Sharfadi.com – Gaskiya Da Gaskiya Shine Muradina
Duniyar Facebook A Yau -Basheer Sharfadi PDF

Duniyar Facebook A Yau -Basheer Sharfadi PDF

Takarda Da Na Gabatar A Babban Taron Kungiyar Wayar Da Kan Matasa Akan Siyasa Ba Da Gaba Ba Ta DUNIYA MAI FADI Wadda Aka Gabatar Ranar Asabar 14 August 2018, A Dakin Taro Na Murtala Muhammad Library Dake Kano. Danna “Download Now” Domin Sauke Cikakkiyar Takardar Dake Kan Wayarka. Bangarori: Gabatarwa Ma’anar Social Media Meye Banbancin Social Media Da Sauran Kafafan Yada Labarai? Yadda Zaka Kare Account Dinka Na Facebook Wasu Daga Abubuwan Da Yakamata Ka Lura Dasu A Facebook Me Yakamata Ka Rubuta A Facebook? Shin Ana Bautar Da Mutane A Facebook? Yadda Zaka Sauke Video Daga Facebook Da Youtube. Wadanne Shafuka Yakamata Ka Mallaka A Yanar Gizo-Gizo? Wadanna […]

Read More
Yadda Zaka Tura Sako A Group Din WhatsApp Sama Da Guda Daya A Lokaci Guda

Yadda Zaka Tura Sako A Group Din WhatsApp Sama Da Guda Daya A Lokaci Guda

Ana Yi Muna Jin Dadi 030 Yadda Zaka Tura Sako A Group Din WhatsApp Sama Da Guda Daya A Lokaci Guda www.sharfadi.com Assalamu Alaikum, Yau a shirin mu na 29 za muyi magana akan Yadda Zaka Tura Sako A Group Din WhatsApp Sama Da Guda Daya A Lokaci Guda sai ku biyo mu. Yadda Zaka Yi Shine: Da farko kana bukatar ka sauke wannan application din na WhatsApp ta hanyar amfani da link din dake kasa. https://abo2sadam.net/UP/WA4.Abo2Sadam-V6.40.apk Sai kayi installing dinsa, zaka iya installing dinsa da wata lambar daban ya zama kana da whatsApp guda biyu a waya daya . Sai ka danna alamar menu dake saman WhatsApp dinka. Zai […]

Read More
Yadda Zaka Tura Sako A Group Din WhatsApp Sama Da Guda Daya A Lokaci Guda

Yadda Zaka Tura Sako A Group Din WhatsApp Sama Da Guda Daya A Lokaci Guda

Ana Yi Muna Jin Dadi 030 Yadda Zaka Tura Sako A Group Din WhatsApp Sama Da Guda Daya A Lokaci Guda www.sharfadi.com Assalamu Alaikum, Yau a shirin mu na 29 za muyi magana akan Yadda Zaka Tura Sako A Group Din WhatsApp Sama Da Guda Daya A Lokaci Guda sai ku biyo mu. Yadda Zaka Yi Shine: Da farko kana bukatar ka sauke wannan application din na WhatsApp ta hanyar amfani da link din dake kasa. https://abo2sadam.net/UP/WA4.Abo2Sadam-V6.40.apk Sai kayi installing dinsa, zaka iya installing dinsa da wata lambar daban ya zama kana da whatsApp guda biyu a waya daya . Sai ka danna alamar menu dake saman WhatsApp dinka. Zai […]

Read More
Yadda Zaka Dakatar Da Posting A Group Din WhatsApp Sai Iya Admin Kadai

Yadda Zaka Dakatar Da Posting A Group Din WhatsApp Sai Iya Admin Kadai

Ana Yi Muna Jin Dadi 029 www.sharfadi.com Yadda Zaka Dakatar Da Posting A Group Din WhatsApp Sai Iya Admin Kadai Assalamu Alaikum, Yau a shirin mu na 29 za muyi magana akan Yadda Zaka Dakatar Da Posting A Group Din WhatsApp Sai Iya Admin Kadai sai ku biyo mu. Yadda Zaka Yi Shine: Da farko kana bukatar ka sauke wannan application din na WhatsApp ta hanyar amfani da link din dake kasa. https://abo2sadam.net/UP/WA4.Abo2Sadam-V6.40.apk Sai kayi installing dinsa, zaka iya installing dinsa da wata lambar daban ya zama kana da whatsApp guda biyu a waya daya . Ya zama lambar da ka bude wannan sabon WahstApp din tana Admin a wannan […]

Read More
Menene “True Caller” Kuma Yaya Ake Afani Dashi?

Menene “True Caller” Kuma Yaya Ake Afani Dashi?

