata a nan sai a rubutu na gaba.

RUBUTUKA MASU ALAKA:

[YouTube] Menene YouTube da Yadda Ake Bude Channel a YouTube?

[YouTube] Yadda Ake Samun Kudi Ta YouTube

[YouTube] Cikakken Bayani Akan Dandalin YouTube

[YouTube] Shafin YouTube Ya Kaddamar Da Tsarin Story A Dandalin

Basheer Sharfadi

07-05-2019.

Facebook Comments
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ku Saurari Fasaha Radio Kai Tsaye

Note: Fasaha Radio tana aiki tsawon awanni 24 domin wayar da kan al'umma akan yadda ake amfani da fasahar zamani.

Saurari Shirin Daga Shafukan Sadarwa

Shirin dake tattauna batutuwan da suka shafi shafukan internet da kuma rahotonni daga makarantunmu.

31-10-2019

14-09-2019

07-09-2019

31-08-2019

24-08-2019

10-08-2019

03-08-2019

26-07-2019

For Registering Domain Names, I trust DomainKing.NG

Subscribe To Our Youtube Channel

Subscribe To Khalyperh The Voice Channel

Subscribe To AU Studio On Youtube

Litattafai Cikin PDF

 1. Takardar Sanin Makama Ga Daliban Da Zasu Zana Jamb 2018 Download Now
 2. Mu Koyi Computer A Saukake Download Now
 3. Duniyar Facebook A Yau Download Now
 4. Yadda zaka fara neman kudi Online ta NNU Download Now
May 2019
M T W T F S S
« Apr   Jun »
 12345
6789101112
13141516171819
20212223242526
2728293031  

ADS

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG
error: Content is protected !!