Connect with us

YouTube

[YouTube] Menene YouTube da Yadda Ake Bude Channel a YouTube?

Published

on

how to create a youtube channel in Hausa Language

[YouTube] Menene YouTube da Yadda Ake Bude Channel a YouTube?

 

Jama’a Assalamu Alaikum, a yau zanyi bayani akan yadda ake bude Channel a YouTube.

 

Menene YouTube:

YouTube daya ne daga cikin shafukan sadarwa na yanar gizo mallakar kamfanin Google wanda ke baiwa mutum damar kallar video da kuma dora video a kai, ta yadda zai samu damar aikawa da mutane sakon video, YouTube shine shafi na biyu a duniya da al’umma suka fi ziyarta. adireshin YouTube shine www.youtube.com.

 

Menene YouTube Account?

YouTube account shine ka mallaki account a dandalin YouTube, wato kayi register dasu.

KARANTA MA’ANAR GOOGLE

Meye Banbancin YouTube Account da Google Account?

YouTube kamar yadda nayi bayani a baya mallakar kamfanin Google ne don haka matukar kana da account na Google to shine da account na YouTube ma’ana dai da Gmail, da Google Account da Kuma YouTube account duka abu ne guda daya.

 

YouTube Personal Account:

Da zarar kayi register (bude account) da YouTube to ka mallaki personal account akai tamkar ace ka mallaki account din facebook, kuma zaka iya kalla za kuma ka iya dora video akai, zai sanya sunanka akan account din.

 

YouTube Channel:

YouTube Channel shine kamar muce shafi a dandalin facebook kana da account kuma sai ka samar da shafi, Misali kana da gida sai ka fasa kofa ka fitar da shago da zaka dinga yin kasuwanci.

YouTube Channel shine kamar ka mallaki tasha a dandalin YouTube ana bukatar ka tsara channel dinka sosai da sosai.

Dukkan masu neman kudi a YouTube zaku ga suna da channel ne inda mutum zai je ya nemi su.

Yadda Ake Bude YouTube Channel:

 1. Mataki na farko kay register (ka shiga) YouTube da Google Account dinka wato Gmail

 

Idan Baka da Google Account Shiga Nan Domin Budewa

 

 1. Idan kaje com zaka ga “sign in” daga sama sai ka shiga , zai baka dam aka zabi ko ka saka account dinka.

 

 1. Bayan kayi wannan shine tamkar kayi login a YouTube yanzu abu nag aba shine ka bude channel account shi kuma yadda zakayi shine, ka duba sama wurin da ka danna kayi sign in zaka ga yanzu alamar farkon sunanka ne ko kuma hotonka, ana kiran nan wurin alamar user a turance sai ka shiga.

 

 1. A kasan nan zaka ga “settings” sai ka shiga.

how to create a youtube channel in hausa

 1. Idan ya bude zai baka wurin “additional features” sai ka shiga.
 2. Zakan ga “create new channel” sai ka shiga.

how to create a youtube channel in hausa

 

 1. A nan zai baka dam aka cike sunan channel dinka da kake so misali Sharfadi TV sai ka saka.

 Zakan ga “create new channel” sai ka shiga.

 1. Daga nan zai baka damar saka hoto na profile da cover d.s.

 

Shikenan ka bude channel.

 

Zan dakata a nan sai a rubutu na gaba.

RUBUTUKA MASU ALAKA:

YADDA ZAKA SAMU KUDI A YOUTUBE

YADDA ZAKA SAMU SUBSCRIBERS DA YAWA A YOUTUBE CHANNEL DINKA

Basheer Sharfadi

Social Media Strategists.

20-02-2019.

Facebook Comments
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Continue Reading
1 Comment

1 Comment

 1. Tanimou Hachimou

  June 18, 2019 at 8:06 pm

  BARKA inada tanbayar kan YouTube yaya zanhadachida Google Ads faga dalibinka tanimou Hachimou

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ku Saurari Fasaha Radio Kai Tsaye

Note: Fasaha Radio tana aiki tsawon awanni 24 domin wayar da kan al'umma akan yadda ake amfani da fasahar zamani.

Saurari Shirin Daga Shafukan Sadarwa

Shirin dake tattauna batutuwan da suka shafi shafukan internet da kuma rahotonni daga makarantunmu.

31-10-2019

14-09-2019

07-09-2019

31-08-2019

24-08-2019

10-08-2019

03-08-2019

26-07-2019

For Registering Domain Names, I trust DomainKing.NG

Subscribe To Our Youtube Channel

Subscribe To Khalyperh The Voice Channel

Subscribe To AU Studio On Youtube

Litattafai Cikin PDF

 1. Takardar Sanin Makama Ga Daliban Da Zasu Zana Jamb 2018 Download Now
 2. Mu Koyi Computer A Saukake Download Now
 3. Duniyar Facebook A Yau Download Now
 4. Yadda zaka fara neman kudi Online ta NNU Download Now
February 2019
M T W T F S S
« Jan   Mar »
 123
45678910
11121314151617
18192021222324
25262728  

ADS

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG
error: Content is protected !!