Mu Koyi Computer A Saukake 008
MICROSOFT POWER POINT:
(Darasi Na Karshe A Wannan Takardar)
Daya daga cikin manhajoji dangin Microsoft suits da mukayi bayani a baya, kuma yana da matukar muhimman ci sosai ana yin amfani dashi wajen tsara Presentation na wajen taro da kuma hada slide show,
Da farko ana bude shi ne kamar yadda ake bude word da sauran manhajoji da mukayi a baya, bayan an bude yana da abubuwa da dama akan sa amman a wannan mataki na farko zamu dauki abubuwa guda biyar (5) ne kacal sai a biyo mu.
- Home:- anan ne zaka ga alamomin rubutu kamar yadda suke a Microsoft word
2. Insert:- a nan ne idan zaka sanya wani abu kamar hoto ko sound ko video da sauran su
3. Design:- anan zaka dauki wane irin salo kake so tsarin aikin da kake yi ya kasance, tsarin kala da kuma design
4. Transitions:- anan zaka zabi yadda kake so design dinka ya fito, misali kana so ya wul-wula ko ya bullo ko ya tarwaste
5. Aminations:- anan zaka zabi yadda kake so design dinka ya fito, misali kana so ya wul-wula ko ya bullo ko ya tarwaste, a yaya kake so abinka yazo? amma akan iya abinda kayi hylighting kamar rubutu ko wani hoton shi kadai.
Alhamdulillah anan ne muka kawo karshen wannan takarda ta biyu.
RUBUTUKA MASU ALAKA:
MENENE EXCEL KUMA YAYA AKE AMFANI DASHI?
MENENE MA’ANAR COMPUTER
BANGARORIN COMPUTER DA IRE-IRENTA
Basheer Journalist Sharfadi
www.sharfadi.com
Email: info@sharfadi.com
09035830253
#BasheerSharfadi #Computer
April 2018.
Muazu sani
April 10, 2018 at 9:07 pm
Allah ya saka da Alkhairi
Auwal Isah
May 6, 2018 at 9:08 am
Alhamdulillah…
Munyi Farin Ciki Kuma Muna Fatan Khairan
Dahiru Musa Turaki
November 9, 2018 at 5:18 pm
Masha Allah.
Allah ya saka da alkarri.