Connect with us

Instagram

[Instagram] Hanyoyi Biyar (5) da Zaka Tallata Kasuwancinka ta Instagram Story

Published

on

5 ways to promote your business on Instagram

[Instagram] Hanyoyi Biyar (5) da Zaka Tallata Kasuwancinka ta Instagram Story

 

Instagram Story shima tamkar Status a WhatsApp ana amfani dashi wajen tallata kasuwanci sai dai da dama ‘yan uwa basu san hanyoyin da akebi wajen tallata kasuwanci cikin sauki kuma a kyauta ta Instagram Story ba, a wannan takaitaccen bayanin nawa a yau zan kawo hanyoyi guda biyar (5) kacal da mutum zaiyi amfani dasu domin tallata kasuwancinsa a dandalin ‘yan birni na Instagram.

 

 1. Location mai yin kasuwanci a Instagram suna amfani da Location domin sanya bayanin kayan, misali ina sayar da jakunkuna a Kano ko kuma wani abu da nake son ‘yan Kano su siya to sai na saka Location na Kano ko kuma wasu yankuna na Kano ta yadda duk wanda yake wadannan yankunan zai ga wannan tallan nawa.

 

Amfani da Location a Instagram Story Yana Samar da Abubuwa Kamar Haka: –

 1. Jawo hankalin mutane zuwa ga abinda kake tallatawa
 2. Samun yawan mutane da zasu kalli tallanka.

 

 1. Mentioned zaka iya amfani da hanyar yin Mentioned domin ka kara tallata sakonka, misali ina sayar da Hoda, Turare, ko Man Shafawa to duk sanda zan tallata kayana a Story sai inyi mentioned din Costumers dina wanda hakan zai sanya su yin sha’awar siyan kayan, a takaice dai kana iya mentioned din ‘yan uwa da abokan arziki akan kayanka.

 

Yin Mentioned Yayin Tallata Kaya a Instagram Story na haifar da abubuwa kamar haka:

 1. Damar gayyatar sauran Account na Instagram
 2. Damar gayyatar masu sha’awar kayayyakin da kake siyarwa.

 

 1. # Hashtag amfani da Hashtag a Story hanya ce da zai baka dama wajen kara tallata kayanka, kamar yadda kuka sani a Instagram ana iya yin following na Hashtag kamar yadda ake yin na Account to duk sanda ka sanya wani Hashtag a Instagram Story dinka to za’a nunawa duk wanda yayi following wannan Hashtag din abinda ka saka.

 

Amfani da Hashtag a Instagram Story Yana Haifar da Abubuwa Kamar Haka: –

 1. Karin yawan mutane da zasu ga tallanka.
 2. Samun damar yin tagging na sauran mutane akan tallanka.

 

 1. GIF Stickers yana daga cikin hanyoyin da masu talla a Instagram ke amfani dasu wajen jan hankalin abokanan cinikayyarsu cikin kankanin lokaci, zakayi amfani dashi ta hanya biyu ka tallata kayanka sannan ka jinjina/yabawa abokanan cinikayyarka, idan ka yabawa mutum to shi kuma zaiyi kokarin taya ka tallatawa jama’a kayanka ba tare da ya sani ba, sai don murnar yaba masa da kayi.

 

Amfani da GIF Stickers a Instagram Story Yana Haifar da Abubuwa Kamar Haka: –

 1. Karin yawan mutane da zasu ga tallanka.
 2. Samun damar yin tagging na sauran mutane akan tallanka.
 3. Da sauran abubuwa da dama.

 

 1. Emoji Slider Stickers & Poll, Emoji baya bukatar wani dogon bayanin kowa ya san yadda ake amfani da alamomin Emoji wajen isar da sako misali ina son nuna maka cewa ina cikin farin ciki, ko harara, bacin rai ko cikin kauna Love duk akwai alamomin da zan iya daukowa, to wadannan alamomin ana amfani dasu wajen tallata kaya a Instagram Story haka kuma ana amfani da Poll (zabe) wajen kara jan hankalin jama’a shine zaku ga ana tambayar abu ko kuma a baka zabin Yes/No akan abu da sauransu, wanda shima yana taimakawa matuka wajen isar da sako.

 

Amfani da Emoji Slider Stickers & Poll a Instagram Story Yana Haifar da Abubuwa Kamar Haka: –

 1. Zaka dinga samun bayanan jama’a (ra’ayoyo) akan yadda kayanka suke.
 2. Karin yawan mutane da zasu ga tallanka.
 3. Samun damar yin tagging na sauran mutane akan tallanka.
 4. Da sauran abubuwa da dama.

 

Zan dakata a nan sai a rubutu na gaba.

RUBUTUKA MASU ALAKA:

Hanyoyi Ashirin (20) Da Zaka Bunkasa Kasuwancinka Ta Instagram

[Ka Karanta Yanzu] Hanyoyi Goma (10) Da Zaka Samu Followers A Instagram

Ka San Tsarin Kasuwanci a Instagram {Instagram for Business)

[Instagram] An Fara Dora Video Mai Tsayi na Sama da Sa’a Guda a Instagram

Basheer Sharfadi

Social Media Strategists.

16-03-2019.

Facebook Comments
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ku Saurari Fasaha Radio Kai Tsaye

Note: Fasaha Radio tana aiki tsawon awanni 24 domin wayar da kan al'umma akan yadda ake amfani da fasahar zamani.

Saurari Shirin Daga Shafukan Sadarwa

Shirin dake tattauna batutuwan da suka shafi shafukan internet da kuma rahotonni daga makarantunmu.

31-10-2019

14-09-2019

07-09-2019

31-08-2019

24-08-2019

10-08-2019

03-08-2019

26-07-2019

For Registering Domain Names, I trust DomainKing.NG

Subscribe To Our Youtube Channel

Subscribe To Khalyperh The Voice Channel

Subscribe To AU Studio On Youtube

Litattafai Cikin PDF

 1. Takardar Sanin Makama Ga Daliban Da Zasu Zana Jamb 2018 Download Now
 2. Mu Koyi Computer A Saukake Download Now
 3. Duniyar Facebook A Yau Download Now
 4. Yadda zaka fara neman kudi Online ta NNU Download Now
March 2019
M T W T F S S
« Feb   Apr »
 123
45678910
11121314151617
18192021222324
25262728293031

ADS

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG
error: Content is protected !!