Hanyoyi Goma Sha Takwas [18] da Zaka Iya Samun Kudi ta Internet

Hanyoyi Goma Sha Takwas [18] da Zaka Iya Samun Kudi ta Internet

Rubutuka Masu Alaka:

Ma’anar Kasuwancin Yanar Gizo da Rabe-Rabensa

Kasuwanci da Samun Kudi ta Yanar Gizo

  1. Facebook Marketing: – hanya ta farko shine mutum ya shiga harkar cinikayya da tallace-tallace ta facebook.
  2. Freelancing: – shine tsarin da zakayi wani aiki a biyaka, wannan sana’ar ana yinta kamar mutum yayi rubutu, fassara, editing ko wani abu da kake da kwarewa akan sa a biyaka, daga cikin manyan wuraren da ake wannan sana’ar akwai shafin Fiverr
  3. Email Marketing: – shine tsarin kasuwanci da tallace-tallace wadda ake yinsa ta email.
  4. Instagram for Business: – shima tsarin kasuwancin Instagram iri daya ne da irin tsarin na facebook.

Duba Nan: Karanta Yadda Tsarin Kasuwancin Instagram Yake

5. Mini Importation: – shine kasuwancin da zai baka damar shigo da kananan kayayyaki daga kasashen waje zuwa gida Nigeria.

Duba Nan: Karanta Cikakken Bayani akan Mini Importation

6. Affiliate Marketing: – shi kuma tsarin kasuwanci ne da ake yin sa tsakanin mutane uku mai kaya, mai shago da dan talla, ta yadda in ka siyar da kaya kana da naka kason, kuma duka ana yinsa ta internet.

Duba Nan: Yadda Zaka Fara Amfani da Tsarin Kasuwancin NNU

7. Pay per click: – tsarine irin na Affiliate Marketing din sai dai shi link ne za’a baka duk wanda yabi ta ciki kana da kasonka.

8. Pay per sale: – shi kuma sai in mutum ya sayi abu ta bangarenka to za’a biyaka naka kason

9. Pay per lead: – Shima nau’ine na Affiliate Marketing amman shi ana biyan mutum ne idan ya nunawa wani zuwa wurin wani zaka ga form ne zaka tallatawa mutum ya cike online da wasunsu.

10. Pay per view: – shi kuma adadin mutanen da suka kalli abinda aka baka tallansa shine za’a baka naka kason.

11. eBook Marketing: – shine hada-hadar cinikayyar kasuwancin litattafai ta internet.

12. Online Courses: – shine wadanda ke koyar da wani abu ta yanar gizo ana biyansu kada ka raina abinda ka iya kawai ka tashi kayi shi.

13. Video Marketing:- shi kuma nau’ine na hada hadar cinikayyar video a yanar gizo.

Duba Nan: Yadda Zaka Fara Samun Kudi ta YouTube

14. Apps Marketing: – shine tsarin kasuwancin na manjaja (application) kamar yadda kuke gani wasu app sai mutum ya biya, sannan akwai wuraren da za’a sanyawa app dinka talla ajiki a dinga biyanka.

15. Games: – suma games da kuke gani ba karamin kudi ake samu dasu ba, shi yasa zaku ga talluka sunyi yawa acikinsu.

16. Blogging:- Sune marubtan da suke rubutu a shafukan internet shima hanyace babba wadda take kawo kudi a yanar gizo.

Duba Nan: Ma’anar Blogging da Yadda Ake Samun Kudi da Blogging

17. Online Forum: – shine ka kirkiri wani zaure a yanar gizo da zai dinga hada jama’a a nan Nigeria kamar Nairaland

18. YouTube:- Gabace mai zaman kanta amman tana karkashin bangaren Video Marketing.

 

Abubuwan suna da fadi kuma suna da yawa sosai, amman a hankali InshaAllah zamu cigaba da kawosu.

Rubutuka Masu Alaka:

Abubuwan Da Kake Bukata Domin Fara Kasuwancin Yanar Gizo

Karanta Ire-Iren Kasuwancin Yanar Gizo

[Radio Program] Social Media da Kasuwancin Yanar Gizo -Arewa Radio Kano

Facebook Comments
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG
error: Content is protected !!