Connect with us

Google

[Email] Yadda Ake Tura Sako ta Email

Published

on

how to send message on gmail in Hausa Language

[Email] Yadda Ake Tura Sako ta Email

 

Da yawa mutanenmu kan tafka kuskure a yayin tura sako ta email a don haka yau zanyi cikakken bayani akan yadda ake tura sako ta email.

 

Da farko idan ka shiga email dinka kayi login, idan kuma ka riga kayi to zai bude maka kamar yadda kake shiga Facebook zai budo maka inbox dinka wato wurin sakonni.

 

Zakaga alamar alkalami a kasa ko kuma an rubutu Compose to nan wurin shine inda ake shiga domin rubuta sako, tamkar inda ake shiga domin yin post a Facebook.

 

Idan ka shiga zai bude maka sabon shafi da gurabe acikinsa kamar haka:

  1. To
  2. Subject
  3. CC
  4. Body
  5. Send

To: a nan ne zaka rubuta adireshin Email na wanda zaka turawa sakon, misali zaka turon sako sai ka saka email dina info@sharfadi.com idan zaka tura da sako sama da email guda daya to sai ka saka alamar comer (,) a gaban email na farko sannan ka rubuta email na biyu ko guda nawa ne haka zakayi.

 

Subject: A nan ne zaka rubutu taken sakon da kakeson aikawa, kamar yadda akeyi a wasika, misali Sako Zuwa Ga Basheer Sharfadi, ko Sakon Neman…

 

CC: a nan idan kana so wasu suga cewa ka turawa wane sakon to sai ka saka email dinsu, misali ka turon mun sako amman kana so sauran abokaina su gani cewa ka turon to sai ka saka email dinsu a CC, shine zakuga a Facebook in akayi posting ana saka CC da sunayen mutane wato ana so sugani.

Body: nan ne zaka rubuta cikakken sakon da kakeson dorawa, idan akwai Document File kamar hoto da sauransu da kakeson daukowa duka a nan zaka dauko akwai wurin Attach kamar yadda kake gani a WhatsApp in zaka tura hoto.

Send: shine tura sakon wanda kana dannawa kai tsaye sakon zai tafi zuwa ga wanda ka turawa cikin kankanin lokaci, a wasu kuma zakaga alamar alkalami ko kibiya daga kasa.

 

Manyan Gurabe da Zaka Kula dasu acikin Email dinka:

Akwai gurabe da suke cikin email dinka ko kuma nace bangarori inda sako ke zirga-zirga acikinsu, zanyi bayanin wasu daga ciki mafiya muhimmanci.

 

Inbox

Social

Promotion

Sent

Out Box

Draft

Spam

Trash

 

Inbox: nan ne inda zaka ga sakonnin da aka turo maka ta Email

Social: Yana tattara sakonnin da aka turo maka na Social Media kamar in ka bude Facebook da Email din.

Promotion: Idan kayi subscribe na wasu shafuka kan su dinga turo maka da sakonni to zasu dinga tura maka email zaka sameshi a wannan folder din, kamar shafukan labarai da sauransu.

Sent: Anan zakaga duk wani sako da ka taba turawa wani.

Out Box: Idan ka tura sako sai ya fara shiga nan sannan ya tafi Sent da zaka tura sako ace bai jeba to cikin Out Box zaka duba zaka samu wannan sakon.

Draft: Zaka iya yin rubutu ka barshi aciki daga baya kazo ka tura ko ka daukeshi zuwa inda kakeso.

Spam: Yana tara sakonni wanda yake ganin basu da kyau, amman wani lokacin ana turo maka sako mai muhimmanci sai ya tafi cikin Spam don haka in kana neman sako zaka iya dubawa cikinta, a irin salo na idan rakuminka ya bata har cikin randa ma dubawa kake, idan baka duba sakon dake cikin Spam ba zai goge kansa bayan kwanaki 60 ko 90.

Trash: nan ne kwandon shara da yake ajiye sakonni da baka so, ko kuma ka goge.

 

Zan dakata a nan sai a rubutu a gaba.

RUBUTUKA MASU ALAKA:

Yadda Zaka Bude Email a Wayarka

[[Facebook]] Yadda masu amfani da Email din Yahoo ke cikin hatsarin rasa account dinsu na Facebook

[Email] Ance Na Tura Email Dina Shin A Yaya Zan Rubuta?

[Facebook] Shin Zan Iya Amfani Da Sabon Email Dina A Facebook Domin Yin Login?

Basheer Sharfadi

Social Media Strategists.

19-04-2019.

Facebook Comments
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ku Saurari Fasaha Radio Kai Tsaye

Note: Fasaha Radio tana aiki tsawon awanni 24 domin wayar da kan al'umma akan yadda ake amfani da fasahar zamani.

Saurari Shirin Daga Shafukan Sadarwa

Shirin dake tattauna batutuwan da suka shafi shafukan internet da kuma rahotonni daga makarantunmu.

31-10-2019

14-09-2019

07-09-2019

31-08-2019

24-08-2019

10-08-2019

03-08-2019

26-07-2019

For Registering Domain Names, I trust DomainKing.NG

Subscribe To Our Youtube Channel

Subscribe To Khalyperh The Voice Channel

Subscribe To AU Studio On Youtube

Litattafai Cikin PDF

  1. Takardar Sanin Makama Ga Daliban Da Zasu Zana Jamb 2018 Download Now
  2. Mu Koyi Computer A Saukake Download Now
  3. Duniyar Facebook A Yau Download Now
  4. Yadda zaka fara neman kudi Online ta NNU Download Now
April 2019
M T W T F S S
« Mar   May »
1234567
891011121314
15161718192021
22232425262728
2930  

ADS

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG
error: Content is protected !!