Connect with us

Ana Yi Muna Jin Dadi

Yadda Zaka Bude Email a Wayarka

Published

on

ANA YI MUNA JIN DADI 007
((YADDA AKE BUDE EMAIL))

Jama’a Assalamu Alaikum da fatan kuna cikin koshin lafiya acikin shirin mu na wannan lokaci shiri na bakwai (7) zanyi bayani akan yadda ake bude email, sai ku biyo mu,

Email: wanda ake kira a turance da Electronic Mail: tamkar wani adreshi ne naka na yanar gizo-gizo ko wani gida naka da idan ana neman ka nan za’aje, idan za’a baka sako nan za’a tura maka, sannan kai ma idan zaka turawa wani sako to sai ka shiga naka email din ka tura sakon,
Sai dai email din nan akwai kala daban-daban ba wai guda daya bane,

EMAIL DINA BIYU NE INA DA EMAIL KUMA INA DA GMAIL:- wannan magana ce da dayawa mutane keyi wadda kuma kuskure ne, misali idan aka ce waya an san akwai waya iri-iri kamfani daban-daban amman duka sunan su waya, haka idan aka ce Mota kowa ya san mota kala-kala ce ba kala daya kawai ba, to idan akace email shima sunan su ne amman idan kace kana da email to kana bukatar yin bayanin shin wane iri ne email din? Gmail ne ko Hotmail, Yahoo da sauran su, ba wai email din shima wani email ne mai zaman kansa ba a’a kawai suna ne, sannan akwai samfirin email kala-kala sunfi shurin masaki,

Rubutuka Masu Alaka:

Menene Ma’anar Google?

Yadda Zaka Dora Lambobin Wayarka a Google

Yadda Zaka Nemi Aikin Yi a Garinku ta Google

 1. YADDA ZAKA BUDE EMAIL NA GMAIL:- da farko ya kamata kasan wani abu game da gmail shi email ne na shahararren kamfanin nan na “matambayi baya bata” (google) kuma idan ka mallake shi to ka mallaki account a wurare kamar haka: Youtube, Google, da Google Plus, da sauran tarin bangarori da google suke dashi, sannan idan kana da android dole zata bukaci ka sanya mata gmail account, wannan kadan kenan,
 2. Idan ka tashi bude email na gmail zaka je www.gmail.com ko www.google.com sai ka shiga “signin” a kasa kuma zaka ga “create account” sai ka shiga,
 3. Daga nan zai budo maka wajen saka suna guda biyu daya sunan ka dayan kuma na mahaifi
 4. Sai kuma wajen saka yadda kake so email din ya kasance misali: hussainauwalu01@gmail.com nake so ya kasance ina saka hussainauwalu01 zai yi min searching idan wani ya riga ya dauki wani sunan zai fada maka sai ka canja, sannan zai baka zabi na wasu misali zai iya ce maka hussainauwalu200 ko 150 da makamanta su yace ka zaba to zaka iya zaba idan kuma akwai wata lamba da kake son sakawa kamar 2017 ko karshen lambar wayarka ko shekarar haihuwarka kawai sai ka saka,
 5. Daga nan sai wajen saka “password” shima guri biyu ne saboda idan ka saka a a farko za kuma ka tabbatar dashi a na biyun, shi kuma akalla kada ya gaza harufa shida (6) sannan ka saka kalma da kuma lambobi
 6. Daga nan sai ka cike ranar haihuwar ka da wata da kuma shekara,
 7. Sai kuma shin kai namiji ne ko mace (jinsi)
 8. Sannan sai ka saka lambar wayarka amman wajen idan kaga ba tutar kasarka bace sai ka shiga ka nemo kasar ka ka danna sai ka saka lambar amman ka cire “0” din farko,
 9. Daga sai saka “current email” shine idan kana da wani email din sai ka saka shi amman na gmail, idan baka dashi kafin ka fara bude email din ka samu wanda yake dashi ya baka nasa zai zamo kamar wanda ya tsaya maka idan gmail dinka ya samu matsala za’a iya amfani da account dinsa a gyara maka,
 10. Daga nan sai ka danna wajen “I agree to the Google terms of Services and Privacy Policy”
 11. Daga nan zai budo maka wajen da zai gaya maka zasu turo maka da sakon “code” ta lambarka sai ka zaba su turo maka sakon ko su kira ka a wayar su fada maka?
 12. Sai ka danna “next” zasu kawo ka inda zaka saka “code” din sai ka saka,
 13. Mene ne “code” din? Lambobi ne zasu turo maka,
 14. Daga nan zaka danna alamar “next” shikenan zasu nuna maka suna tayaka murna da zuwa dandalin gmail,
 15. Shi kenan account dinka ya bude.

 16. YADDA ZAKA BUDE EMAIL NA YAHOO:- shi ma kamar wancan na sama ne ga kuma link din da zaka bidon budewa https://www.yahoo.com/

 17. YADDA ZAKA BUDE EMAIL NA HOTMAIL:- shi ma kamar wancan na sama ne ga kuma link din da zaka bidon budewa https://www.hotmail.com/
 18. YADDA ZAKA BUDE EMAIL NA NAIJ:- shi ma kamar wancan na sama ne ga kuma link din da zaka bidon budewa https://www.mail.naij.com/

Zan dakata anan sai a shiri na gaba mai taken yadda ake bude email.

 

Facebook Comments
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Facebook Comments

Continue Reading
2 Comments

2 Comments

 1. Free Cryptocurrency

  March 3, 2018 at 5:10 pm

  Mannabase a new Cryptocurrency is actually giving away FREE coins every week to new users. The best part is they are a Humanitarian organisation set to be bigger than Bitcoin. This could be the Biggest Free Investment you ever make. If you have 5 Minutes spare read the Whitepaper these Guys are something else. http://bit.ly/-FreeCryptocurrency

 2. Voice Comments

  March 21, 2018 at 3:13 am

  WordPress has now enabled voice comments for websites. Bring your website up to date and get the free plugin here, http://bit.ly/Voice-Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ku Saurari Fasaha Radio Kai Tsaye

Note: Fasaha Radio tana aiki tsawon awanni 24 domin wayar da kan al'umma akan yadda ake amfani da fasahar zamani.

Saurari Shirin Daga Shafukan Sadarwa

Shirin dake tattauna batutuwan da suka shafi shafukan internet da kuma rahotonni daga makarantunmu.

31-10-2019

14-09-2019

07-09-2019

31-08-2019

24-08-2019

10-08-2019

03-08-2019

26-07-2019

For Registering Domain Names, I trust DomainKing.NG

Subscribe To Our Youtube Channel

Subscribe To Khalyperh The Voice Channel

Subscribe To AU Studio On Youtube

Litattafai Cikin PDF

 1. Takardar Sanin Makama Ga Daliban Da Zasu Zana Jamb 2018 Download Now
 2. Mu Koyi Computer A Saukake Download Now
 3. Duniyar Facebook A Yau Download Now
 4. Yadda zaka fara neman kudi Online ta NNU Download Now
February 2018
M T W T F S S
    Mar »
 1234
567891011
12131415161718
19202122232425
262728  

ADS

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG
error: Content is protected !!