Connect with us

News

Dan Iya Yayi Sati Guda A DSS Saboda Facebook

Zuwa Ga ‘Yan Uwana ‘Ya’yan Malam Talaka!

Labarin Dan Iya A DSS

Idan ka san babanka Gwaska ne ba sai ka karanta ba.

Dan uwa da ‘yar uwa ‘ya’yan mai karas da dan mai yalo zalla!

A wannan lokacin da zabe yake tahowa duk mun cika social media da zage-zagen ‘yan siyasar da basa iya yi mana komai.

Ina son muyi tunani cewa Buhari da Atiku, Kwankwaso da Ganduje duk suna da ‘ya’ya amman ba’a ganinsu suna kare Iyayensu a Social Media ko kuma kai kafi su son Iyayensu?

Ka tuno cewa kana da ‘yan uwa kuma suna sonka kaima na san kana son su, baza kaso ka jefasu cikin tashin hankali ba, ka tuno shin yaya zasu ji in suka wayi gari baka nan?

*Labarin Dan Social Media*
Dan Iya ya hau facebook ya zage wani babban dan siyasa a garinsu wai don ya kare dan siyasar da yake goyon baya.

Dan siyasar da aka zaga ya dauki waya ya kira wanda dan iya yake karewa yace “kasan wani yaro wani?” yace “bai sanshi ba!” (kuma bai sanshin ba).

Don haka ya samu qwarin gwiwa yayi kararsa a DSS Dan Iya yana wajen Qwadagonsa da ‘Yar wayarsa Vivo ranar ba Data yana jiran ya gama qwadago yaje ya saka Data ‘yar turi.

Kawai sai yaji an kirashi “sunana wane daga hukuma kaza! Yanzu kana wuri kaza to kayi maza kazo office dinmu wuri kaza yanzu”

Kafin jami’i ya gama magana Dan Iya ya yanke jiki ya fadi!

A karshe Dan Iya ya shafe kusan sati guda a hannun hukuma mahaifiyarsa kullum tana faman kuma saboda babu abinda zata iya yi akai, hakan ma wai Dan Siyasar ne ya tausaya masa ya yafe masa.

Shine yake taimakawa mahaifiyarsa da Dan Cefane gashi ya zaune tsawon sati guda….

Budar bakin wanda Dan Iya yake karewa sai yace “yara ne matsiyata marasa kunya!”.

A nan zan barku da labarin Dan Iya!

Yanzu Dan uwa da ‘Yar uwa ka kalli koda gwamnonin Kano mafi yawansu ba ‘Ya’yan Talaka bane, Rimi, Kwankwaso da Ganduje duk ‘Ya’yan Dagatai ne.
To kai Dan Malam Talaka daman Allah ya haliccekane don ka kare a wahala??

Basheer Sharfadi
Gaskiya Da Gaskiya
#HateSpeach #Political #2019Election #WeAre4Peace #Peace4Arewa #Arewa #Hausa #Kano #SiyasarKanoSaiKano

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Saurari Shirin Daga Shafukan Sadarwa

Shirin dake tattauna batutuwan da suka shafi shafukan internet da kuma rahotonni daga makarantunmu.

31-10-2019

14-09-2019

07-09-2019

31-08-2019

24-08-2019

10-08-2019

03-08-2019

26-07-2019

For Registering Domain Names, I trust DomainKing.NG

Subscribe To Our Youtube Channel

Subscribe To Khalyperh The Voice Channel

Subscribe To AU Studio On Youtube

Litattafai Cikin PDF

  1. Takardar Sanin Makama Ga Daliban Da Zasu Zana Jamb 2018 Download Now
  2. Mu Koyi Computer A Saukake Download Now
  3. Duniyar Facebook A Yau Download Now
  4. Yadda zaka fara neman kudi Online ta NNU Download Now
December 2018
M T W T F S S
 12
3456789
10111213141516
17181920212223
24252627282930
31  

ADS

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG
error: Content is protected !!