Connect with us

Facebook

[[Facebook]] Yadda masu amfani da Email din Yahoo ke cikin hatsarin rasa account dinsu na Facebook

Published

on

[[Facebook]] Yadda masu amfani da Email din Yahoo ke cikin hatsarin rasa account dinsu na Facebook

 

Da yawa masu amfani da email na Yahoo a facebook suna cikin hatsarin rasa account dinsu, kuma mafi yawan wadannan sune wadanda suka fara facebook tun a farkon farowarsa a nan kasar.

 

A lokacin da aka fara facebook duk wanda zai bude sai yaje café su kuma suna amfani da email domin bude masa, a wancan lokacin kuma Yahoo shine email din da yake tashe, shine wanda ake yayi.

 

To sai mutum ya cigaba da amfani da wannan email din wajen shiga facebook dinsa, ba tare da yana zuwa kuma ya shiga kan email dinsa na yahoo dinba.

 

Shi kuma yahoo akwai tsawon lokacin da in ka dauka baka hawa account dinka to zasu rufe maka shi.

 

To idan aka samu irin wannan matsalar duk sanda facebook dinka ya samu matsala, sai suce sun tura maka da sako cikin email dinka na yahoo kai kuma a lokacin sai kayi tayi amman yahoo dinka ba zai bude ba, domin sun riga sun rufe maka shi.

 

Kaga Kenan ka rasa account dinka.

 

YADDA ZAKA MAGANCE WANNAN MATSALAR SHINE:

 

Da farko dolene ka mallaki wani email din mai rai, wato wanda yake aiki, idan yahoo ne ka tabbatar da kana shiga akai-akai.

 

Duba Wannan:- Yadda Ake Bude EMAIL

 

Bayan ka mallaki email mai rai, sai kaje facebook dinka ka sanya (adding) din sa a kai.

 

Yadda Ake Saka Email a Facebook:

Kayi amfani da browser kayi login a facebook dinka a www.facebook.com sai ka shiga <profile> sai ka shiga <about> kayi kasa har wajen email sai ka shiga <edit> zai baka add/remove sai ka shiga ka saka sabon email din naka sannan ka saka password dinka zasu aika maka da Activation Link ta Email din, sai ka shiga ka dannan Activating din, shikenan ka dora wannan email din akai.

 

Yadda Zaka Mayar da Sabon Email dinka Primary Email:

Kamar yadda ka shiga wurin email dinka a profile na facebook din haka zaka koma sai ka zabeshi a matsayin Primary wato email dinka mafi muhimmanci, shima zaka saka password dinka shikenan yanzu sabon email dinka ya zama shine primary email dinka, daga nan idan zakayi login a facebook dinka to kana saka sabon email din da password dinka facebook dinka zai bude.

 

Yadda Zaka Cire Tsohon Email Dinka Daga Kan Facebook:

Shima zaka shiga profile dinka kaje wurin email kaje wajen tsohon email dinka (Yahoo) shiga wurin edit sai ka dannan remove zaka saka password dinka daga nan shikenan ka cireshi, daga nan ba zaka kara yin login da wannan tsohon email dinba, ko ka saka ba zai budu ba saboda facebook bai sanshi ba tunda ka cireshi, Kenan zaka koma shiga da sabon email dinka.

Rubutuka Masu Alaka:

Yadda Zaka Kare Account Dinka na Facebook

Yadda Ake Dawo da Facebook din da aka sace

Yadda Ake Dawo da Facebook din da akayi Disabled

Mungode sosai da ka tsaya ka karanta wannan bayanin.

 

Basheer Sharfadi

Social Media Strategists.

30-01-2019.

Facebook Comments
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ku Saurari Fasaha Radio Kai Tsaye

Note: Fasaha Radio tana aiki tsawon awanni 24 domin wayar da kan al'umma akan yadda ake amfani da fasahar zamani.

Saurari Shirin Daga Shafukan Sadarwa

Shirin dake tattauna batutuwan da suka shafi shafukan internet da kuma rahotonni daga makarantunmu.

31-10-2019

14-09-2019

07-09-2019

31-08-2019

24-08-2019

10-08-2019

03-08-2019

26-07-2019

For Registering Domain Names, I trust DomainKing.NG

Subscribe To Our Youtube Channel

Subscribe To Khalyperh The Voice Channel

Subscribe To AU Studio On Youtube

Litattafai Cikin PDF

  1. Takardar Sanin Makama Ga Daliban Da Zasu Zana Jamb 2018 Download Now
  2. Mu Koyi Computer A Saukake Download Now
  3. Duniyar Facebook A Yau Download Now
  4. Yadda zaka fara neman kudi Online ta NNU Download Now
January 2019
M T W T F S S
« Dec   Feb »
 123456
78910111213
14151617181920
21222324252627
28293031  

ADS

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG
error: Content is protected !!