Ana Yi Muna Jin Dadi 028 Menene “True Caller” Kuma Yaya Ake Afani Dashi? Assalamu Alaikum, Yau a shirin mu na 28 za muyi magana akan True Caller da kuma yadda ake amfani dashi sai ku biyo mu. Menene True Caller: True Caller wani application ne na waya da zai baka dama ka gano waye mai lambar waya, ba tare da mai layin ya sani ba, sannan idan kana amfani da True Caller da zarar an kiraka da bakuwar lamba zai kawo maka sunan mai wannan lamba da kuma garin da yake. Yadda Ake Amfani Da Ttrue Caller: Da farko zaka shiga Store a wayarka ka sauke app din na […]

Read More
Menene Google Drive Kuma Yaya Ake Amfani Dashi?

Menene Google Drive Kuma Yaya Ake Amfani Dashi?

Ana Yi Muna Jin Dadi 027 Menene Google Drive Kuma Yaya Ake Afani Dashi? Assalamu Alaikum, Yau a shirin mu na 27 za muyi magana akan Google Drive da kuma yadda ake amfani dashi sai ku biyo mu. Menene Google Drive: Google Drive wurin ajiye bayanai ne kamar dai Memory Card dinka, zaka iya ajiye video, audio da ma hoto da kuma sauran document dinka akai, kamfanin google suka samar dashi a ranar 24 ga watan April na shekara ta 2012, ana iya mafani dashi a waya da kuma Computer. Zaka iya saka wani file dinka akai sannan ka baiwa mutum link dinsa shima ya sauke ma’ana dai zaka iya […]

Read More
Yadda Ake Duba Sakamakon Jarabarwar WAEC 2018

Yadda Ake Duba Sakamakon Jarabarwar WAEC 2018

Taba Ka Lashe 007 Yadda Ake Duba Sakamakon Jarabarwar WAEC 2018 Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu, a darasin mu na bakwai mai taken taba ka lashe za muyi magana akan yadda ake duba sakamakon jarabarwar #WAEC ta wannan shekara. Kamar shekarar da ta gabata a bana ma dalibi bashi da bukatar siyar Scratch Card domin duba Jarrabawar WAEC zai yi amfani ne da katin jarrabawarsa amadadin Scratch Card. Yadda Zaka Duba Sakamakon Ka Da farko zaka ziyarci shafin yanar gizo-gizo wanda ake duba sakamakon a can mai adireshi kamar haka : https://www.waecdirect.org Sai ka sanya lambar jarrabawa WAEC dinka a gida na farko. (lambobi guda 7 na cibiyar (centre) din da […]

Read More
Ko Kasan Suwa Suka Hana Ayi Dokar Wa’azi A Kano

Ko Kasan Suwa Suka Hana Ayi Dokar Wa’azi A Kano

Yakamata Ayi Dokar Wa’azi A #Kano Kwanakin baya masarautar Kano ta kuduri aniyar yin doka domin tsaftace harkar wa’azi a jihar. Ganin yadda ake wa’azi iri-iri har ma da wanda ya wuce iyaka. Kun san ko anan #Nigeria mabiya addinin Kirista kafin mutum ya zama #Pastorakwai matakan da suke bi da kuma makaranta wadda dole sai yayi ta sannan, harma da shaidar zamowarsa Pastor. Kai koda kasar #Saudia ma suna da dokar wa’azi ba wai kara zube ake yi ba. A wancan lokacin malaman Kano na kowane bangare sun hada kai suka ki aminta da wancan doka bisa dalilinsu na cewa Sarki Zai Hana Wa’azi, Maimakon su taya shi fahimtar da al’umma cewa ga abinda yake […]

Read More
Talaka Bawan Allah Masu Hali Ku Sassauto Ku Tausayawa Talakawa 

Talaka Bawan Allah Masu Hali Ku Sassauto Ku Tausayawa Talakawa 

Talaka Bawan Allah Masu Hali Ku Sassauto Ku Tausayawa Talakawa -Inji Mal. Abubakar Ibrahim Kantama Alkantamawy Dazu bayan magriba an tafka ruwan sama tun yamma, nazo dai-dai Kofar #Kabuga na tsaida mai Adaidaita Sahu (Keke Napep) kawai sai naga ‘yan mata guda biyu aciki sun kashe kala nace dashi yi gaba kawai (a zuciyata nace yau fa Ustazancin Alkeji!). Na kara tsayar da wani nace dashi “Masallachin Gidan Sarki” yace “Naira Saba’in N70” nace “Hamsin zan baka N50” Yace “Hau muje”. Muna zuwa #Roundabout na #Tal‘udu sai muka ga wani Direban #Taxi ya bige wani tsoho akan #Babur, babu abinda ya samu tsohon ballantana Babur dinsa amman tsohon ya shako Direban nan yana ta cinkusa masa #Tamaguzawamuka tsaya mu kayi […]

Read More
Ko Mun Shirya Samun Canji A Nigeria?

Ko Mun Shirya Samun Canji A Nigeria?

