Connect with us

Facebook

[Google] Yadda Zaka Gano Bayananka Da Kamfanin Google Da Facebook Ke Dauka Da Kuma Yadda Zaka Karesu

Published

on

Yadda Zaka Gano Bayananka Da Kamfanin Google Da Facebook Ke Dauka Da Kuma Yadda Zaka Karesu

Na san dukkaninku kuna ganin yadda ake satar account din mutane a facebook a canja musu suna da makamantansu sai dai wani abin takaici shine wadannan barayin suna satar duk wani bayanan mutum dake kan account dinsa.

Hackers masu kutse na gida da na wajen Nigeria babban abinda suke so su samu game da mutum shine bayananka, suna adireshi, lambar waya, email, Ranar haihuwa, ginsi, d.s.

Hatta irin sakonnin waya da zaka ga an turo maka ta lambar wayarka wanda baka da alaka dashi kamar ace maka ATM dinka ya samu matsala ko wani abu naka, to mutanen dake yin wannan suna amfani ne da bayananka da suka sace, kuma idan aka saci na abokin mu to lamarin zai iya muma shafarmu wadanda yake da lambobin wayarmu.

A yau zan hasko muku yadda Facebook da Google ke sarrafa bayananka ta yaso kuma dabara ta rage ga mai shiga rijiya…

Rubutuka Masu Alaka :

Yadda Zaka Gano Wanda Ya Fara Saka Hoto a Internet

Yadda Zaka Kare Facebook Dinka Daga Blocking Ko Hacking

Ana Tuhumar Google Da Facebook Da Karya Dokar Kare Bayanai

Bara na danyi mi’ara koma baya kadan:-

Idan kazo yin register dasu facebook google d.s zaka amince da sharudansu wanda wannan sharudan daga ciki akwai damar gani da kuma amfani da bayananka, Wanda ta wannan hanyarce yanzu idan na baka lambata kayi saving a contact dinka anjima kana hawa facebook sai kaga sun tallato maka ni kayi adding dina.

Da wannan bayanin ne idan ka shiga google kayi wani bincike kana hawa facebook sai kaga an turo maka bayani mai alaka da abinda ka bincika.

Sai dai a doka iya su wadannan kamfanunuwan ne ya halatta suyi amfani da wannan bayanan naka, bai halatta su baiwa kowa ba sai dai in umarni suka gani daga hukuma akan wani bincike da ake akanka.

Wannan ba iya su facebook ba har su layin waya, Account din banki da muke budewa.

To akwai masu aikata laifi a gefe wadanda suke yin kutse su kuma su saci bayananka don su cutar da kai.
Bayanin yana da fadi amman nayi cikakken bayani a shrinmu na Mukoyi Computer a Saukake na Express Radio Kano shirin da mukayi bayani akan Masu Yin Kutse a Internet.

  1. Google Yana tattara duk bayanan wani abu da kakeyi a Internet wannan zai sa ka tuno lahira inda Allah zaiyi hisabi wannan link din da zan kawo nan ne zaka shiga zaka ga duk wani shafi da ka taba shiga a Internet tun daga farawarka zuwa yau matukar kana amfani da Google:-
    https://myactivity.google.com/myactivity

Idan baka so wasu su dinga samun bayani akanka ta google to ka shiga nan ka canja settings dinka:-
https://myaccount.google.com/privacycheckup

Google na tallata maka wasu bayanai wanda a tunanin google kana da sha’awarsu to shima zaka iya shiga wannan link din domin gyarawa:-
https://adssettings.google.com/authenticated

  1. Haka abin yake a wurin dan uwan dayan wato Facebook shi kuma yadda zaka magance shine ka shiga <Settings> <Security and Privacy> <App and Websites> <Ads> shima zaka saita shi yadda kake so kamar na Google.

Zan dakata a nan sai a rubutu na gaba.

Basheer Sharfadi
Social Media Strategist.
January, 2019.

Facebook Comments
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Ku Saurari Fasaha Radio Kai Tsaye

Saurari Shirin Daga Shafukan Sadarwa

Shirin dake tattauna batutuwan da suka shafi shafukan internet da kuma rahotonni daga makarantunmu.

14-09-2019

07-09-2019

31-08-2019

24-08-2019

10-08-2019

03-08-2019

26-07-2019

For Registering Domain Names, I trust DomainKing.NG

Subscribe To Our Youtube Channel

Subscribe To Khalyperh The Voice Channel

Subscribe To AU Studio On Youtube

Litattafai Cikin PDF

  1. Takardar Sanin Makama Ga Daliban Da Zasu Zana Jamb 2018 Download Now
  2. Mu Koyi Computer A Saukake Download Now
  3. Duniyar Facebook A Yau Download Now
  4. Yadda zaka fara neman kudi Online ta NNU Download Now
January 2019
M T W T F S S
« Dec   Feb »
 123456
78910111213
14151617181920
21222324252627
28293031  

ADS

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG
error: Content is protected !!