Connect with us

Google

[Google] Yadda Google Ke Samun Kudin Shiga

Published

on

[Karanta Yanzu] Ta Yaya Google Ke Samun Kudin Shiga?

Da yawa ‘yan uwa muna shiga Google mu tambayi abu kuma ya bamu amsa, amman shin mun taba tunanin ko ta yaya Google din ke samun kudin shiga?

Domin google ba wai suna yin raba dai-dai ne da kamfanunuwan waya da kake siyan Data ba sannan shi Google duk sanda kayi search ba ma shafinsa yake mayar da kai ba, sai dai ya kawo maka amsoshi daga shafukan wasu.

Kuma a fili yake cewa ba wasu ne suka dauki nauyin google ya dinga wannan aikin ba, to wai yaya abin yake?

Rubutuka Masu Alaka:

Yadda Kamfanin Facebook Ke Samun Kudin Shiga

Yadda Instagram Ke Samun Kudin Shiga

Yadda Masu Amfani da Social Media ke Samun Kudin Shiga

A duk lokacin da kayi amfani da google domin tambayar wani bayani to google zaiyi kokari yaga ya kawo maka bayanin wannan abin da ka tambaya, sannan zai kawo maka sakamako masu alaka da abinda ka tambaya wanda mafi yawanci daga sashen Google Adwords Advertisement shi kuma sashi ne da Google ke amfani dashi wajen kawo maka talla a dukkanin bangarorinta, shine tallukan da kake gani idan ka shiga Gmail, YouTube, Google Maps, Google Plus, da sauran application na Google.

To wadannan tallukan biyan google ake don haka idan kayi searching wani abun google yana iya hado maka da talla, haka kuma kaima kana iya biyan google don su kara tallata shafinka ta yadda da anyi searching na abinda kake yi google din zai kawo shafinka a farko, wannan dayace daga cikin hanyoyin da google ke samun kudin shiga.

Google AdSense shi kuma tsari ne da google ke karbar talluka daga kamfanunuwa da kuma mutane wanda zasu biya google, shi kuma google zai yi amfani da shafukan (websites) da sukayi register da shi ta wannan tsarin, ko kuma YouTube wanda yake da register, irin wannan sune tallukan da kuke gani a shafukan internet kamar su BBC HAUSA, DAILY NIGERIAN, DAILY TRUST dama namu na SHARFADI.COM haka shine kuke gani a yayin da kukaje kallon video a YouTube, google kan biya masu wadannan shafin daga yadda ake dannan tallukan dake kan shafinsu, haka ma masu YouTube, Google na biyansu daga cikin kudin da ake biyansa sannan shima ya dauki nasa kason.

A shekarar da ta gabata ta 2018 Google yana da ma’aikata kusan Dubu Saba’in da Biyar 75,000 kuma ma’udan kudade yake biyansu a matsayin albashi, kaga ko ba’a fada maka ka san ba kananun kudi google ke samu ba.

Bayan wadannan manyan hanyoyin kuma Google ya kanbi wasu kananun hanyoyi domin samun kudin shiga.

Yanzu ya rage naka kaima kayi kokarin shiga hanyar neman kudi ta internet.

 

Basheer Sharfadi

Social Media Strategist.

January, 2019.

Facebook Comments
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Ku Saurari Fasaha Radio Kai Tsaye

Saurari Shirin Daga Shafukan Sadarwa

Shirin dake tattauna batutuwan da suka shafi shafukan internet da kuma rahotonni daga makarantunmu.

14-09-2019

07-09-2019

31-08-2019

24-08-2019

10-08-2019

03-08-2019

26-07-2019

For Registering Domain Names, I trust DomainKing.NG

Subscribe To Our Youtube Channel

Subscribe To Khalyperh The Voice Channel

Subscribe To AU Studio On Youtube

Litattafai Cikin PDF

  1. Takardar Sanin Makama Ga Daliban Da Zasu Zana Jamb 2018 Download Now
  2. Mu Koyi Computer A Saukake Download Now
  3. Duniyar Facebook A Yau Download Now
  4. Yadda zaka fara neman kudi Online ta NNU Download Now
January 2019
M T W T F S S
« Dec   Feb »
 123456
78910111213
14151617181920
21222324252627
28293031  

ADS

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG
error: Content is protected !!