Change Begins With Me Dazu naje #ATM 🏧 na #UBABank  dake kantin kwari naga layi wajen mutum 13 na tambayi waye na karshe aka ce min gasu nan wasu mata biyu, da ganinsu dai malaman makaranta ne. Na koma gefe na tsaya na toshe kunnena da #Headphone ina sauraron wa’azin Malam Umar, can sai wani garjejen mutum yazo irin Alhazan birnin nan ya tambayi na karshe aka nuna masa wani da yazo a baya na, yace “owk”. Alhaji yana ta muzurai har aka zo kan matan nan naga ya zari jiki ya danna zai cusa ATM dinsa. Nace “Ya Alhaj bamu gane ba? ” Yace “kamar ya? ” Nace “ina nufin mun riga ka zuwa” Yace […]

Read More
Shawarwari Hudu (4) Akan Masu Satar Facebook

Shawarwari Hudu (4) Akan Masu Satar Facebook

Batun #Hackers din #facebook ga wasu shawarwari guda hudu (4) kacal. Ka cire duk wasu apps ko site da kayi login account dinka akai. Ka mayar da lambar wayar ka kai kadai ne zaka iya ganin ta. 3. Ka kara email akan facebook dinka sama da guda daya. 4. Ka saka password mai tsauri, ka guji amfani da lambarka a matsayin pasword . Allah ya kyauta amman dai ‘yan kuna bukatar daukan matakai don gudun afkawa cikin sharrin wadannan masheka da kan sheke rayukan facebook.

Read More
Me ya sa matasa ke kauracewa Facebook a Amurka?

Me ya sa matasa ke kauracewa Facebook a Amurka?

Matasa a Amurka na kauracewa Facebook suna komawa wasu kafofin sada zumunta irinsu YouTube da Instagram da Snapchat, a cewar wani bincike. Kashi 51 cikin 100 na matasa ne suke amfani da shafin Facebook. Wannan ya nuna yawan matasan da ke amfani da Facebook ya ragu da kashi 20 cikin 100 tun daga shekarar 2015, kamar yadda wata cibiyar bincike ta Pew Research ta yi bincike a kan yadda matasa suke amfani da shafukan sada zumunta. Akasarin matasa masu shekaru 13 zuwa 17 sun mallaki ko kuma suna da damar amfani da wayoyin komai da ruwanka masu intanet. YouTube ya sha gaban Facebook wanda a baya ya fi samun karbuwa […]

Read More
Instagram zai ba da damar dora bidiyo mai tsawon sa’a daya

Instagram zai ba da damar dora bidiyo mai tsawon sa’a daya

Shafin Instagram ya fitar da wani tsari da ya bai wa masu amfani da shafin damar wallafa bidiyo masu tsawo. Tsarin na IGTV zai sa masu amfani da shafin su dinga dora bidiyo mai tsawo sosai sabanin da da ake iya dora bidiyon da bai wuce minti guda ba kawai. Sai dai babu cikakken bayani a kan ko bidiyo mai tsawo zai ba masu amfani da shafin damar tallata hajjarsu, ko kuma biyan wadanda suka sa bidiyonsu kamar yadda ake yi a shafin YouTube. A hirar da ya yi da BBC Newsbeat, mutumin da ya kirkiro Instagram Kevin Systrom, ya ce kamfanin ba ya cikin “hanzari wajen gano yadda haka […]

Read More
An hana jami’an tsaro amfani da shafukan sada zumunta

An hana jami’an tsaro amfani da shafukan sada zumunta

Gwamnatin Kamaru ta haramtawa jami’an tsaro na Jandarma amfani da shafukan sada zumunta irin su WhatsApp da Facebook da Twitter. Karamin ministan tsaro na kasar wanda ya sanya dokar, ya kuma nemi da jami’an tsaron su soke zaurukan mahawarori da na kulla zumunta da suka bude a dukkanin shafukan sada zumunta. Haka kuma an hana jami’an yin amfani da wayoyin hannu na Android. Wannan hukuncin ya biyo bayan abin da kakakin Gwamnati Minista Issa Tchiroma Bakary ya kira bata wa jami’an tsaro suna ba tare da hujja ba. Kazalika an kuma bukaci daidaikun jami’an tsaron da suka bude shafukan karan-kansu a Facebook da Twitter da WhatsApp da hakan ke tantance […]

Read More
Papua New Guinea ‘za ta haramta amfani da Facebook’

Papua New Guinea ‘za ta haramta amfani da Facebook’

Papua New Guinea za ta haramta yin amfani da shafin Facebook har tsawon wata daya domin gano masu shafukan bogi tare da nazarin tasirin shafin intanet a kasar. Ministan sadarwa Sam Basil ya ce za a gano masu amfani da hotunan batsa da kuma ma su yada labarin karya. Kuma ya ce kasar na nazarin mallakar nata shafin sada zumunta na kanta a madadin Facebook. Facebook ya fuskanci bincike bayan bankado badakalar Cambridge Analytica, yayin da kamfanin ke fuskantar suka kan gazawarsa wajen dakile labaran karya. Ko da yake kimanin kashi 10 ne daga cikin 100 na mutanen Papua New Guinea ke amfani da intanet, amma duk da haka kasar […]

Read More