Connect with us

Instagram

[Online Business] Hanyoyi Ashirin (20) Da Zaka Bunkasa Kasuwancinka Ta Instagram

Published

on

Hanyoyi Ashirin (20) Da Zaka Bunkasa Kasuwancinka Ta Instagram

Instagram shima kamar sauran shafukan sadarwa na internet ana amfani dashi wajen tallata haja, tunda dai malam dan Hausa yace mai talla shike da riba…

Kayi searching @jiffpom a instagram wadda take bayyana kanta a matsayin kare, amma yanzu haka tana da mabiya Miliyan Takwas da dubu dari biyar 8.5M a Instagram kuma tana cikin wadanda ke kan gaba wajen samun kudi a instagram.

Bara na kyale labarinta haka, Yau Ina tafe da hanyoyi guda ashirin cir! Wanda zasu taimaka maka wajen cicciba kasuwancinka a Instagram sai a biyoni sau da kafa.

 1. Kayi bayanin kasuwancinka a Bio din account dinka, ka saka takaitaccen bayanin abubuwan da kake siyarwa.

 2. Ka dinga neman mabiyanka suyi tagging din abinda ka saka, zaka ga idan masu tallan kaya a instagram sukayi posting suna rubuta “tag friend”.

 3. Ka dinga neman irin wanda suke irin sana’arka a shafin kaga yadda suke nasu tsarin, kuma ka dinga tagging dinsu a post dinka, Da wannan hayar Kanny Wood suka mamaye Instagram a Arewacin Nigeria.

 4. Ba ko yaushe zaka dinga posting akan kasuwanci ba, Ana son ka dinga yin posting na nishadantawa lokaci zuwa lokaci

 5. Ka dinga yin Garabasa (Promo) kamar dai a lokutan azumin Ramadhan ko Sallah d.s.

 6. Ka dinga tallata kayanka a comment din abokanka, Ka dinga shiga tattaunawar da ta shafi sana’arka.

 7. Ka dinga yin “repost” na posting din mabiyanka, tamkar kana yaba musu hakan zai sa su dinga daraja kayanka.

 8. Account dinka ya zama biyu personal mai sunanka da kuma na kasuwancinka yadda zaka dinga mentioned din kowanne.

 9. Ka kaucewa yin duk wani posting da bai dace ba, na cin zarafi ko kuma na tada tarzoma.

 10. Ka dinga yin posting na abubuwan dake da alaka da al’ummar da kake son su sayi kayanka.

Hanyoyi Goma Da Zaka Samu Followers A Instagram

An Bada Damar Dora Video Mai Tsawon Sama Da Awa Guda A Instagram

Yadda Tsarin Kasuwancin Instagram Yake

 1. Ka dinga taya followers dinka murna a duk ranaku kamar sabuwar shekara, da makamantansu.

 2. Ka dinga amfani da HashTag na abinda kake siyarwa da Abinda keda alaka dashi da kuma yankin da kake.

 3. Ka saka link din tallan kayanka a bio link.

 4. Ka tsara rubutu da hotuna masu kyau wanda zasu ja hankali.

 5. Ka saka location din inda kasuwancinka yake a Instagram din.

 6. Ka sanya alamar kira (call) a account dinka.

 7. Ka dinga saka link din kayanka a story. Da HashTag a story din.

 8. Kayi amfani da salon siyar da kaya kyauta abinda mutum zai biya shine kudin kawowa, misali kayan N300 ne kudin kai masa kuma N150 to sai kace ga kaya yau kyauta kawai kudin kawowa mutum zai biya N500.

 9. Ka dinga yin live video kana tallata kayan aciki.

 10. Ka dinga biyan Instagram su tallata maka kayanka.

Allah ya bada sa’a.

RUBUTUKA MASU ALAKA:

[Instagram] Hanyoyi Biyar (5) da Zaka Tallata Kasuwancinka ta Instagram Story

[[Instagram]] An Fara Yin Chatting a Instagram ta Computer

[Karanta Yanzu] Yadda Instagram Ke Samun Kudin Shiga

Basheer Sharfadi
Social Media Strategist.
20-12-2018.

Facebook Comments
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ku Saurari Fasaha Radio Kai Tsaye

Saurari Shirin Daga Shafukan Sadarwa

Shirin dake tattauna batutuwan da suka shafi shafukan internet da kuma rahotonni daga makarantunmu.

14-09-2019

07-09-2019

31-08-2019

24-08-2019

10-08-2019

03-08-2019

26-07-2019

For Registering Domain Names, I trust DomainKing.NG

Subscribe To Our Youtube Channel

Subscribe To Khalyperh The Voice Channel

Subscribe To AU Studio On Youtube

Litattafai Cikin PDF

 1. Takardar Sanin Makama Ga Daliban Da Zasu Zana Jamb 2018 Download Now
 2. Mu Koyi Computer A Saukake Download Now
 3. Duniyar Facebook A Yau Download Now
 4. Yadda zaka fara neman kudi Online ta NNU Download Now
December 2018
M T W T F S S
« Nov   Jan »
 12
3456789
10111213141516
17181920212223
24252627282930
31  

ADS

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG
error: Content is protected !!