Connect with us

Google

[Google] Menene Google Drive Kuma Yaya ake Amfani Dashi?

Published

on

Menene Google Drive Kuma Yaya Ake Afani Dashi?

Assalamu Alaikum, Yau a shirin mu na 27 za muyi magana akan Google Drive da kuma yadda ake amfani dashi sai ku biyo mu.

Rubutuka Masu Alaka:

Yadda Zaka Dora Lambobin Wayarka Akan Google

Yadda Ake Bude Gmail

Menene Google Drive:
Google Drive wurin ajiye bayanai ne kamar dai Memory Card dinka, zaka iya ajiye video, audio da ma hoto da kuma sauran document dinka akai, kamfanin google suka samar dashi a ranar 24 ga watan April na shekara ta 2012, ana iya mafani dashi a waya da kuma Computer.
Zaka iya saka wani file dinka akai sannan ka baiwa mutum link dinsa shima ya sauke ma’ana dai zaka iya turawa mutum wani file ta google drive.
Google Drive suna bada Gigabytes 15 kyauta ga duk wanda ke amfani da account na google ma’ana idan kana da Gmail to ka mallaki Gigabytes 15 a Google Drive dinka, idan mutum yana son sama da haka to kamfanin google suna siyarwa ma’ana zaka biya kudi, Google Drive yana amfani ne da Data wajen sanyawa da kuma sauke abu akai.

Yadda Ake Amfani Da Google Drive:

Yadda ake amfani dashi a Computer:
Zaka ziyarci www.drive.google.com
Sai ka yo uploading din files dinka da kake son ajiyewa akan Drive din.
Sai kayi sharing in kana so ma’ana ka fitar da link dinsa yadda zaka iya baiwa wani ya sauke, ko kuma ka gyara wani abun aciki.

Yadda Ake Amfani dashi a waya:
Ka shiga application mai suna “Drive” wanda yake cikin jerin application da mafiya yawa android tana zuwa dasu sai dai da yawa mutane ba’a amfani dashi, ko kayi searching dinsa a Play Store.
Idan ka shiga anan zaka gani idan ka sanya gmail dinka akan wayar kai tsaye zai budo maka idan ma kana da files akai zaka gani.
Akwai alamar “+” wadda itace zaka danna domin dora sabbin files dinka.
Akwai menu dinsa kamar sauran app a gefe.

Rubutuka Masu Alaka:

Ka Shiga Kayi Karatu Kyauta Daga Kamfanin Google

Yadda Zaka Nemi Aikin Yi A Garinku Ta Google

Amfanin Google Drive:
Amfani da files dinka a duk sanda kake so a ko ina kake, misali ina Kano sai na ajiye files dina a Drive wataran ina Abuja sai bukatar wannan files din ta taso to kawai zanyi login a drive ne koda ba a wayata bane na sauke wannan files din.
Aikawa da wasu sakonka ta nan ta yadda zaka iya baiwa mutum dama ya sauke wani sako da kake son tura masa misali daga nan Nigeria zaka iya turawa mutumin da yake London sakon wasu files daga nan.
Yin aiki da Document dink aba tare da network ba “Work Offline” akwai inda zaka shiga ka tsara files dinka a menu na Google Drive su zama zaka iya amfani dasu koda baka Network (Data) ma’ana bayan kayi Uploading.
Backup na files dinka misali idan zaka sake installing WhatsApp zaka gay a baka dama ka dawo da tsohon chat dinka wanda shima yana adana maka shi ne a wancan Drive din naka.
Zaka iya yin searching na duk wani file da ka ajiye a Drive din.
Zaka iyi yin Scanning ko Snapping na Credential dinka ko wasu takardunka masu muhimmanci ka adanasu a Drive.
Yana adana maka duk wani sako da ya hada da hoto sauti ko document da aka aika maka dashi ta gmail dinka, ko bayan tsawon lokaci idan kaje Drive zaka ga wannan sakon.

Zan dakata anan sai a rubutu na gaba mai taken “Menene True Caller Kuma Yaya Ake Amfani Dashi?”

Domin samun sauran rubutuka masu alaka da wannan da muka tattauna a baya sai a ziyarci www.sharfadi.com
Domin Karin haske ko shawarwari ko aiko da wani batu da kakeson a tattauna a kai sai a tuntubi:

Email: info@sharfadi.com
Call & WhatsApp: 09035830253

RUBUTUKA MASU ALAKA:

Shin Ko Kasan Ma’anar Google?

Google Reverse: Yadda Zaka Gano Wanda Ya Fara Saka Hoto A Internet

Yadda Ake Yin Bincike A Google

Facebook Comments
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Continue Reading
3 Comments

3 Comments

 1. Mubarak

  July 8, 2018 at 4:40 pm

  Allah ya kara basira. Godiya muke

 2. Mubarak Rabiu

  November 25, 2018 at 11:46 am

  Thanks you malam basheer and God bless you for your great contributions in the world of internet, and convincing others to the

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ku Saurari Fasaha Radio Kai Tsaye

Note: Fasaha Radio tana aiki tsawon awanni 24 domin wayar da kan al'umma akan yadda ake amfani da fasahar zamani.

Saurari Shirin Daga Shafukan Sadarwa

Shirin dake tattauna batutuwan da suka shafi shafukan internet da kuma rahotonni daga makarantunmu.

31-10-2019

14-09-2019

07-09-2019

31-08-2019

24-08-2019

10-08-2019

03-08-2019

26-07-2019

For Registering Domain Names, I trust DomainKing.NG

Subscribe To Our Youtube Channel

Subscribe To Khalyperh The Voice Channel

Subscribe To AU Studio On Youtube

Litattafai Cikin PDF

 1. Takardar Sanin Makama Ga Daliban Da Zasu Zana Jamb 2018 Download Now
 2. Mu Koyi Computer A Saukake Download Now
 3. Duniyar Facebook A Yau Download Now
 4. Yadda zaka fara neman kudi Online ta NNU Download Now
July 2018
M T W T F S S
« Jun   Aug »
 1
2345678
9101112131415
16171819202122
23242526272829
3031  

ADS

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG
error: Content is protected !!