Connect with us

Digital Marketing

[YouTube] Yadda Zaka Saka YouTube Talla a YouTube

Published

on

[YouTube] Yadda Zaka Saka YouTube Talla a YouTube

Na san da yawanku kuna ganin talluka a lokacin da kukaje bude Video a YouTube sai dai da yawa mutane basu san yaya za’ayi suma su bada wannan tallan domin YouTube ya tallata masu ba.

Yana da kyau duk dan Social Media musamman na Siyasa su iya wannan domin zai taimaka musu sosai, kuma idan ka iyashi kaima zaka iya cajar wadanda zaka sanyawa tallansu su kuma su biyaka kudin aikinka da kuma kudin sakawa.

A yanzu hanyoyine mai sauki da zaka kirkiri tallanka a YouTube musamman idan ka saba amfani da sauran nauikan talla na Internet kamar su Facebook dasauransu.

Ga Hanyoyin da Akebi Wajen Kirkirar Talla a YouTube: –

 1. Da farko zaka fara bude Google Ads Account
 2. Bayan ka bude sai ka shiga wurin alamar Settings kamar yadda kake gani a hoton dake kasa.

 1. Sai ka danna Linked Account kamar yadda kuke gani a hoton dake kasa.

 

 1. Zai hade da Account dinka na YouTube idan kuma ba kaine mai Channel dinba to sai ka saka email din mai Channel

 2. A nan zai baka damar kayo Uploading (saka) Video din tallanka kamar yadda kuka sani Video ne na ‘yan sakann Some Seconds.

 3. Daga nan sai ka zabi nau’in tallan Campaigns sai ka danna wurin New Campaign.

Akwai nau’ikan talla kala-kala daga ciki akwai: –

a. Leads and Website Traffic: shine wanda zasu gayyaci mutane zuwa wani shafinka, kamar yadda kuke ganin tallan website kala-kala a YouTube kamar su gg.ng, Amazon, Wix dasauransu.

b. Product and Brand Consideration: Shine na masu tallata kayayyaki kamar kaga tallan Jaka, Mota, Takalmi da sauransu.

c. Brand Awareness and Reach: shine na yada wata manufa kamar tallan kungiyoyi ko kuma ‘yan siyasa da kuke gani a YouTube.

 1. Bayan ka saka Videon sai kuma ka zabi salon tallan da kakeso irin mai zuwa a gefen Video ko kuma a’a mai zuwa aciki, kamar yadda kuke gani a hoton dake kasa:

 

 1. Daga nan zaka iya yin Review kaga yaya tallanka zai kasance.

 

 1. Daga nan sai ka zabi sunan Campaign dinka da kuma tsawon ranakun da zaiyi.

 1. Sannan zaka zabi jama’ar yankin da kakeso YouTube ya tallatawa kayanka.

 1. Sannan zaka cike sharuda aciki zaka tabbatar musu da cewa babu batsa a tallanka da sauran abubuwa da Google suka haramta.

 2. Sannan zaka zabi jinsi da kuma nau’in mutanen da kakeso su kalla ‘yan shekara nawa zuwa ‘yan shekara nawa.

 3. Sannan ka zabi masu aure ko marasa aure.

 4. Masu sha’awar wasanni ko masu harkar kiwon lafiya da sauransu.

 5. Daga nan sai sanya kamar su tagging da sauransu.

 6. Sai kuma biyan kudin tallan.

Zamu dakata a nan sai a rubutu na gaba.

RUBUTUKA MASU ALAKA:

[YouTube] Menene YouTube da Yadda Ake Bude Channel a YouTube?

[Karanta Yanzu] Yadda zaka samu Subscribers a YouTube Channel dinka

[Labari] An Fara Kallon Video A YouTube Daga Kan WhastApp

[Facebok] YouTube Ya Samu Kishiya, An Fara Biyan Kudi ga Masu Dora Video a Facebook

Basheer Sharfadi

Social Media Strategists.

17-03-2019.

Facebook Comments
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ku Saurari Fasaha Radio Kai Tsaye

Note: Fasaha Radio tana aiki tsawon awanni 24 domin wayar da kan al'umma akan yadda ake amfani da fasahar zamani.

Saurari Shirin Daga Shafukan Sadarwa

Shirin dake tattauna batutuwan da suka shafi shafukan internet da kuma rahotonni daga makarantunmu.

31-10-2019

14-09-2019

07-09-2019

31-08-2019

24-08-2019

10-08-2019

03-08-2019

26-07-2019

For Registering Domain Names, I trust DomainKing.NG

Subscribe To Our Youtube Channel

Subscribe To Khalyperh The Voice Channel

Subscribe To AU Studio On Youtube

Litattafai Cikin PDF

 1. Takardar Sanin Makama Ga Daliban Da Zasu Zana Jamb 2018 Download Now
 2. Mu Koyi Computer A Saukake Download Now
 3. Duniyar Facebook A Yau Download Now
 4. Yadda zaka fara neman kudi Online ta NNU Download Now
March 2019
M T W T F S S
« Feb   Apr »
 123
45678910
11121314151617
18192021222324
25262728293031

ADS

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG
error: Content is protected !!