Connect with us

Computer

[Computer] Taza Da Tsifa Dangane Da Virus A Computer 💻

Published

on

Menene Virus a Computer?
Virus shine kwayar cutar dake kama na’urar computer sannan take yi mata illa kamar yadda cuta take yiwa mutum illa. Virus na zuwa a tsarin code ko kuma yaren baiwa computer umarni.
Virus yana lalata bayanan da ya samu akan computer.
Masu yin kutse a na’urar computer da internet sune ke kirkirar mafi yawan virus domin su samu damar leken asirin wasu computers din.

Ta Ina Virus Yake Shafar Computer?
Virus yana lalata programs da akayi installing (software’s) ko kuma kaya (files, document) dake kan computer.
Idan virus yakama computer ka to zaka iya shafawa sauran computer dake alaka da ita kamar ta networks ko kuma offline wajen karbar wasu bayanai daga wasu computer din.

Ta Ina Ake Samun Virus?
Ana samun virus a computer ta hanyoyi kamar haka:
1. Sakonnin Email & Text messages
2. Files da kake download daga internet
3. Link da kake budewa ta internet,
Ka kula da kyau kada kayi downloading a shafin da baka gasgata ba.

Alamomin Dake Nuna Virus Ya Kama Computer Dinka Sune:
1. Window dinka zai dinga daukewa, screen din computer zai dinga yin baki, wani lokacin ma ya kashe maka computer din.
2. Dawo da kai Home page kana cikin yin aiki a computer sai ta dawo da kai farko.
3. Ka dinga ganin wani ya tura sako ta email dinka dake kan computer din.
4. Lalacewar kayanka, Haka kawai sai ka ga kayanka sun zama virus, Video, Audio, Hotuna da software’s.
5. Computer dinka ta dinga yin yawan slow bata sauri.
6. Idan ka bude computer dinka, ko kayi restart kawai sai wani program ya bude kai tsaye ba tare da ka shiga ba.
7. Password ba dai-dai ba, kazo kayi ta saka password tace ba dai-dai bane ko kuma an canja.
8. Ka dinga ganin computer ka tana yi maka shutcut na foldoji da programs.
9. Computer dinka ta dinga yin kara.

Ire-iren Virus:
1. Boot sector virus:- shine wanda yake samun computer yayin da ka kunna ta ko kuma kayi restart ko kuma ka saka wani USB wanda yake da Virus.
2. Web scripting virus: sune wanda mutum zai iya kwasowa yayin da ya shiga wasu shafukan internet dake dauke da Virus.
3. Browser hijacker: shine wanda zaka ga duk sanda ka bude browser dinka sai kaga ta tafi wani shafi daban ba tare da ka bata umarni ba.
4. Resident virus: shine virus din da ita kanta computer dince ke haifar dashi saboda baka kula da ita, akwai files marasa amfani akai.
5. Macro virus: shine wanda yake shafar sakonni musamman na email.
6. Rootkit virus: yana hawa computer dinka a rashin sani, yana baiwa wadanda suka kirkire shi damar su sarrafa computer dinka, Su dauki files da suke so su goge wanda suke so.

Yadda Zaka Cire Virus Daga Computer Dinka:
1. Ka dinga amfani da windows defender wadda take zuwa acikin computer.
2. Ka nemi anti virus software’s kayi installing ka dinga amfani dasu.

Yadda Zaka Kare Computer Dinka Daga Kawumawa Da Virus
1. Ka dinga scanning din computer dinka lokaci zuwa lokaci.
2. Ka dinga updating windows defender.
3. Kada ka bude sakon baka tantance ba idan aka turo maka sakon email.
4. Ka dinga amfani da karin software’s na anti virus.
5. Idan ka saka USB ka dinga jira ya gama budewa kafin ka shiga.
6. Kayi scanning kafin fara amfani bayan ka saka mata USB
7. Kayi eject kafin ka cire USB din.
8. Kada ka bude duk file da ka gani da wannan alamar a karshensa “txt.vbs” wannan alama ce ta virus a computer.
9. Ka dinga goge temporary files yadda zaka goge shine ka shiga <> Start Menu <> All Programs <> Accessories <> System Tools <> Disk Cleanup <> shikenan.
10. Ka dinga tabbatar da ingancin memory ko waya kafin ka jonawa computer dinka.

12. Kada ka dinga Kama WIFI din da ba naka ba sai da iznin mai shi.

Allah Ya Kiyaye Mu Daga Virus Amin.

RUBUTUKA MASU ALAKA:

[Computer] Virus da Yadda Za’a Maganceshi a Computer -Express Radio Kano

[Computer] Menene Wi-Fi Mouse Kuma Yaya Ake Amfani Dashi? PDF

[Computer] Microsoft Excel da Yadda Ake Amfani Dashi

[Computer] Power Point da Yadda ake Amfani Dashi

Basheer Sharfadi
Social Media Strategist.
06-12-2018.

Facebook Comments
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ku Saurari Fasaha Radio Kai Tsaye

Note: Fasaha Radio tana aiki tsawon awanni 24 domin wayar da kan al'umma akan yadda ake amfani da fasahar zamani.

Saurari Shirin Daga Shafukan Sadarwa

Shirin dake tattauna batutuwan da suka shafi shafukan internet da kuma rahotonni daga makarantunmu.

31-10-2019

14-09-2019

07-09-2019

31-08-2019

24-08-2019

10-08-2019

03-08-2019

26-07-2019

For Registering Domain Names, I trust DomainKing.NG

Subscribe To Our Youtube Channel

Subscribe To Khalyperh The Voice Channel

Subscribe To AU Studio On Youtube

Litattafai Cikin PDF

  1. Takardar Sanin Makama Ga Daliban Da Zasu Zana Jamb 2018 Download Now
  2. Mu Koyi Computer A Saukake Download Now
  3. Duniyar Facebook A Yau Download Now
  4. Yadda zaka fara neman kudi Online ta NNU Download Now
December 2018
M T W T F S S
« Nov   Jan »
 12
3456789
10111213141516
17181920212223
24252627282930
31  

ADS

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG
error: Content is protected !!