Connect with us

Digital Marketing

[Online Business] Menene Kasuwancin eBook Marketing?

Published

on

Abin takaici ne yadda ‘yan arewa muke da tarin dubban marubuta na harshen Hausa amma ace kullum sai kara samun koma baya sukeyi maimakon suyi gaba, musamman tasgaron da suka samu na rashin tafiya da zamani, a baya tilas ne ka buga littafi a takarda sannan ka sayar dashi littafinka ya karbu, amman yanzu abin ba haka yake ba.

Zaka rubuta ka wallafa littafi kuma ya yadu ko ka siyar ba tare da kayi shi a bugun takarda ba, dukkanku kun sani yanzu muna cikin zamanin da cigaba ke kara hauhawa wanda kuma in baka bishi ba to tilas a barka da sallallami!

Yau a Nigeria manyan shafukan da suke hada-hadar kasuwancin litattafai ta Iternet mallakar ‘yan Kudu ne! shin babu marubuta  Arewa??

Akan haka na takarkare na danyi shimfida kadan akan ma’anar tsarin kasuwancin litattafai da kuma salon da ake yinsa da bangarorin da yake dashi.

Menene eBook Marketing:

eBook Marketing daya ne daga kasuawancin yanar gizo wanda ke baiwa mutum damar saye da kuma siyan litattafai ta yanar gizo, eBook Marketing zai baka damar bajakolin basirarka/ki musamman ga marubuta ta yadda zasu bunkasa sana’arsu musamman ta bangaren samun kudin shiga.

Wannan kasuwancin yana samar da littafai ne wadanda za’a iya amfani dasu ta yanar gizon ba wai littafi wanda ake bugawa a iya tabashi a hannu ba.

Sannan ana iya yinsa ba tare da wasu tarin tsarabe-tsarabe ba domin kuwa har a waya mutum zai iya gudanar da wannan kasuwancin.

Rubutuka Masu Alaka:

Menene Kasuwancin MINI IMPORTATION?

Yadda Ake Amfani da Tsarin Kasuwancin Facebook

Tsarin eBook Marketing:

eBook Marketing zai baiwa mutum damar ya ga littafi da kuma takaitaccen bayanin littafin amman sai dai ba zaka iya samun sauke ko karanta cikakken littafin ba har sai ka biya kudin littafin.

Tsarin Cinikayyar eBook Marleting:

Wasu shafukan suna yin tsarin biya ta katin waya, ko kuma ta account din banki

Bangarorin eBook Marketing:

eBook Marketing yana da bangarori kamar haka:

 1. Marubuci/Mawallafi
 2. Mai Shago
 3. Mai Talla
 4. Mai Saye
 • Marubuci/Mawallafi: Shine jigon eBook Marketing domin shine yake da kadarar da ake siyarwa, shine marubucin dake rubuta littafi.
 • Mai Shago: Shine mai shafin da marubuci zaije ya saka littafinsa domin tallata shi ga jama’a. Idan aka siya mai shago yana daukan kasonsa aciki.
 • Mai Talla: Shine wanda zaije shafin (wurin mai shago) ya dauki tallan littafi ya tallata,
 • Mai Saye: shine wanda zai ga littafin ya birgeshi sai ya siya.

BA IYAKAR RUBUTUN KENAN BA INSHA ALLAH ZAN DORA A GABA.

Basheer Sharfadin Kano

26-01-2019.

 

Rubutuka Masu Alaka:

Ma’anar Kasuwancin Yanar Gizo da Kuma Rabe-Rabensa

Ire-Iren Kasuwancin Yanar Gizo

Abubuwan da Kake Bukata Domin Fara Kasuwancin Yanar Gizo

Facebook Comments
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Ku Saurari Fasaha Radio Kai Tsaye

Note: Fasaha Radio tana aiki tsawon awanni 24 domin wayar da kan al'umma akan yadda ake amfani da fasahar zamani.

Saurari Shirin Daga Shafukan Sadarwa

Shirin dake tattauna batutuwan da suka shafi shafukan internet da kuma rahotonni daga makarantunmu.

31-10-2019

14-09-2019

07-09-2019

31-08-2019

24-08-2019

10-08-2019

03-08-2019

26-07-2019

For Registering Domain Names, I trust DomainKing.NG

Subscribe To Our Youtube Channel

Subscribe To Khalyperh The Voice Channel

Subscribe To AU Studio On Youtube

Litattafai Cikin PDF

 1. Takardar Sanin Makama Ga Daliban Da Zasu Zana Jamb 2018 Download Now
 2. Mu Koyi Computer A Saukake Download Now
 3. Duniyar Facebook A Yau Download Now
 4. Yadda zaka fara neman kudi Online ta NNU Download Now
January 2019
M T W T F S S
« Dec   Feb »
 123456
78910111213
14151617181920
21222324252627
28293031  

ADS

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG
error: Content is protected !!