[YouTube] Yadda zaka samu Subscribers a YouTube Channel dinka

Yadda zaka samu Subscribers a YouTube Channel dinka

A yau zanyi magana akan hanyoyin da mutum zaibi domin samun mabiya a YouTube, da yawa masu channel a YouTube sunayin kukan shan wahalar gaske kafin samun mabiya, hakan kuwa baya rasa nasaba da rashin bin wadannan matakan da zan kawo.

Rubutuka Masu alaka:

[YouTube] Menene YouTube da Yadda Ake Bude Channel a YouTube?

Yadda Yaro Dan Shekara 7 da Ya Samu Sama da Biliyan Bakwai ta YouTube

  1. Ka dinga sanya video mai kyau wanda zai ja hankalin jama’a hakan zai sanya duk wanda ya gani yayi subscribing.
  2. Kayi Title mai kyau sosai wanda zai ja hankalin jama’a a videon ka.
  3. Ka dinga fadawa masu kallon video dinka cewa suyi subscribing kamar yadda kuke gani a sauran channel suna sanarwa ayi subscribe sannan a danna kararrawar sauti.
  4. Kayi blocking duk video din da zakayi uploading ta yadda babu wanda zai kara saka wannan videon sai kai, duk mai bukata a iya channel dinka zai gani.
  5. Ka dinga sharing zuwa sauran social media da kake yi kamar su facebook WhatsApp d.s
  6. Ka yi amfani da Hashtag kamar yadda kuke gani a wasu channel din misali na saka video akan Kano to akwai wurin tag sai in saka Kano idan kuma ta waya ne acikin wurin description sai na saka #Kano d.s ba iya sai guda daya ba, duba cikakken bayanin hashtag a nan.
  7. Kayi amfani da website dinka wajen tallata channel dinka, ka sanya yadda mutane zasuyi subscribing din channel dinka daga kan website dinka.
  8. Zaka iya biyan facebook su tallata maka ta tsarin Facebook for Business.

Wadannan wasu ne daga cikin hanyoyin da in ka bisu InshaAllahu zaka samu mabiya (followers) sosai a YouTube dinka.

 

Zan dora a gaba Insha Allahu.

Basheer Sharfadi

Social Media Strategist.

January, 2019.

Rubutuka Masu Alaka:

[YouTube] Yadda Ake Samun Kudi Ta YouTube

[YouTube] Yadda Ake Dora Video a YouTube

Yadda Ake Sauke Video daga YouTube

An Fara Kallon Video akan YouTube ta WhatsApp

Facebook Comments
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG
error: Content is protected !!