Connect with us

WhatsApp

[WhatsApp] Dalilan da Yasa WhatsApp Ke Dakatar da Mutum daga WhatsApp

why whatsapp banned my number in Hausa

[WhatsApp] Dalilan da Yasa WhatsApp Ke Dakatar da Mutum daga WhatsApp

 

A kwanakin nan na samu korafe-korafe da dama daga ‘yan uwa kan dandalin sada zumunya na WhatsApp sunyi Banning nasu wato sun rufe lambar mutum bashi da damar yin WhatsApp, kana kai zasu koreka kamar dai yadda Facebook keyin Blocking wannan sabon abune ga wasu, amman dama can akwai wannan tsarin sai dai kawai yanzu za’a iya cewa irin ta shugaban Nigeria da yace da zafi-zafi za’ayi Next Level to suma sun gwadata ne a nan wajen daukan mataki mai tsauri.

 

Kar na cikaku da surutu ina tafe da dalilan dake sawa WhastApp su salami mutum don haka sai kayi kokarin kiyayewa gudun samun matsala, kana ji kana gani duk dadin WhatsApp dinnan ace sai ka canja lamba.

 

  1. Yin amfani da wani Application a madadin WhastApp ko mai taimaka masa, akwai WhatsApp kala-kala amman guda daya tak wanda kuke gani a Play Store shi kadaine mallakar kamfanin WhatsApp kuma bayaso kayi amfani da wanda ba nasa ba, amman zaka ga Apps sunyi kare-kare sosai abubuwan da baka iya yi a WhatsApp su zaka iya yi a kansu, to WhatsApp baya son wannan kuma yana rufe lambar duk masu yin amfani da irin wadannan Application
  2. Yawan tura sako ga wanda bashi da lambarka, takurawace mutum bashi dalambar ka, ka dameshi da tura masa sako, WhatsApp sun dauki wannan a matsayin laifi domin kana musgunawa wani, don haka tilas mutum ya guji yawan tura sako ga lambar da mai lambar bashi da taka lambar, matukar kana yawan yin hakan to zasu rufe lambarka, duk wanda zakuyi chat kayi masa Hands-free kace masa yayi saving lambarka.
  3. Ka dinga saka mutane a Group wadanda basu da lambarka, haka kawai sai mutum ya bude Group baka da lambarsa kaga ya saka ka aciki ka fita ya kara adding dinka, wannan shima babban laifine a kundin WhatsApp yana da kyau duk wanda zaka saka a Group ya zama yana da lambarka kaima kana da tasa, wannan shine ya sanya da yawa aka dinga rufe lambobin masu Group saboda kawai zasuce duk me son shiga group ya basu lambarsa, a maimakon hakan gwara ka fitar da link na Group
  4. Idan ka aikata daya daga cikin wadancan laifukan sai mutane suka dinga yin reporting dinka to shima WhatsApp zai kori lambarka, misali ka sakani a Group na fita ka kuma sani to a karo na biyu zan fara Blocking dinka ne sannan na fita, to WhatsApp suna lura da wannnan.

 

Daya daga cikin wannan dalilan shi zaisa kana cikin WhatsApp sai kaga an koroka waje an rubuta maka “Your phone number ******** is temporarily banned from WhatsApp. Contact Support “.

 

Wato dai an rufe Account dinka na WhatsApp.

 

Zan dakata a nan sai a rubutu na gaba.

RUBUTUKA MASU ALAKA:

[WhatsApp] Yadda Zaka Dawo da Lambar da Aka Dakatar Daga Yin WhatsApp

[WhatsApp] Yadda Zaka Dakatar da Posting Sai Iya Admin Kadai a Group Din WhatsApp

[[Karanta Yanzu]] Hanyoyi Bakwai (7) Da Zaka Tantance Ingancin Sako a WhatsApp

[WhatsApp] Yadda WhastApp Ke Cinye Space a Waya da Yadda Zaka Magance Matsalar

[[WhatsApp]] Yadda Zaka Duba Chat Din Abokinka Ta Whatsap

[Facebook] Yadda Zaka Kare Facebook Dinka daga Blocking ko Hacking

[[Facebook]] Yadda Ake Dawo Da Facebook Din Da Aka Sace

Yadda Ake Dawo Da Facebook Din Da Akayi Disable

 

Basheer Sharfadi

Social Media Strategist.

04-03-2019.

Email: info@sharfadi.com

Phone: +2349035830253

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Saurari Shirin Daga Shafukan Sadarwa

Shirin dake tattauna batutuwan da suka shafi shafukan internet da kuma rahotonni daga makarantunmu.

31-10-2019

14-09-2019

07-09-2019

31-08-2019

24-08-2019

10-08-2019

03-08-2019

26-07-2019

For Registering Domain Names, I trust DomainKing.NG

Subscribe To Our Youtube Channel

Subscribe To Khalyperh The Voice Channel

Subscribe To AU Studio On Youtube

Litattafai Cikin PDF

  1. Takardar Sanin Makama Ga Daliban Da Zasu Zana Jamb 2018 Download Now
  2. Mu Koyi Computer A Saukake Download Now
  3. Duniyar Facebook A Yau Download Now
  4. Yadda zaka fara neman kudi Online ta NNU Download Now
March 2019
M T W T F S S
 123
45678910
11121314151617
18192021222324
25262728293031

ADS

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG
error: Content is protected !!